Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Sa Kayan Sata

TAMBAYA (230)

Assalamualaikum. Dan Allah INa da tambaya tambaya na shi ne mene ne hukunci Wanda ya sa kayan sata Amman daga baya sai ya zo ya yi nadama shin Malam ya matsayin to tubarsa

AMSA

Waalaikumus salam, warahmatullahi, wabarakatuhu

Allaah Azzawajallah yana yafe kowanne irin laifi in dai ba wanda mutum ya mutu yana shirka ba da kuma laifin dake tsakanin bawa da bawa

Wannan hakki ne kuma idan ba a biya mai shi anan duniyar ba to ranar lahira za a biya mai kayan da sallah, azumi ko sadakar wannan wanda ya danne masa hakkin

Idan kuma ladan ba su kai na hakkin ba to za a dauki zunubban mai kayan a jibgawa wanda ya dannewa hakkin

Don haka a shawarce a gaggauta mayarda kayan ga mamallakin sa

Idan kuma ba a san inda za a same shi ba sai ayi sadaka da niyyar Allaah ya sa ladan a mizanin mai kayan

Wallaahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments