Ticker

6/recent/ticker-posts

Karatun Fatiha Acikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam Ya hukuncin wanda ke bin liman kuma har aka gama sallar shi bai karanta fatiha ba.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

karatun fatiha rukunine daka cikin rukunan sallah akan mamu da liman da wanda zaiyi sallah shi kaɗai, saboda faɗin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam (Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba) Imamul bukhari yafitar da wannan hadisi ababin kiran sallah (714). Amma karatun fatiha ga wanda yake bin liman asallar da ake bayyana karatunta akwai maganganu biyu na malama:

1. Magana tafarko: suka ce wajibine karatun fatiha ga wanda yake bin liman asallah, dalili akan haka suka ce faɗin maganar manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam daya ce (Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba), saboda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam lokacin da yake koyar da wanda bai iya sallah ba ya umarceshi da karantata. Ya inganta daka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yakasance yana karanta ta akowacce raka'ar sallah.

Ibnhu hajar Rahimahullah ya ce: Acikin fathul baary, hakika ya tabbata umarnin karatun fatiha akan mamu asallar da ake bayyana karatunta batare dawani kaidi ba, hakan yanan cikin abunda imamul bukhary yafitar, da turmuzi da ibnu hibban daka ruwayar makhuul, daka mahmud binu rabee'i binu ubadah, watarana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam karatu yai masa nauyi asallar asuba, lokacin da'aka idar da sallah sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: watakila kuna yin karatu abayan limaminku? Sai sahabbai suka ce eh, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: kada kudunga aikata hakan saifa karatun fatiha saboda babu sallah ga duk wanda bai karantata ba.

2. Magana ta biyu: suka ce karatun liman shi ne karatun mamunsa dalili akan haka suka ce faɗin Allah maɗaukakin sarki:

 وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنْصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ ۝٢٠٤

Idan Ana karanta Alƙur'ani kuyi sauraro na fahimta, kuma kuyi shiru, shiru na nutsuwa ko kwa samu Rahamar Allah. (Surah Al-A'raf - 204).

Ibnu hajar ya ce: Masu cewa karatun fatiha yafadi akan mamu daka malikiyyah sunkafa hujja da wani hadisi dayake cewa (Idan ana karanta Alƙur'ani kuyi shiru) kuma hadisine ingantacce muslim ya ruwaitoshi daka hadisin Abu musa Al Ash'ary Allah yakara yarda dashi.

Waɗanda suke fatawa da wajabcinta suntafi akan cewa mutum zai karantata bayan liman yagama karatun fatiharsa atsakanin ɗan shirun dayake kafin yashiga karatun surah, sai ka karanta duk da wannan shirun da liman yake malamai sun ce bidi'ane baida asali, ibnu hajar ya ce: mamu "zaiyi shiru idan liman yana karanta fatiha, shi mamu zai karanta idan yai shiru"

Sheik bin baaz ya ce: Abunda ake nufi da shirun liman shi ne shirun da mamu zai iya karanta fatihar, ko bayanta, ko acikin surar datake bayan fatihar, idan liman baya shiru ɗin to abunda yake wajibi akan mamu shi ne karanta fatihar koda liman yana karatun surah ne, wannan shi ne mafi ingancin magana cikin maganganun malamai, fatawa sheik bin baaz (221).

An tambayi majalisar fatawa da ilmi ta kasar saudiyyah irin wannan tamabaya sai suka amsa dacewa: Magana igantacciya wajan ma'abota ilmi shi ne karatun fatiha wajibine akan wanda zai sallah shi kaɗai, da kuma liman da mamu asallar da ake bayyana karatunta ko ake boye karatunta, saboda dalilai dasuka nuna hakan, da kuma kebantuwar dalilan, Amma faɗin Allah madaukakin sarki daya ce:

 وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنْصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ ۝٢٠٤

Kuma idan an karanta Alƙur'ani sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammaninku, ana yi muku rahama. (Surah Al-A'raf - 204).

Da fadin Manzan Allah (ﻭﺇﺫﺍ ﻗﺮﺃ ﻓﺄﻧﺼﺘﻮﺍ ) ya haɗe karatun fatiha da waninta, sai ake bance su da hadisin dayake cewa (Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba). Ma'ana waccan aya da waccan hadisi basu shafi wajabcin karatun fatiha akowacce sallah ba, kuma basu shafi wajabcin karatun fatiha akan kowaba asallah dan haɗa dalilan gaba ɗaya kai aiki dasu.

Amma hadisin dake cewa (karatun liman shi ne karatun mamu )wannan hadisine mai rauni, maganar da ake cewa, faɗin mamu Ameen idan liman yagama karanta fatiha yana matsayin karatun fatihar su, wannan maganace mai rauni bata ingantaba.

Muna rokon Allah shiriya cikin abunda akai saɓani kansa nagaskiya domin shi mai jine da amsa addu'ar bayinsa.

WALLAHU A'ALAM

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments