Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Bar Sallar Jumma'a Ba Tare Da Wani Uzuri Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam. Mene ne hukuncin wanda ya bar sallar juma'a ba tare da wani kwakwkwaran dalili ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.

Barin zuwa sallar juma'a ga mutum baligi Mai lafiya wanda ta wajaba akansa ba tare da wani dalili na shari'a ba Kaba'irace cikin Manyan Laifuka, duk wanda kuma ya bar sallar Juma'a har Uku ajere bai jeba Allah zai toshe Zuciyarsa yakasance Cikin gafalallu, kamar yanda Muslim Yaruwaito A cikin Sahihin Littafinsa Daka Abu Huraira Yardar Allah takara tabbata a gareshi da Abdullahi Ɗan Umar, Allah ya kara yarda dasu, Sun ji Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam akan Munbari yana cewa (Kodai Mutane Sudena barin kinzuwa Sallar Juma'a kokuma Allah yakulle zukatansu, Sannan Sukasance Cikin gafalallu). Awani hadisin Daban (Duk wanda ya bar Sallar juma'a uku dagan-ganci Allah Zai toshe Zuciyarsa).

Waɗannan Uƙubobine Nazuciya, Sunfi tsanani akan uƙuba tajiki tahanyar kulle mutum akurkuku ko dukansa da bulala, Kuma wajibi ne ga shugaba Yahukunta waɗanda ba sa Zuwa Sallar Juma'a ba tare da Wani Uzuri karɓabe Ashari'aba, Abin da zai zamto Firgici Na laifinsu, Dukkan Musulmi ya ji tsoran Allah karya tozarta wani wajibi ciki Abubuwanda Allah ya wajabta masa, Ya dunga Tunawa Kansa Uƙubar Allah, Ya kiyaye Abin da Allah ya wajabta masa danya Samu ladansa Awajan Allah, Allah yana bayar da Falalar ga Wanda yaso.

Shaiek Abdurrahman Mubaraka. Saboda Haka wanda ya bar sallar juma'a ba tare da wani Uzuriba ya aikata babban laifi cikin Manyan Laifuka, Kuma Inbai tubaba Allah zai rufe zuciyarsa Babu wani alkhairi da zai shiga cikinta sai sharri da bala'i Sannan yazamto cikin gafalallu, Wadanda Zasuyi Nadama Ranar Alkiyama. Allah yakiyayemu.

WALLAHU A'ALAMU.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Barin sallar Juma’a ga mutum baligi, lafiyayye, wanda ta wajaba a kansa, ba tare da wani uzuri na shari’a ba, yana daga cikin manyan laifuka (Kaba’ir) a Musulunci.

Manzon Allah ya yi gargaɗi mai tsanani game da hakan.

Hadisai kan barin Juma’a

1. Allah zai kulle zuciyar wanda ya bar Juma’a saboda raini

Muslim ya rawaito daga Abu Huraira da Abdullahi ɗan Umar – Allah ya ƙara yarda da su – cewa Annabi ya ce:

Ko dai mutane su daina barin zuwa Juma’a, ko kuwa Allah zai kulle zukatansu, sannan su kasance cikin gafalallu.”

A wani hadisin kuma:

Duk wanda ya bar sallar Juma’a uku saboda ganganci, Allah zai toshe zuciyarsa.”

Wannan hukuncin zuciya ya fi duk wata hukuncin jiki tsanani — domin rufe zuciya na nufin:

Rashin natsuwa

Rashin jin daɗin ibada

Rashin fahimtar Alkhairi

Zama cikin gafala

Hukuncin Shari’a

Malamai sun ce:

Wajibi ne ga shugabanni su hukunta wanda ya yawaita barin sallar Juma’a ba tare da uzuri ba.

Domin hakan saba wa doka ce ta addini, kuma ya jawo lalacewar al’umma.

Nasiha ga Musulmi

Ya kamata kowa ya tsoraci barin abin da Allah Ya wajabta.

Ya tuna da uƙubar da ke tare da watsi da farilla.

Ya kiyaye wajibai domin samun lada da falalar Allah.

Sakamakon barin Juma’a

Wanda ya bar ta ba tare da uzuri ba:

Ya aikata babban laifi.

Idan bai tuba ba, Allah zai rufe zuciyarsa.

Zuciyarsa ba za ta karɓi alkhairi ba.

Zai shiga cikin gafalallu.

Zai yi nadama a ranar Kiyama.

Allah Ya kiyaye mu daga barin wajibai, Ya sa mu kasance cikin masu tsoronSa.

WALLĀHU A‘ALAM.

Post a Comment

0 Comments