Hausa-Fulani kalma ce da ake siffanta wata al'umma a arewacin Najeriya, wacce kuma ta daɗe tana jawo muhawara a kafofin sadarwa na zamani, wato social media.
Tambayar da ake muhawara a kai dai ita ce, "Shin ku Fulani ne ko Hausawa ko Hausa-Fulani?"
Wasu masana dai sun yi tsokaci a kan cewa babu wata ƙabila
mai suna Hausa-Fulani, ko da yake sun amince cewa mutum na da damar ya siffanta
kansa yadda ya so.
Farooq Kperogi mataimakin Farfesa ne a Jami'ar Kennesaw da
ke Atlantar Jihar Georgia ta Amurka, kuma mai bincike a kan asalin ƙabilu,
a wata hira da ya yi da BBC ya ce har yanzu ba a iya samun taƙamaiman
asalin kalmar Hausa-Fulani ba.
Ya ce, "Abin da na sani shi ne jaridun Lagos da Ibadun
ne suka sa kalmar ta shahara."
Tun a shekarar 1920 aka fara ambatar kalmar Hausa-Fulani.
Kuma a cewar Farfesa Kperogi, dalibai irin su Ahmadu Bello sun yi amfani da ita
a kwalejin Barewa sakamakon samun mutanen da a ƙabilance Fulani ne amma da Hausa suke
magana.
Kansancewar an rasa yadda za a siffanta su sai aka kira su
da Hausa-Fulani. Farfesa Kperogi ya ƙara da cewa, "ina ganin 'yan siyasar
Kudu maso yammacin Najeriya ne dalillin shaharar kalmar."
Ya cigaba da cewa hakan ya faru ne saboda wahalar tantance
asalin arewa saboda addini ya yi tasiri a wanan ɓangaren.
A kwana a tashi kalmar Hausa ta zama wata kalmar da ba ƙabila
take alamtawa ba.
Kamar yadda Dakta ya bayar da misalin cewa za a iya samun
Bayarbe ko Ibo wanda ya koma arewacin Najeriya da zama ya hayayyafa. Idan
'ya'yansa suka rungumi Musulunci suka kuma iya harshen Hausa sosai, shi ke nan
sun zama Hausawa.
Fulani da yawa sun zama Hausawa a harshe, kamar wasu mutanen
da dama.
Farfesa Kperogi ya yi bayanin cewa a yunƙurin
siffanta kaka-gidan da 'yan arewa suka yi a fagen siyasa, da farko an zaci cewa
ba Hausawa ba ne, saboda a kan basu suna Hausa Fulani.
Ya ce, "Amma kalmar ba tana nufin dunƙulewar
Hausawa da Fulani ba ne".
A haƙiƙanin gaskiya abin da ake nufi a yanzu shi ne Musulmi ɗan arewacin Najeriya mai
amfani da harshen Hausa.
Sai dai kuma wasu masanan sun ce akwai Hausawa da Fulani waɗanda ba Musulmai ba ne.
Farfesa Kperogi ya tabbatar da hakan, sai dai a cewarsa basu
da yawa. Kuma saboda yawansu bai taka kara ya karya ba, mutane ba sa lura da
hakan.
Kasancewar ƙabilar Hausa ta ɗamfara da Musulunci kuma hakan ne ma yasa a
cikin al'ummar Hausawa, waɗanda
ba Musulmi ba sai ake kiransu Maguzawa.
Duk faɗin
Afrika babu wani misali na mutanen da suka cuɗanya
ta fuskar harshe da al'adu kamar Hausawa da Fulani.
A Rwanda 'yan ƙabilar Hutu da Tutsi sun gauraya ta
hanyar auratayya, amma yawan hakan bai taka kara ya karya ba, shi yasa babu
wani abu kamar Hutu-Tutsi, saboda ko wannensu bai bar asalinsa ba.
Amma a ƙalla a Najeriya duk inda Fulani suka je, ban da kudu maso
gabas, su kan ajiye Fulatancinsu su ɗauki
al'adu da harsunan mutanen da suka samu.
Kuma kasancewar Hausa ƙabila ce da ta fi yawan mutane a Najeriya
da ma Afirka ta yamma, Fulanin da suka shiga cikinsu sun sarayar da harsunansu
da al'adunsu.
A Afirka, al'ummar Fulani su ne suka fi kowacce ƙabila
yaɗuwa a yammacin
nahiyar, ana samunsu a ko ina, amma basu da rinjaye sai a Guinea. Kuma a ƙasar
Hausa ne kawai suka yi cakuɗuwa
ta ƙut-da-ƙut har
suka sarayar da harshensu da ma ƙabilarsu
Madogara: Daga zauren WhatsApp na www.amsoshi.com
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.