𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ya halarta ga Musulmi ya halarci bikin Kirsimeti ko wani bikin Kiristoci a cikin coco? Mene ne hukunci shiga cikin coci ga Musulmi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Shiga cikin Coci Asali Halal
ne, haka yiwa kafiri barka a munasaba keɓantacciya
aduniyance data shafe shi halal ne, kamar yi masa barka dayin Aure, ko Samun
wata Nasara akan wani Abu, jarabawa Samun Aiki ko samun Haihuwa.
Hukuncin shiga coci halal ne
awajan mafi yawan Malamai, batare da karhanci ba,Duba Al'insaaf (1/496)
Wasu Suka ce: Ya halatta
ashiga coci idan Babu hotuna acikinta ko gumaka agirke acikinta.
Sahihiyar Magana Ya halatta
shiga coci koda akwai hoto acikinta, inwani dalili yasa ashiga ɗin.
Duba: Bukhary (1276) da Almusannaf (4871) da Ahkamu Ahlul Zimmah (3/164), da
Al-Musannaf Na Abdurrazaƙ (1610)
da Al-mugny (8/113).
Halayen dabai Halatta
musulmi yaziyarci Coci ba, ko Wajan Bautar kafirai ba.
1. Lokacin dayake da
Munasaba da Wani idi Nasu, ko wata Munasaba tasu ta Addini, ziyartar coci
awannan halin yazama tarayya dasu acikin idinsu nakafirci wanda Shari'ah ta
hana.
Umar Allah yaƙara yarda dashi ya ce: Kada kushiga
cocin kafirai lokacin bukukuwansu domin fushin Allah yana sauka akansu.Musannaf
Na Abdurrazaƙ (1609).
2. Idan yazama za a lazimtawa
wanda suke acocin su yi tarayya wajan wani Abu na addinisu, kamar Anemi wanda
ya je cocin yagabatar ko Aikata wani Abu dayake akwai girmamawa ga Abun
bautarsu kamardurkusawa ko sunkuyar da baya ko tsugunawa ko rankwasar da kai,
ko wake
3. Idan Mai zuwa Coci yana
tsoran fitina akansa, kada wani Abu yasameshi, to jefa masa rudu azuciyarsa
cikin Abunda zai gani koya ji, wannan yana sa wanda baida ilmi da wayau
lalacewar Addininsa.
4. Idan ba da izininsune ba,
ko kuma Zasu Ɗauki zuwanka kamar
izgilancine da Addininsu da ibadarsu.
5-. dan Akwai wani Al'amari
dazaisa ka fitinu saboda shi, wanda wannan zaisa wanda baida ilmi ya ɗauka
kamar kana tabbatar da Abunda sukene, kamar yanda yake aƙissar Umar ɗan
Khaddab Allah yaƙara
yarda dashi.
6. Idan zuwanka zai zama
awata sifa ta tabbatar da Abunda suke fadi da aikatawane na kafirci da Shirka
acikin sallar su da ibadarsu.
Bikin Aure idan ba bikine Na
addininsu ba, kuma yakuɓuta daka Ababen da suke
haramun kuma yakuɓuta daka Ababen da'aka hana
ziyartar coci acikinsu, kuma bai haɗu da
Al'ada ta tsiraici da ketare iyaka da munanen Halaye wanda zai gudana daka
mahalarta ko Amare ba, inkaga akwai Maslaha kana iya halarta, inhar babu Abu
daya da shari'a ta tsoratar awajan. Domin Yana cikin asalin halaccin zuwa coci
amunasaba ta harkar duniya. Mussaman idan Akwai alaƙa ta zuwa kamar kiransa zuwaga addini.
Dan haka Bai halatta kaje
bikin Auren Abokinka kirista ba koda ba'a coci bane, indai bikin yana da alaƙa da wani abu da suke ƙudurcewa acikin addininsu, ko akwai
abunda shari'a ta tsoratar akansa.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
HUKUNCIN MUSULMI YA SHIGA COCI KO YA HALARCI BIKIN
KIRISTOCI
Tambaya:
Shin musulmi na da izinin shiga coci? Kuma ya halatta ya
halarci bikin Kirsimeti ko wani biki na addinin Kirista?
1. Asalin hukunci: Shiga Coci ba haramun ba ne
Asalin ziyarar coci halal ce idan ba domin taron addininsu
ba, kuma akwai dalili da ya halatta shigowar Musulmi.
Hujoji daga Sunnah:
1. Nasāran Najrān
Sakamakon zuwan Nasāran Najrān wurin Annabi ﷺ, ya ba su mafaka a
cikin Masallaci, kuma ya yarda su zauna kuma su tattauna.
