Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Yaye Bakin Ciki Da Damuwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah, Sheikh barka da kokari Allah ya saka da alheri, tambayata shi ne, me yake sa yawan bacin rai ga mutum musamman ga mace, sannan meye mafita? malam a taimaka min da addu'ar da zan dinga yi inna cikin damuwa. Allah ba da ikon amsamin.

ADDU'AR YAYE BAƘIN-CIKI DA DAMUWA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Daga cikin abubuwan da suke jawo ɓacin-rai akwai:

1. ZUNUBAI: Saboda duk mai aikata su, zai samu kunci a rayuwar shi, kamar yadda Ibnulkayyim ya faɗa !

2. Tunawa da mummunan abin da ya gabata ko kuma fargabar abin da zai faru Nan gaba.

3. Yawan burace-burace.

4. Rashin yafiya da niyyar ɗaukar fansa.

5. Yawaita alaka da mutane, saboda duk wanda alakokinsa suka Yi yawa, ko masu binsa bashin nauyi za su yawaita.

Yawaita Istigfari, da cikakken dogaro ga Allah, da kuma takaita Mu'amala da mutane yana karanta damuwa.

Rokon Allah da dogaro ga Allah da yarda da Ƙaddara mai kyau ko marar kyau, yana daga cikin mafi girma hanyar samun waraka da damuwa da bakin-ciki da yake damun bawa.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya koyar da mu addu'oin da yakamata mu yawaita karantawa dan samun waraka daga dukkan wani bakin-cikin da damuwa da kuncin rayuwa nan duniya da lahira da yardar Allah.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa: Adduar zinnun lokacin da ya roki Allah yana cikin kifi:👇

  ﺇﻟﻪَ ﺇﻟَّﺎ ﺃﻧﺖَ ﺳﺒﺤﺎﻧَﻚ ﺇﻧِّﻲ ﻛﻨﺖُ ﻣﻦ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦَ

"LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN"

babu wani mutum da zai shiga cikin damuwa kuma ya roki Allah da wannan adduar, face sai Allah ya fitar da shi daga wannan damuwar).

Haka kuma an ruwaito daga Abu Bakrah cewa Manzon Allah (tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi) ya ce addu'ar wanda ya shiga mawuyacin hali ita ce:👇

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺭَﺣْﻤَﺘَﻚَ ﺃَﺭْﺟُﻮ ، ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻜِﻠْﻨِﻲ ﺇِﻟَﻰ ﻧَﻔْﺴِﻲ ﻃَﺮْﻓَﺔَ ﻋَﻴْﻦٍ ، ﻭَﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲﺷَﺄْﻧِﻲ ﻛُﻠَّﻪُ ، ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖ

"ALLAHUMMA RAHMATAKA ARJU,FALA TAKILNI ILA NAFSI DHARFATA AININ, WA ASLIH LI SHA'ANI KULLAHU, LA ILAHA ILLA ANTA"

[Abu Dawood (5090), Ahmad (27898)]

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya cewa Asma'u bntu Umais R.A: Shin bazan koya maki ba wata addu'a da zaki karantata alokacin damuwa da bakin-ciki, ko lokacin kuncin rayuwa?? Kice:👇

 ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺭﺑِّﻲ ﺃﺷﺮِﻙُ ﺑِﻪِ ﺷﻴﺌًﺎ

"ALLAHU ALLAHU RABBI LA USHRIKU BIHI SHAI'AN"

Sa'annan kuma an ruwaito daga Ɗan Abbas cewa Manzon Allah (tsira da amincin Alllah su tabbata a garshi) ya kasance yana yin wannan addu'ar alokacinda ya ji kansa a yana yin damuwa:👇

 ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢُ ﺍﻟْﺤَﻠِﻴﻢُ ، ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺭَﺏُّ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢِ ، ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺭَﺏُّ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺭَﺏُّ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﺭَﺏُّ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻜَﺮِﻳﻢ

