TAƘAITACCEN TARIHIN ANNABI IDRIS (AS)
Sunansa na ainihi shi ne: Ukhnuukhu ɗan Shithu ɗan Adamu (AS).
An fara ambatonsa a cikin Alƙur’ani Maigirma a
Sura ta 19, aya ta 56-8:
“Ka tuna a cikin littafi labarin Idris (AS). Shi ya kasance mai gaskatawa ne kuma Annabin Allah (SWT). Mun ɗaukaka shi (zuwa gare mu kuma yana) a kan wani matsayi maɗaukaki.”
Daga nan sai a Sura ta 21, aya ta
85:
“Da Isma’ila da Idrisa da Zal Kifl, kowane yana daga cikin managartan
bayinmu.”
Sai kuma a Sura ta 96, a aya ta 4:
“(Allah shi ne) wanda ya sanar (da mutum) da alƙalami (wato, wanda ya ba mutum ilimi da rubutu da
karatu). (Mamman, 2014:241).
Ya kasance mai gaskatawa ne kuma annabin Allah (SWT).
Shi kakan Nuhu (AS) ne. An haife shi a zamanin da Annabi Adamu (AS) yake
raye, kafin ya mutu da shekara ɗari (100).
An ba shi annabta da misalin shekaru ɗari biyu (200) bayan wafatin
(mutuwar) Annabi Adamu (AS). Annabi Idris ya rayu bayan an ba shi annabta har
tsawon shekaru ɗari da hamsin (150).
Ibn Ishaƙ ya ce, Annabi Idris ya tarar da
wani ɓangare na rayuwar Annabi Adamu da shekaru ɗari uku da tamanin
(380).
A wani bayanin, ɗaukacin shekarunsa a duniya su ne ɗari huɗu da hamsin (450).
Ya kasance tsakaninsa da rayuwar Annabi Nuhu kimanin shekaru dubu ɗaya (1000).
An yi masa laƙabi da Idris domin shi ne wanda ya
fara karanta littafi, domin Allah (SWT) ya saukar masa da littattafai guda
talatin (30).
An ce farkon wanda ya fara rubutu da alƙalami da kuma na ram(a)li shi ne Annabi Idris (AS). Shi
ne kuma wanda ya fara ɗaukar makami ya yaƙi kafirai da shi. Shi ya fara yin nazarin ilimin taurari
da na lissafi (hisabi).
Masana sun ce wannan ya samar da abin faɗakarwa kan falalar
rubutu don amfaninsa mai yawa ga ɗan Adam, kamar wajen:
- Gane wasu lamurran suka ɓoye.
- Aje ilimi (sannai) daban-dabam.
- Taskace hikimomin ɗan Adam.
- Gane labarun mutanen farko da halayensu da tarihinsu da zantukansu.
Masana sun nuna ba don rubutu ba, da lamarin addini (ko wani na duniya) bai
tsaya daidai ba.
Allah (SWT) ya aike shi zuwa ga ɗiyan ƙabila, wanda shi ne ɗaya daga cikin
‘ya’yan Annabi Adamu (AS).
Mai yawan ibada ne, musamman ta yin azumi. An ce yawan ladar aikinsa a
kullum ta kai ta talikan zamaninsa kuma sai Allah ya yabe shi don ya ƙara duƙufa ga bautarsa.
Allah ya ɗauke shi zuwa wani matsayi a sama ta huɗu ko a gidan
aljanna, kuma a raye yake ko a halin yanzu yana ta bautar Allah (SWT) tare da
mala’iku a can sama.
An ce ya shiga aljanna bayan an ɗanɗana masa mutuwa a wani ɗan lokaci sannan
aka tashe shi kuma da ya shiga bai fito ba. Mala’ikan mutuwa ne ya kai shi a
bakin ƙofar wuta ya gan ta sannan sai kuma ya kai shi aljanna.
Da aka kai shi ya samu ya shiga sai ya ƙi fitowa, da izinin
Allah (SWT).
Bayanin Manzon Allah (SAW) a cikin wata doguwar ruwaya ta hadisinsa, game
da tafiyar dare (isra’i) da aka yi da shi, daga masallaci mai alfarma da ke
Makkah zuwa masallaci mai nisa da ke birnin Ƙudus, da kuma hawa sama (mi’iraji) da aka yi da shi don
ganawa da Allah (SWT), ya tabbatar da cewa Annabi Idris (AS) yana a sama ta huɗu ne, kamar haka:
“...sai aka hau da mu (shi da mala’ika Jibrilu) zuwa sama ta huɗu. Da Jibrilu
ya nemi a buɗe ƙofar sai aka ce da shi, “Wane ne kai?” Sai ya ce, Jibrilu
ne.” Sai aka ce, “Wa ke tare da kai?” Sai ya ce, “Muhammad ne.” Sai kuma aka
ce, “An yi aike zuwa gare shi?” Sai Jibrilu ya ce, “I, an yi aike zuwa gare
shi.” Daga nan sai aka buɗe mana, sai ga ni ga Idris. Ya yi mani maraba ya kuma yi
mani addu’a ta alheri...” (Hashiyyatus Saawiy..., Juzu’i na II, shafi na
418).
An ce Annabi Idris shi ne ya fara ɗunka tufafi. Kafin nan, mutanensa sun
kasance fatu suke yafawa a jikinsu. Allah ya yabe shi kuma ya ba shi siffa ta
siddiƙantaka (ban gaskiya ga lamarin Allah a kodayaushe).
Don ƙarn bayani, duba littafin:
1. Suyuti, J. da Muhalli, J. (2017). Hashiyyatus Saawiy ala Tafsiril
Jalalaini. Juzu’i na II, shafi na 418; Juzu’i na III, shafi na 49 da na 105;
Juzu’i na IƁ, Shafi na 447. Madaba’atu Darul
Fikr, Beirut, Lebanon.
2. An Nisaburiy, A.I. (1954). Ƙisasul Anbiya’i:
Ara’isul Majalis. Maktabatu Mustapha Alhalbiy, Misra, Egypt. Pp. 49-50.
3. Ibn Katheer, I. (2002). Ƙisasul Ambiya’i.
DarulGadeed al Jadid, Al ƙahira, Egypt. Pp.
59-61.
4. Mamman, M. (2014). Fassarar Alƙur’ani Mai Girma
Cikin Harshen Hausa. Ahmadu Bello University Press Ltd,
Zaria.
Tushe: Zauren WhatsApp na www.amsoshi.com
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.