قَدِمَ وَفْدُ نَجْرَانَ عَلَى النَّبِي ﷺ فَأُنْزِلُوا
الْمَسْجِدَ
(Ibn Hishām da Ibn Sa’d sun rawaito)
Ma’ana:
Wani ƙungiya daga Najrān
suka zo wurin Annabi ﷺ,
sai ya sauke su a masallaci.
Wannan hujja ce cewa shigar musulmi wurin da suke ibada ba
abu ne da ya haramtu ba, matuƙar ba tarayya a ibada ba.
2. Abu Musa Al-Ash'ari (RA)
Ya yi sallah a cikin wata coci lokacin da bai samu masallaci
ba.
(Musannaf Ibn Abi Shaybah – Hadisi 4871)
2. Amma akwai lokuta da ya haramtu shiga Coci
Shigar coci zai zama haram idan:
1 — Lokacin bikin addininsu (Kirsimeti, Easter, Mass,
Communion, da sauransu)
Saboda wannan tarayya a ibadah ce, kuma shari’a ta haramta
yin tarayya ko goyon bayan abinda ya haɗa
da imani ko shaida a bautar da ba ta musulunci ba.
Hujja:
Umar ibn al-Khattab (RA) ya ce:
لَا تَدْخُلُوا عَلَى الْمُشْرِكِينَ فِي كَنَائِسِهِمْ
يَوْمَ عِيدِهِمْ، فَإِنَّ السَّخْطَةَ تَنْزِلُ عَلَيْهِمْ
(Musannaf Abdurrazzaq – 1609)
Ma’ana:
Kada ku shiga wurin mushrikai cikin cocinsu a ranar idinsu,
domin fushin Allah yana sauka a kansu.
Wannan shi ne matakin da mafi yawancin malamai suka yi aiki
da shi.
2 — Idan shigar ya tilasta maka aikata wani abu na addininsu
Kamar:
• durƙusawa
• yin alama (sign of the cross)
• tsayuwa lokacin karatun su
• wake
• amsa waazi
• shiga jerin ibada
Wannan ya zama haram domin tarayya ce a bautarsu.
Ayah daga Qur’ani:
وَالَّذِينَ لَا يَشْهَدُونَ الزُّورَ
(Surat Al-Furqān: 72)
Malamai da yawa sun fassara Az-Zūr a nan da: Idi da
bukukuwan mushrikai.
3 — Idan akwai fitinar zuciya ko ruɗu a imani
Wani na iya shiga coci ya ji kida, surutai, raka'a da
hotuna, ya fara samun ruɗu
ko tambayoyi da suke buga zuciya. Idan mutum bai da ƙarfi, yana iya shiga
cikin shakku.
Saboda haka malamai suka ce:
“Idan akwai fitina, to haramun ne.”
4 — Idan ba a ba su izini ba
Shiga wurin addinin mutum ba tare da izini ba haramun ne,
saboda cin mutunci ne ga addininsu da masallacinsu.
5 — Idan za a ɗauka
tamkar ka yarda da akidar su
Idan jama'a za su gan ka ka shiga a bikin su har su ɗauka cewa ka yarda da
addininsu, to tafi kyau ka nisanta, domin kare dukibar imani.
3. Halarci bikin aure na Kirista (in ba na addini ba)
Idan biki ba biki na addini ne ba, kuma:
• babu haramun a wurin,
• babu wake,
• babu cakude cewa ba'a kiyaye ba,
• ba a cikin cocin ibada ba,
• kuma biki ne na al’adar duniya (civil
wedding),
to za a iya halarta idan akwai maslaha (kamar zumunci,
da’awah, mutunci, zaman lafiya).
Amma idan bikin shi ne na addininsu (church wedding), to
haramun ne domin tarayya a ibadah ce.
Takaitaccen Hukunci
✓ Halal:
Shiga coci idan dalili na duniya ne, ba na ibada, kamar:
• aikin government
• karatu
• ziyara don mu’amala
• gudanar da magana
• saboda maslaha mai tsarki
✓ Haram:
Shiga coci a:
• lokacin Kirsimeti / Easter / Mass
• bikin aure na addininsu
• wani taron da ake yin ibada
• idan za ka aikata wani abu na
addininsu
• idan fitina za ta samu
• idan za a ɗauka tamkar ka yarda da akidarsu
Ayoyin Qur’ani Masu Ƙarfi Akan Karhanci Tarayya a Addinin
Kafurai
Suratul Maidah 2:
وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ
Ma’ana:
Kada ku taimaka wajen zunubi da keta haddi.
Suratul Baqarah 120:
وَلَن تَرْضَىٰ عَنكَ الْيَهُودُ وَلَا النَّصَارَىٰ
حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ
Ma’ana:
Yahudawa da Nasara ba za su taba yarda da kai ba sai ka bi addininsu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.