"LA ILAAHA ILL-ALLAAH AL-‘AZEEM UL-HALEEM, LAA ILAAHA ILL-ALLAAH RABB IL-‘ARSHIL-‘AZEEM, LAA ILAAHA ILL-ALLAAH RABBIS- SAMAWAATI WA RABB IL-ARD WA RABBIL-‘ARSH IL-KAREEM"

[ Muslim (2730) ]

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa: Babu wani Mutum da zai sami kansa a cikin damuwa da bakin ciki, sai ya ce:👇

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﻋَﺒْﺪُﻙَ، ﺍﺑْﻦُ ﻋَﺒْﺪِﻙَ، ﺍﺑْﻦُ ﺃَﻣَﺘِﻚَ، ﻧَﺎﺻِﻴَﺘِﻲ ﺑِﻴَﺪِﻙَ، ﻣَﺎﺽٍ ﻓِﻲَّ ﺣُﻜْﻤُﻚَ، ﻋَﺪْﻝٌ ﻓِﻲَّ ﻗَﻀَﺎﺅُﻙَ، ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺑِﻜُﻞِّ ﺍﺳْﻢٍ ﻫُﻮَ ﻟَﻚَ ﺳَﻤَّﻴْﺖَ ﺑِﻪِ ﻧَﻔْﺴَﻚَ، ﺃَﻭْ ﺃَﻧْﺰَﻟْﺘَﻪُ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺑِﻚَ، ﺃَﻭْ ﻋَﻠَّﻤْﺘَﻪُ ﺃَﺣَﺪًﺍ ﻣِﻦْ ﺧَﻠْﻘِﻚَ، ﺃَﻭِ ﺍﺳْﺘَﺄْﺛَﺮْﺕَ ﺑِﻪِ ﻓِﻲ ﻋِﻠْﻢِ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻋِﻨْﺪَﻙَ، ﺃَﻥْ ﺗَﺠْﻌَﻞَ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥَ ﺭَﺑِﻴﻊَ ﻗَﻠْﺒِﻲ، ﻭَﻧُﻮﺭَ ﺻَﺪْﺭِﻱ، ﻭَﺟَﻠَﺎﺀَ ﺣُﺰْﻧِﻲ، ﻭَﺫَﻫَﺎﺏَ ﻫَﻤِّﻲ

"ALLAHUMMA INNIY ‘ABDUKA IBN ABDIKA IBN AMATIKA, NAASIYATIY BIYADIKA, MAADIN FIYYA HUKMUKA, ‘ADLUN FIYYA ƘADAA’UKA, AS’ALUKA BIKULLI ISMIN HUWA LAKA SAMMAITA BIHI NAFSAKA, AU ANZALTAHU FIY KITAABIKA, AU ‘ALLAMTAHU AHADAN MIN KHALƘIKA, AU ISTA’SARTA BIHI FIY ILMIL GAIBI ‘INDAKA AN TAJ’ALAL ƘUR’ANA RABIY’A ƘALBIY, WA NUURA SADRIY WA JALA’A HUZNIY WA ZIHAABA HAMMIY"

Face sai Allah Ta’ala Ya tafiyar masa da damuwar shi da bakinhcikin shi, kuma Ya musanya masa da farin-ciki a maimakon su. Sai Sahabbai R.A suka ce: "Ya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shin bazamu koyawa yan'uwanmu ba saboda mahimmanci wannan adduara ba??" Sai ya ce: (Eh dukkan wanda ya ji wannan addu'ar to yana da kyau ya koyar da wanda bai sani ba).

Duba littafin al-Kalimu al-Dayyib na Sheikhul Islam Ibn Taimiyya, Rahimahullah, tahkikin Sheikh Muhammad Nasiruddeen al-Albani shafi ba 72.

To ire-iren waɗannan addu'o'in waɗanda suka tabbata daga Annabi (sallalahu alaihi wasallam) sune ake son Musulmi ya lazimci yinsu a duk lokacinda ya tsinci kanshi a cikin wani mawuyacin hali, bakin ciki, masifa ko damuwa.

ALLAH KA YAYE MANA DUKKAN KUNCI DA DAMUWA DA BAKIN-CIKI DA MATSALAR RAYUWAR DUNIYA DA LAHIRA.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments