Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Yi Wasiyyar Kada A Raba Masa Gado Sai An Aurar Da Yaransa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asalamu alaikum. Dan Allah malam ina da tambaya. Idan Mutum ya yi wasiyya a kan kar a raba masa gado har sai an aurar da yaransa da suka rage. Sai wani kuma acikin 'ya'yansa ya ce shi idan aka yi haka bai yafe ba. Muna neman fatawa a kai.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Ita dai wasiyyah tana daga cikin abubuwan da shari'ar addinin Musulunci ta shar'anta. Wasu daga cikin Malamai kamar su Ibnu Hazmin da Ibnu Shihab Azzuhriy sun tafi akan cewa yin Wasiyyah wajibi ne akan duk musulmin da ya mallaki wani abu na dukiya wanda za a iya raba gadonsa bayan mutuwarsa.

Wasu Malaman kuma suna ganin cewa yin wasiyyah zuwa ga iyaye da kuma makusanta waɗanda ba zasu ci gadon mutum ba, shi ne kaɗai wajibi. Wannan ita ce fatawar su Imam Ƙataadah da Masruƙ da Iyaas da Ibnu Jareer (Allah yai rahama garesu).

Wasu Malaman kuma suna ganin cewa hukuncin yin wasiyyah yana bambanta ne bisa gwargwadon hali ko yana yin da mutum ya tsinci kansa. Wani lokacin takan zama wajibi ayita, wasu lokutan kuma Mustahabbi.

Misali wanda ake binsa bashi, ko aka bashi ajiyar wata amana, to wajibi ne gareshi ya yiwa magadansa wasiyyar cewa su biya masa bashin da ake binsa, ko kuma su mayar da amanar nan dake hannunsa. Wannan shi ne ra'ayin Jagororin mazhabobin nan guda huɗu na Ahlus Sunnah wal jama'ah. Kuma shi ne ra'ayin Mazhabar Zaidiyyah daga ɓangaren Mazahibu na Shi'ah.

Wasiyyah kuma takan zama haramun idan ya zamto anyita da mummunar manufa kamar tauye hakki ko hana hakkokin wasu daga magadan, ko kuma idan aka yita domin assasa wasu abubuwan da shari'ah ta haramta.

Wasiyyah tana da wasu Ƙa'idodin bayan wannan. Shi ne kamar yadda ya zo acikin wani hadisi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce "BA'A YIN WASIYYAH GA MAGAJI". (Ahmad Abu Dawud da Tirmidhiy ne suka ruwaitoshi).

Wato duk wanda ya kasance yana cikin masu cin gadonka, babu damar ka bar wasiyyar cewa shi za a bama gona kaza ko gida kaza, ko abashi Miliyan kaza daga cikin dukiyarka bayan ka rasu. Kuma babu damar ka keɓance shi da wani abun amfani ko amfanarwa domin kansa shi kaɗai.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam acikin wani hadisin da Imam Abdurrazzaƙ ya ruwaito acikin Almusannaf nashi cewa: "Mutum yakan kasance yana aikata irin ayyukan mutanen kirki har tsawon shekara saba'in amma idan ya aikata wauta acikin wasiyyarsa sai wannan ya janyo masa mummunar cikawa sai ya shiga wuta".

Sa'eed bn Mansur ya ruwaito ta hanyar Abdullahi bn Abbas (radhiyalLahu anhuma) yana cewa "CUTARWA ACIKIN WASIYYAH YANA DAGA CIKIN MANYAN LAIFUKA".

A takaice dai, ita wannan wasiyyar da kika ce mamacin nan yayi, ba halastacciya bace bisa dokokin addinin Musulunci, kuma ta saɓa da Umurnin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Don haka haramun ne a zartar da ita. Wajibi ne ku raba gadon nan a bama kowanne mai gado rabonsa da Allah ya riga ya bashi.

Jinkirin raba gado zalunci ne da wasu suke fakewa dashi suna cin hakkin masu hakki. Sannan mamaci fa bashi da wani sauran hakki acikin dukiyar da ya bari, bayan an biya masa basussukan dake kansa sai kuma zartar da halastattun wasiyyoyinsa, shikenan. Amma gaba ɗayan sauran dukiyar nan ta magada ce. Kuma bashi da damar tsara musu lokaci ko yana yin yadda zasu raba gadonsu.

Shi wannan ɗan nasa da ya bukaci azo araba a bashi nasa rabon, ya yi daidai. Su kuwa waɗannan yaran da mamacin ya ce ayi aurensu da dukiyar da ya bari, ai ba nasu ne su kaɗai ba. Don haka ba za a yi biyayya ga wannan umurnin nasa ba. Umurnin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam)kadai za a bi anan.

Inama da cewa ya yi Idan lokacin auren nasu yayi, dukkan 'ya'yansa su haɗa kai su ba da gudunmuwa su aurar dasu, to da wannan ya fi daidai kuma ya fi alkhairi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments