Babu abin da zai hada kai sai gaskiya. Da a ce mutane za su hadu a kan gaskiyar da Allah ya saukar da ita ga Manzanninsa, gaskiyar da don ita ya halicci halittu, don ita ya aiko Manzanni, don ita ya saukar da Littatafai, don ita sammai da kasa suka tsaya to da ba a samu rarrabuwa da sabani ba. Amma sai wasu mutane suka dauki rabin gaskiya, suka bar daya rabin, haka wasu ma, suka dauki gaskiyar da wadancan suka bari, suka yi watsi da gaskiyar da suka dauka.
Misali: Mushrikai suka ce: Allah yana da girma,
yana da matsayi, don haka bai kamata a isa gare shi kai tsaye ba. Don haka dole
ne a sanya tsani zuwa gare shi, da wanda zai yana yi wa mutane iso gare shi.
Kamar yadda Allah ya ce:
{وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِهِ أَوْلِيَاءَ مَا نَعْبُدُهُمْ
إِلَّا لِيُقَرِّبُونَا إِلَى اللَّهِ زُلْفَى} [الزمر: 3]
((Wadanda suka riki ababen bauta koma bayan Allah,
(sukan ce:) ba don komai muke bauta musu ba sai don su kara mana kusaci zuwa ga
Allah, (su cece mu))).
To ka ga akwai nau’in gaskiya a cikin maganarsu,
shi ne cewa; Allah yana da girma, amma rikan wani tsani da za kana tawassuli da
shi, tsakaninka da Allah wannan shi ne karyar da Allah ya aiko Manzanni don
yakarta. Wato shirka.
Don haka shi ya sa mutane suka yi sabani, suka
rabu gida biyu, tsakanin Masu Tauhidi Mabiya Annabawa da Manzanni, da kuma
Mushrikai mabiya Shaidanu, kuma masu bautar ababen bauta daban-daban. Amma da a
ce duka mutane za su riki gaskiyar Tauhidi to da kai ya hadu, ba a samu Addinai
sabanin Addinin dukkan Annabawa da Manzanni ba, wato Addinin Muslunci.
To haka idan ka kalli Bidi’a ma, da a ce: dukkan
Musulmai sun hadu a kan gaskiyar Sunnar Annabi (saw), da ba a rabu
kungiya-kungiya ba. Amma kowace kungiya sai ta yi riko da rabin gaskiya, ta yi
watsi da daya rabin.
Misali: Khawarijawa suka yi riko da rabin gaskiya,
suka yi riko Nassoshin alkawarin Azaba ga mai sabo (Wa’eedi), suka yi watsi da
daya rabin, suka yi watsi da Nassoshin alkawarin rahama da Aljanna ga masu
sabon (Wa’adi). Wanda a kan wannan suka gina manyan bidi’o’insu na kafirta
Musulmai, da fita daga Jama’ar Musulmai da halasta jinanensu.
Haka Rafidha ‘Yan Shi’a, suka yi riko da rabin
gaskiya, suka yi riko da son Ahlul Baiti, sai kuma suka yi watsi da daya rabin,
suka yi watsi da sauran Sahabban Annabi (saw), suka kafirta su, suka yi Guluwwi
a game da Aliyu (ra) da sauran ‘yan’yansa, suka ba su matsayin Isma, kai har
matsayin Allah, suka rinka zuwa kabarburansu suna bauta musu.
Haka idan ka dauki Sufaye da son Annabi (saw) da
son Waliyyai, wannan gaskiya ne, amma sai suka yi guluwwi a hakkin Annabi
(saw), da kuma Waliyyansu. Suka bai wa fasikai matsayin Walittaka, suka ba su
matsayin Allah, da manyan matsayin da a bisa hakika sun fifita su a kan
Annabawa da Manzanni. Suka rinka zuwa kabarburansu suna bauta musu, suna
rokonsu biyan bukata, da sauran abubuwan da babu mai iko a kansu sai Allah.
Ko wannan Maulidi da suke yi, a cikinsa akwai riko
da rabin gaskiya, wato yin bikin da suke yi bisa niyyar son Annabi (saw), amma
kuma sun yi watsi da daya rabin gaskiyar, wato nisantar kirkiran bidi’a a
Addini da sunan bikin murnan haifuwar Annabi (saw).
