Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sayar Da Maganin Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina sayar da kayan mata kamar na matsi da sauransu, sai aka ce wai ba kyau in sayar wa karuwa ko Kirista. Mene ne gaskiyar wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da take nufi da kayan mata a nan shi ne ‘maganin mata.’ Wato maganin da mata suke amfani da shi domin ƙara samun soyuwa a wurin mazajen aurensu. Shi kuma maganin mata a fahimtarmu iri-iri ne:

1. Akwai wanda addini ya hana kai-tsaye, kamar abin da malamai suka san shi da suna: At-Tiwalah. Shi ne wanda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ambata a cikin maganarsa cewa:

إِنَّ الرُّقًى وَالتَّمَائِمَ وَالتِّوَلَةَ شِرْكٌ

Lallai Ar-Ruƙaa da At-Tamaa’im da At-Tiwalah duk shirka ne! (Abu Daawud: 3883 da Ahmad: 3615 da Ibn Maajah: 3530 da Al-Haakim: 4/217 da Ibn Hibbaan: 1412 duk sun riwaito shi, kuma Al-Haakim da Az-Zahabiy da Al-Albaaniy duk sun ce: Hadisi ne sahihi. Dubi Silsilah Sahihah: 1/584 a ƙarƙashin hadisi na: 331).

Wurin fassara ma’anarsa ne Sahabi Ibn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) ya ce:

«شَيْءٌ يَصْنَعُهُ النِّسَاءُ يَتَحَبَّبْنَ إِلَى أَزْوَاجِهِنَّ»

Wani abu ne da mata suke aikata shi, suna ƙara soyuwa da shi a wurin mazajensu. (Sahih Ibn Hibbaan: 6090).

Shi kuma Ibn Al-Atheer (Rahimahul Laah) cewa ya yi:

مَا يُحبّب الْمَرْأَةَ إِلَى زوْجها مِنَ السِّحْرِ وَغَيْرِهِ، جَعَلَهُ مِنَ الشِّرْكِ لِاعْتِقَادِهِمْ أَنَّ ذَلِكَ يُؤَثِّرُ ويَفْعل خِلَافَ مَا قَدَّرَهُ اللَّهُ تَعَالَى.

Abin da yake soyar da mace ga mijinta ne, na sihiri ko waninsa. Ya sanya shi daga cikin sihiri ne domin suna ƙudurce cewa shi ɗin yana yin tasiri kuma yana aikata saɓanin abin da Allaah Ta’aala ya ƙaddara. (An-Nihaayah: 1/200).

Wannan nau’in shi ne sananne kuma wanda ya fi yawa a cikin mata.

2. Akwai kuma wanda nau’in kayan abinci ko abin sha ne na halal wanda mace ke ci ko sha ko shafawa ko yin wanka da shi, domin ya gyara mata jiki ya zama mai laushi ko taushi, ba tare da wani abu na saddabaru ko mu’amalar bokaye ko matsafa ba. Wannan halal ne, ba laifi ba ne, in sha’al Laah.

Sai dai akwai tsoron cewa, ta wannan hanyar ana iya bayar da maganin ‘matsi’ kamar yadda aka ambata a wannan fatawar. Wannan kuma yana iya kai ’yan mata ga cigaba da holewa kafin aure, tun da suna da sanin cewa akwai wannan maganin da za su yi amfani da shi kafin tarewa da mazajensu na aure! Sai a kiyaye sosai, kar aikin ya zama taimakawa wurin yaɗa ɓarna, maimakon maganinta da daƙile ta a cikin alumma.

3. Akwai kuma waɗansu magungunan da su ke ƙwayoyi ne ko allurori irin na asibiti da ake yi wa mace na wani lokaci, har kuma hakan ya kai ga sauya mata yana yi da launin fatar jiki ko kuma gashin kai, sauyawa tabbatacce na dindindin. Wannan kai-tsaye ya saɓa wa dokokin musulunci mai hana zaƙewa da wuce iyaka a wurin kwalliya, domin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

«لَعَنَ اللهُ الْوَاشِمَاتِ وَالْمُسْتَوْشِمَاتِ، وَالنَّامِصَاتِ وَالْمُتَنَمِّصَاتِ، وَالْمُتَفَلِّجَاتِ لِلْحُسْنِ الْمُغَيِّرَاتِ خَلْقَ اللهِ»

Allaah ya la’anci mata masu yin zane a fatar jiki da masu neman a yi musu zanen; da mata masu aske gashin fuska da masu neman a aske musu; da mata masu yin wushirya, domin ƙarin kyau, masu sauya halittar Allaah. (Sahih Al-Bukhaariy: 4886; Sahih Muslim: 2125).

Abu ne dai sananne a wurin masana cewa, duk abin da aka cusa wa jikin ɗan’adam alhali ba yana da buƙatarsa ba, wannan yana haifar da matsala gare shi ko a kusa ko a nesa.

A ƙarƙashin wannan dole mai sayar da irin wannan kayayyakin ta yi taka-tsantsan, ta bincika ta tabbatar ba zai cutar da wadda za ta yi amfani da shi ba ko a nan kusa ko a can nesa. Kuma a nan babu bambanci ko wacce za ta yi amfanin da shi musulma ce ko wacce ba musulma ba. Kuma ko matar kirki ce mai kamun kai, ko kuwa dai karuwa ce mai zaman kanta. Duk dai bai halatta musulma ta zama sanadin cutarwa ga kowa ba.

Allaah ya ƙara mana shiriya.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments