Ticker

6/recent/ticker-posts

Malamai Ahalis Sunnah

A da Malaman Ahlus Sunna suna samun shahara ne saboda matsawa a kan kira ga Tauhidi da Sunna, da raddi ga masu shirka, masu zuwa kabarburan shehunai suna rokonsu biyan bukata, da raddin bidi’o’i, da sauran almaran Sufaye. Shi ya sa har yau Sufaye suna cike da jin haushin Malam Kabir Gombe, da ire - irensa wadanda suke bin wannan Manhaji, na rashin sassauci wajen inkarin Shirka da Bidi’o’in Sufaye. Kai, haka Malam Ja’afar ma, babban misali.

Abin takaici, a yau Malamai masu dangantuwa ga Sunna, suna samun shahara ne da wa’azozin mata, da na ma’aurata, a ciki har da fadin abubuwan da bai dace kamilin mutum yana fada a bainar jama’a ba, idan ba da bukata ta musamman ba, kuma ba da wargi ba. Wasu kuma sun shahara da yawan ba da labaru, har ya kai ga ana fara jin labari mai hatsari a bakin Malami mai wa’azi, alhali idan aka yi bincike labarin bai tabbata ba. Wasu sun zama ‘yan comedy, masu barkwanci da ba da dariya wa ‘yan mata da samari, a kan kujerar wakiltar Manzon Allah (saw), suna fadin yasassun maganganu, wasu ma irin na ‘yan tasha, don birge ‘yan mata da samarin, suna status da clip na bidiyonsu. Wasu ka ji suna fatawa a kan abubuwan da ba su da ilimi a kansu. Wani lokaci har da zagi, alhali a Masallaci dakin Allah suke.

Amma asalin Malamai da suke karantarwa, wanda babu tarkace a cikin karatunsu, sai ka samu gama

-garin mutane ba su cika mai da hankali a kansu ba, duk da muhimmancin abin da suke karantarwa, na Akida da Ibada da Tarbiyya, da hanyar gyaran zuciya, don al’umma ta gyaru, har a samu saukin rayuwa da iznin Allah.

Saboda haka muna kira ga manyan Malamanmu - duk da cewa muna kyautata zaton suna iya kokarinsu na Nasiha ga irin wadancan Malamai - su kara kaimi wajen jan hankali gare su, kar su gajiya, da fatan Allah zai sa su gyara.

Kuma ni ma daga wannan minbari na Facebook, ina gabatar da Nasiha ga dukkan Malamin da ya san yana bin solo irin wadancan salo da suka saba salo mai kyau, ya ji tsoron Allah ya gyara. Saboda a zamanin yanzu al’umma ta fi bukatar gyara Akida da Tarbiyya fiye da sauran babukan Addini, balle kuma barkwanci da comedy da ba da dariya wa mutane.

Aiki Ne Abin Lura Ba Sunayen Kungiyoyin Addini Ba

Cikakken sunan Kungiyar Izala bai zo a cikin Alkur'ani ko Sunna ba, kamar yadda sunan Salafiyya ma bai zo a cikinsu ba. Amma ma'anar sunan Izalar ta dace da ma'anar Sunna, kamar yadda ma'anar sunan Salafiyya ta dace da Tafarkin Salaf, wato tafarkin da suke bi na Sunna.

Saboda haka, ba suna ba ne abin lura, aiki da hakikanin sunan shi ne abin lura.

A yau in da Dan Kungiyar Salafiyya zai cika Duniya da kururuwar cewa: ba ruwansa da Kungiyar Izala, amma kuma ya riki tafarkin Salaf yana binsa gwargwadon iko, haka shi ma Dan Izala ya yi yekuwar cewa: ba ruwansa da 'Yan Kungiyar Salafiyya amma kuma ya riki tafarkin Sunna yadda ya kamata to ko shakka babu duka su biyun a kan tafarki daya suke, tafarki madaidaici, kuma babu yadda za a yi daya ya kori daya daga tafarkin.

Don haka kawai hakikanin abin da zai hana 'Yan Kungiyar Salafiyya zama 'Yan Kungiyar Izala shi ne neman daukaka da son shugabanci ko kuma rashin fahimtar hakikanin Salafiyyar.

Saboda haka, ba sunan kungiya ne abin lura ba, abin lura shi ne riko da hakikanin ma'anar sunan tare da aiki da shi.

Saboda haka, zafin kai da wasu matasa suke yi a kan Kungiyar Izala da sunan Salafiyya duka kawai rashin sanin hakikanin Salafiyyar ne.

Daga karshe muna tunatar da dukkan mabiya Sunna da tafarkin Salaf cewa; Allah ya wajabta mana bin Sunna da Shari'a ne tare da hadin kai a cikinsu ba tare da rarrabuwa ba.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments