Ticker

6/recent/ticker-posts

Dalilan Da Ke Sa Allah Ya Ki Amsa Addu'ar Bawansa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam Khamis. Don Allah wanne abubuwa ke sa mutum ya yi tayin addu'a amma Allah ba zai amsa masaba.?

DALILAN DA KE SA ALLAH YA ƘI AMSA ADDU'AR BAWANSA:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

Kaɗan daga cikin abubuwan dayasa mutum zaitayin addu'a amma baza'a amsa masaba.

1. CIN HARAM: Allah baya amsar addu'ar maciyin haram, ko mara kula da alƙawari da ƙarya da cin amana da kuma yawan zantukan batsa.

2. RASHIN GASGATA ADDU'A: Idan mutum zai yi addu'a kuma bai yi ta da ikhlasi ba to kamar bai gasgakata ta bane. Ko kuma rashin furta lafuzzan daidai.

3. RASHIN TSARKIN ZUCIYA: Babu yadda za ai zuciyarka ta cika da Hassada da baƙin-ciki da jin haushin wani kuma Allah ya Amsa maka addu'arka.

4. RASHIN KULA DA IBADA: Babu yadda za ai bawa ya yi watsi da abin da Allah ya wajabta masa kuma ya roƙi Allah, Allah yamasa abin da yakeso.

5. RASHIN KYAUTATA IBADA: Babu yadda za ai bawa yana sallah ko wata ibada batare da nutsuwa da kyautata ibadar ba, kokuma kana sallah amma zuciyarka tana cike da tunnin wani abu daban ba sallar ba.

6. GIRMAN KAI: Allah baya Amsa addu'ar masu girmankai, domin girman kai sifface ta yahudawa maƙiya addinin Allah.

7. RASHIN HIKAYO ABIN DA AKE FAƊA ACIKIN ADDU'A: Idan mutum yana addu'a kuma baya hikayo (hango ma'anonin) ababan dayake faɗi na girmama Allah da ayoyinsa ayayin addu'ar da kuma kiyaye girman wanda yake roƙon to shi ma bazai sami biyan buƙataba.

8. CIN MUTUNCIN MUTANE: Babu wani wanda zai zama mai cin mutuncin mutane yana wulaƙantasu kuma ya yi tsammanin za a amsa masa addu'arsa.

9. GAGGAWA. Ɗan Adam akwaishi da gaggawa sha yanzu magani yanzu, Allah ba ya son gaggawa, shi yasan lokacin dayafi dacewa ya baka duk abin da kakeso. Shi yasan lokacin dayafi dacewa yabaka arzikinka. Ko mutum yarinƙa cewa ni inata addu'a amma haryanzu ba'a amsamin ba. Haka haihuwa. Haka ilimi. Haka lafiya ga mara lafiya. Haka aure. Da sauaransu. Duk Allah ke badasu a lokacin dayaso.

10. RASHIN NACI AKAN ADDU'A: Idan mutum baya naci akan addu'a shi ma wanann baya samun biyan buƙatarsa. Domin Allah yanason bawa mai yawan naci acikin roƙon ubangijinsa.

11. Rashin ƙasƙantar da kai agaban Allah, da nuna gazawa agaban Allah, da nutsuwa agaban Allah.

12. Rashin kyautata zato ga Allah da kwaɗaituwa a gareshi akan samun biyan buƙatu, da cire kokwanto acikik zuciya.

Yazo A Hadisi Cewa: Abdullahi ɗan Abas (RA) Ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah {Sallallahu Alaihi Wasallam} wata rana, Sai ya ce dani, Yakai yaro. Zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah sai ya kiya ye ka, Ka kiyaye Allah zaka same shi a gaba gare ka, idan zakai roƙo to ka roƙi Allah, idan zaka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Ka sani da alumma zasu taru don su amfane ka da wani abu, bazasu iya amfanar da kai komai ba, sai dai abin da Allah ya rubuta maka. Idan kuma da alumma zasu taru don su cuceka da wani abu, bazasu cuceka da komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta agareka. An ɗauke alƙaluma, takardun kuma sun bushe. [ Tirmiziy:2516 ]

A wata ruwayar kuma wacce ba ta Imam tirmiziy ba, Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, Ka nemi sanin Allah a lokacin da kake cikin yalwa zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. Kasani duk abin da ya kuskure maka to bai kasance zai same ka ba, Duk kuma abin da ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. Ka sani lallai cin nasara yana tare da haƙuri, Yayewar musiba kuma tana tare da baƙin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki.

Ya tabbata a hadisi cewa; An Karɓo daga Abu Hurayrah (R.A) Ya ce; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Ya ce: (Allah) yana karɓawa ɗayanku (addu'arsa) matuƙar baiyi gaggawa ba, (shi ne) ya ce na yi addu'a (amma har yanzu) ba'a amsamin ba. (Bukhari, 5865. Muslim, 2735).

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Ya ce: "hakika ubangijinku mai kunya ne, mai karamci ne. yana jin kunyar bawansa yayin da ya cira hannayensa ya rokeshi, a ce ya mayar dasu ba tare da komai ba".

An karbo hadisi daga Buraidata (r.a) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa:👇

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنِّي أَشْهَدُ أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ الأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ

FASSARA: "Ya Allah hakika ina rokonka, na shaida kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai, makaɗaici, madawwami, wanda ba ya haifuwa kuma ba a haife shi ba, kuma babu wanda ya kai shi. Sai manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: “Lallai ka yi roƙo da sunan da Idan aka yi roƙo da shi ana bayarwa, kuma idan aka yi addu'a da shi ana amsawa". mutane huɗu suka ruwaito shi, Ibn Hibban ya inganta shi.

Wannan hadisin na nuna mana kenan ana saurin Amsa addu'ar Wanda ya yi amfani da waɗannan sunayen kenan. Saboda haka idan mutum zai yi addu'a, sai ya fara ambaton waɗancan sunayen, sannan sai addu'ar ta biyo baya.

Akwai wasu lokuta idan bawa ya yi addu'a Allah na karɓa masa kai tsaye kamar yadda ya tabbata a hadisi. Misali kamar sulusin dare na ƙarshe, lokacin saukar ruwan sama, tsakanin Kiran sallah da tada iƙama, Ranar juma'a daga sallar la'asar zuwa faduwar Rana, in an yi sujjada ansa goshi aƙasa.

Waɗannan duka lokuta ne da Allah ke karban Addu'a, Lokacin da mutum yake kan hanyar tafiya. Allah yana karban Addu'a, Addu'ar Wanda aka zalunta Allah (S. W. T) yana karba, Addu'ar iyaye wa yayansu Allah (S. W. T) yana karba. Addu'ar me azumi lokacin budabaki wannan Addu'a Allah na karba, Addu'a lokacin dakaji zakara yai cara idan Kai Addu'a dai dai lokacin dayake cara wannan Addu'ar Allah (S. W. T) yana karbanta.

Allaah Ta’aala Yana saukowa zuwa saman duniya a ƙarshen dare Yana cewa: Wa zai yi addu’a gare ni in amsa masa? Kuma wa zai roƙe ni in ba shi buƙatarsa? Kuma wa zai nemi gafarata in gafarta masa? (Al-Bukhaariy: 7494; Muslim: 758)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments