Ticker

6/recent/ticker-posts

Hotunan Taron Kara Wa Juna Sani Na Kasa Da Kasa Game Da Rayuwa Da Wakokin Maza Na Makada Abubakar Kassu Zurmi

HOTUNAN TARON ƘARA WA JUNA SANI NA ƘASA DA ƘASA GAME DA RAYUWA DA WAƘOƘIN MAZA NA MAKAƊA ABUBAKAR KASSU ZURMI

Taron Kassu Zurmi
Shugaban kula da Sashen gabatar da Muƙalu ta hanyar zamani/intanet(Zoom) a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato daga Ranar Juma'a 18 zuwa Ranar Litinin 21 ga watan Afrilun 2025, Malam Ibrahim Maidamma Furfuri tare da masu taimaka masa a bakin aiki.

Kassu Zurmi
Maigirma Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Sakkwato Farfesa M B Yerima kuma babban mai masaukin baƙi ke gabatar da jawabinsa a lokacin bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Dakta Chaibou Landi
Dakta Chaibou Landi daga Jami'ar Abdoulmumini dake Yamai a Jamhuriyar Nijar ke gabatar da Muƙalarsa a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato daga Ranar Juma'a 18 zuwa Ranar Litinin 21 ga watan Afrilun 2025.
Jikan Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi, Saifullahi Rabi'u Kassu Zurmi
Jikan Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi, Saifullahi Rabi'u Kassu Zurmi ke gabatar da ƙira'ar Alƙur'ani maigirma a lokacin bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Farfesa Balarabe Zulaydaini

Babban baƙo mai jawabi a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya, Farfesa Balarabe Zulaydaini na Jami'ar Maiduguri ke gabatar da jawabinsa a wajen bikin buɗe Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.

Farfesa M B Yarima

Mai gayya mai aiki, Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Sakkwato, Farfesa M B Yarima (riƙe da takarda) a lokacin da yake shigowa Zauren gabatar da bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi wanda Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar ya shirya aka gudanar a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.

Hajiya Kulu Modi Yabo

Mai girma Magatakardar Jami'ar Jihar Sakkwato, Hajiya Kulu Modi Yabo tana duba littafin tsare-tsaren bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya, a lokacin bikin buɗe Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.

Farfesa Yakubu Aliyu Ɗanmasanin Gobir na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato (a tsakiya), mai gabatar da babbar muƙala ta biyu Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin na Fadar
Masu gabatar da manyan muƙalu a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya, mai gabatar da babbar muƙala ta farko, Farfesa Yakubu Aliyu Ɗanmasanin Gobir na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato (a tsakiya), mai gabatar da babbar muƙala ta biyu Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin na Fadar  Mai Martaba Ɗan Alin Birnin Magaji (a gefen hagu) da Alh. Abubakar Sani Sayaya Iyatanci, Ƙofar Sauri, Katsina mai gabatar da babbar muƙala ta huɗu (a gefen dama) a lokacin da suke gabatar da Muƙalun nasu Ranar Asabar 19 /04 /2025 a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato.
Farfesa Hafiz Miko Yakasai na Jami'ar Bayero Kano
Farfesa Hafiz Miko Yakasai na Jami'ar Bayero Kano(farko daga gefen dama) a ɗakin gabatar da Muƙalu( Rana ta biyu, Lahadi 20 /04 /2025) na Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar ya shirya aka kuma gudanar a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato.Farfesa B B Usman
Farfesa B B Usman shugaban Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato a ɗakin gabatar da Muƙalu na Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi wanda Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Lahadi 20/04 /2025.
Kyautar girmamawa da Jami'ar Jihar Sakkwato