To haka lamarin yake a kowane babi, idan an rike
gaskiya gaba daya to ba za a samu sabani da rabuwar kai ba, amma idan kowane
bangare ya rike sashi na gaskiya, ya bar daya sashin, to dole a samu sabani da
rarrabuwa.
Misali a kan haka na abin da ke faruwa a tsakanin
masu dangantuwa ga Sunna a yau, musamman tsakanin ‘Yan Kungiyar Salafiyyun
(Madakhila) da kishiyoyinsu; ‘Yan Ikhwan, Sururiyya da sauransu, kowane bangare
ya riki rabin gaskiya, ya yi watsi da daya rabin da yake wajen abokin
husumarsa.
Misali a kan haka: Daga cikin abin da ya haifar da
sabani akwai Manhajin da ‘Yan Madakhila suke bi na "Jarhi da Ta’adili",
wanda yake dauke da ma’anar zargin karkatattu a Sunna da Addini. Lallai ko
shakka babu, duk wanda ya saba ma Sunna sabawa bayyananniya dole a zarge shi, a
bidi’antar da shi.
To sai Madakhila suke zargi da aibanta duk wanda
ya saba wa Kungiyarsu, ta hanyar kiransa da sunaye daban-daban, alal akalli za
su kira shi "Hizbiy", bisa ma’anar dan Bidi’a. Sai suka wayi gari
cikin guluwwi a bidi’antarwa, saboda bidi’antar da Malamai Ahlus Sunna da
sukarsu ba bisa hujja ba.
Su kuma ‘Yan Ikhwan da Sururiyya sai suka saba
musu, suke kare dukkan karkataccen da wadancan suka soka, ko da kuwa karkacewar
tasa a fili take.
Alhali akwai da yawa daga cikin wadanda Madakhila
suke bidi’antarwa ba su cancanci suka ba, balle Bidi’antarwa. Kamar yadda akwai
da yawa cikin wadanda ‘Yan Ikhwan da Sururiyya suke karewa ido rufe sun cancanci suka da Bidi’antarwa.
Misalinsu su ne Sayyid Qutub, Qardhawiy da sauransu. Shaikhul Islam ya ce:
((من خالف الكتاب المستبين والسنة المستفيضة أو ما أجمع عليه سلف
الأمة خلافا لا يعذر فيه فهذا يعامل بما يعامل به أهل البدع)).
مجموع الفتاوى (24/ 172)
((Duk wanda ya saba wa Ayar Alkur’ani
bayyananniya, ya saba ma Hadisi da ya zo ta hanyoyi masu yawa, ko ya saba Ijma’in
Salaf, sabanin da ba za a iya yi masa uzuri ba, to wannan za a yi masa mu’amala
da abin da za a yi mu’amala da shi wa ‘Yan Bidi’a)).
Saboda haka duk lokacin da ba za a karbi gaskiya
gaba dayanta ba, ko ba za a karbi gaskiyar da take wajen abokin jayayya da
husuma ba, to ba za a rabu da sabani abin zargi, da rabuwar kai abin zargi ba.
Shi ya sa Ibnu Taimiyya ya ce:
((علينا أن نؤمن بكل ما جاء من عند الله ونقر بالحق كله ولا يكون
لنا هوى ولا نتكلم بغير علم؛ بل نسلك سبل العلم والعدل وذلك هو اتباع الكتاب والسنة؛
فأما من تمسك ببعض الحق دون بعض فهذا منشأ الفرقة والاختلاف)).
مجموع الفتاوى (4/ 450)
((Wajibi ne a kanmu mu yi imani da dukkan abin da
ya zo daga Allah, mu karbi gaskiya gaba dayanta, bai halasta gare mu mu yi
magana bisa son rai ba, kuma bai halasta mu yi magana ba tare da ilimi ba. A’a,
sai dai mu bi hanyar ilimi da adalci, hakan kuwa shi ne Bin Alkur’ani da Sunna.
Amma duk wanda ya yi riko da sashen gaskiya, ya bar sashe, to wannan abin da ya
yi shi ne tushen rarrabuwar kai da sabani)).
Saboda haka hanyar Bin Manzon Allah (saw) ita ce
bin gaskiya gaba dayanta, ba riko da sashenta da watsi da wani sashen nata ba.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani Misau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.