Kyautar girmamawa da Jami'ar Jihar Sakkwato ta gabatar zuwa ga Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Maru da Bunguɗu a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bunguɗu wanda shi ne ya ɗauki nauyin gudanar da Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato daga Ranar Juma'a 18 zuwa Ranar Litinin 21 - 04- 2025.
An gabatar da wannan kyautar ce Ranar Asabar 19 /04 /2025 a lokacin bikin buɗe Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato.
Wani sashe na mahalarta bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya
Wani sashe na mahalarta bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Sha'iri Bello Shehu Alkanci Talata Mafara
Sha'iri Bello Shehu Alkanci Talata Mafara ke gabatar da waƙe a wajen bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Alhaji Bello Idris Chimmola
Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Sakkwato, Alhaji Bello Idris Chimmola ke gabatar da jawabin babban baƙo, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato) a wajen bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alh. Muhammad Sanusi Muhammad Ahmad Asha
Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alh. Muhammad Sanusi Muhammad Ahmad Asha ke gabatar da jawabinsa na Uban Taro a wajen bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi wanda Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Mai Martaba Sarkin Zamfaran Zurmi, Alh. Muhammad Bello Suleiman kuma Uban Taron
Mai Martaba Sarkin Zamfaran Zurmi, Alh. Muhammad Bello Suleiman kuma Uban Taron da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi a lokacin bikin buɗe Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Makaɗa Zayyanu Garba Ɗanwasa Gummi
Riƙe da turun magana Makaɗa Zayyanu Garba Ɗanwasa Gummi ne ɗaya daga cikin Makaɗan Maza da aka gayyata domin bayar da nishaɗi ga mahalarta Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a Ranar buɗen Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Wakilin Maigirma Ɗan Majalisar Wakilai
Wakilin Maigirma Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Maru da Bunguɗu ta Jihar Zamfara a Majalisar Wakilai ta Tarayya(Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bunguɗu) wanda kuma shi ne ya ɗauki nauyin Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya,  Mai baiwa Maigirma Ministan Ƙasa a Ma'aikatar Tsaro ta Tarayyar Nijeriya, Alh. Bello Muhammad Matawallen Maradun MON wato Alhaji Ibrahim Maigandi Ɗanmaliki Gidangoga farko daga gefen dama yake gabatar da jawabin Ɗan Majalisar a wajen bikin buɗe Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Halifan Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi, Alh. Mande Garba Sangamawa Zurmi
Halifan Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi, Alh. Mande Garba Sangamawa Zurmi da Ƙungiyarsa ke bayar da shaƙatawa a lokacin bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Maigirma Wakilin  Galadiman Garin Sakkwato
Maigirma Wakilin  Galadiman Garin Sakkwato memba a majalisar gudanarwar Jami'ar Jihar Sakkwato kuma ɗaya daga cikin Uwayen Taro, Alh. Aliyu Attahiru kenan a gefen hagu wato Ɗangaladiman Galadiman Garin Sakkwato, Alhaji Tukur Galadima ke tattaunawa da Wakilin Maigirma Ɗan Majalisar Mazaɓar Maru/Bunguɗu ta Jihar Zamfara a Majalisar Wakilai ta Tarayya wanda kuma shi ne ya ɗauki nauyin Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya, Hon. Ibrahim Maigandi Ɗanmaliki Gidangoga (Mai baiwa Maigirma Ministan Ƙasa a Ma'aikatar Tsaro ta Tarayyar Nijeriya, Alhaji Bello Mohammed Matawallen Maradun MON) a lokacin bikin buɗe Taron Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Alhaji Liya'u Alkali Daraktan Tsare-Tsare a Ma'aikatar Ilimi
Alhaji Liya'u Alkali Daraktan Tsare-Tsare a Ma'aikatar Ilimi mai zurfi ta Jihar Sakkwato wanda ya wakilci Maigirma Kwamishinan Ma'aikatar Farfesa Isah Muhammad Maishanu ke gabatar da jawabi a wajen bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi wanda Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya shirya a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 2025.
Wani ɓangare na mahalarta bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi
Wani ɓangare na mahalarta bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da ya gudana a harabar Jami'ar Jihar Sakkwato dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.
Farko daga gefen dama Maigirma Sarkin Sudan na Wurno memba a majalisar gudanarwar Jami'ar Jihar Sakkwato kuma ɗaya daga cikin Uwayen Taro, Alh. Kabiru Cigari Alhassan tare da Shugaban Tsangayar
Farko daga gefen dama Maigirma Sarkin Sudan na Wurno memba a majalisar gudanarwar Jami'ar Jihar Sakkwato kuma ɗaya daga cikin Uwayen Taro, Alh. Kabiru Cigari Alhassan tare da Shugaban Tsangayar Fasaha ta Jami'ar Jihar Sakkwato, Farfesa Sirajo Mohammed a wajen bikin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da aka gudanar a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 2025.
Farfesa Bello Bada
Farfesa Bello Bada memba a Majalisar gudanarwar Jami'ar Jihar Sakkwato wanda ya wakilci shugaban Taro kuma shugaban hukumar gudanarwar Jami'ar, Amb. Abubakar Muhammad Sani Makaman Sakkwato a lokacin da yake gabatar da jawabi wajen buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da aka gudanar a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19/04 /2025.
Alhaji Yahaya Sarkin Makafin Zurmi ne tare da Shugabar Kwamitin Shirya Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi
Farko daga gefen dama Alhaji Yahaya Sarkin Makafin Zurmi ne tare da Shugabar Kwamitin Shirya Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi wanda Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Jihar Sakkwato ya  shirya daga Ranar Juma'a 18 zuwa Ranar Litinin 21-04-2025 a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato, Farfesa Aliyah Adamu Ahmad, na farko a gefen hagu kuma ɗan Marigayi Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi ne Mal. Aliyu. An ɗauki hoton ne a lokacin da aka gabatar da manyan muƙalu na Taron.
Maigirma Yariman Ɗankanjiba Alh. Ibrahim Abdulƙadir Yammama
Farko daga gefen hagu Maigirma Yariman Ɗankanjiba Alh. Ibrahim Abdulƙadir Yammama, a tsakiya Mal. Aliyu Abubakar Kassu Zurmi (ɗan Marigayi Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi) tare da Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji na farko a gefen dama a ranar Asabar 19 /04 /2025 wajen Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da ya gudanar a Jami'ar Jihar Sakkwato dake Birnin Sakkwato.
Alh. Ibrahim Ƙofa Birnin Magaji
Na farko daga gefen hagu shine Alh. Ibrahim Ƙofa Birnin Magaji. Jika ne ga Ɗan Tauri Mai Babarbara Shehu Ɓuraguji Birnin Magaji wanda Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi ya yiwa Waƙa. An ɗauki wannan hoto ranar Lahadi, 20/04 /2025 a lokacin da ake ci gaba da gabatar da Muƙalu a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi a Jami'ar Jihar Sakkwato dake Birnin Sakkwato.
Maigirma Ɗangaladiman Galadiman Garin Sakkwato
Maigirma Ɗangaladiman Galadiman Garin Sakkwato, Alhaji Tukur ya na gabatar da jawabin Maigirma Galadiman Sakkwato memba a Majalisar gudanarwar Jami'ar Jihar Sakkwato kuma ɗaya daga cikin Uwayen Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi a lokacin bikin buɗe Taron da ya gudana a harabar Jami'ar dake Madorawa, Sakkwato Ranar Asabar 19 /04 /2025.

Post a Comment

0 Comments