Ticker

6/recent/ticker-posts

Iddah Da Takaba A Musulunci: Iddar (Takabar) Macen Da Mijin Ta Ya Mutu

TAMBAYA

Assalamualaikum warahamatullah wabarakatouh ya Malam, da fatan alkhair.

Tambaya ta anan itace:-

1_ Me nene iddah

2_ Yaya ake yinta bisa Sunnah

3_ Yaushe ake farawa

4_ Yaushe ke dai nawa

5_ Mai nene abin da shari’a ta hana mai mace mai yin iddah tayi da kuma ta bari

AMSA

 1:- MA’ANAR IDDA A YARAN LARABCI DA SHARI’A

Iddah a harshen larabci suna ne na "masdari" daga Kalmar "adda, ya’uddu, addan" wanda aka ciro shi daga "adadi da ƙididdiga" saboda "iddah" ta ƙunshi: adadi ƙididdigagge na: jini ko tsarki, da na watanni.

A shari’ar Musulunci kuma "iddah": suna ne na wani lokaci aiyananne da mace za ta zauna a cikinsa; da nufin bautawa Allah mabuwayi da daukaka, ko don alhinin rasuwar miji, ko don ta tabbatar cewa ba komai a mahaifarta.

  ABUBUWAN DA SUKE SAWA AYI IDDAH

1-RASUWA, 2- SAKIN HAURE

"Iddah" tana kasancewa ne bayan rasuwa ko shika.

 DALILAN DA SUKA SHAR’ANTA YIN IDDAH

Dalilan da suka wajabta yin iddah sun zo ne a cikin alƙur’ani da sunna, da kuma, ijma’i.

1:-Amma daga alƙur’ani; to akwai fadin Allah maɗaukakin sarki:

وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ ثَلَاثَةَ قُرُوءٍ ۚ (البقرة 228:2)

(Matan da aka riga aka sake za su dakatar da kansu na tsawon tsarki uku) [Baƙarah: 228].

 2:-Da kuma saboda faɗinsa:-

وَاللَّائِي يَئِسْنَ مِنَ الْمَحِيضِ مِنْ نِسَائِكُمْ إِنِ ارْتَبْتُمْ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَاثَةُ أَشْهُرٍ وَاللَّائِي لَمْ يَحِضْنَ ۚ وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَنْ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مِنْ أَمْرِهِ يُسْرًا (الطلاق 4:65)

(Waɗanda suka debe tsammani daga haila daga cikin matanku, iddansu wata uku ne, haka suma yara mata da basu fara haila ba. Su kuma ma’abota ciki lokacinsu na idda shine su sauke cikinsu) [Ɗalaƙ: 4]

3:-Da kuma saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki:

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ (البقرة 234:2)

(kuma Wadanda suka mutu daga cikinku, suka kuma bar mata na aure, (su mata) za su yi zaman jira na watanni guda hudu da kwana goma. (A matsayin takaba) [234].

4:-Amma dalilin iddah daga sunna kuma: Shine hadisin Almiswar dan Makhramata (r.d) yana cewa:

"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ(رضي الله عنها) نُـفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِلَيَال، فَجَاءَتِ النَّبِيَّ, فَاسْتَأْذَنَتْهُ أَنْ تَنْكِحَ، فَأَذِنَ لَهَا فَنَكَحَتْ" رواه البخاري (رقم/5320).

Ma’ana: (Haƙiƙah Subai’ah al-aslamiyyah {r.d} ta haihu bayan rasuwar mijinta da ‘yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi {s.a.w} tana neman izininsa akan za ta yi aure, sai yayi mata izini, sai kuma ta yi aure) {bukhari ne ya rawaitu shi a hadisi mai lamba ta 5320}.

  HIKMAR DA TA SA AKA SHAR’ ANTA IDDAH

=Hikimar hakan itace: Domin tabbatar da cewa babu komai a cikin mahaifar mace (juna biyu) domin kada a samu chakudar nasaba.

= Yana kuma daga cikin hikimar: Bada dama ga mijin da yayi sakin ya waiwayi kansa idan yayi nadama, sai ya mai da matar sa cikin igiyar auran sa, wannan kuma idan sakin da ya aiwatar ana iya kome a cikinsa (na ɗaya da na biyu ne).

=haka kuma: Lura da haƙƙin ciki dana jariri, idan har an rabu, ko an mutu an bar mace da ciki.

NAU’UKAN {IDDAH}

=Iddodin da mata ke yi sun kasu kashi biyu:

(1) Iddan mutuwa (takaba)

(2) Iddan rabuwar aure.

Na farko: Iddan mutuwa (takaba): Wannan kuma shine: iddar da take wajaba ga matar da mijinta ya rasu ya bar ta, (kenan zamu fahimci iddar itace takabar kuma takabar ita ce iddar kenan duk abu daya ne ga wace mijin ta ya rasu) shi kuma halin matar da mijin ta ya rasu baya fita daga dayan halaye guda biyu:

(1)Ko wannan matar ta zama tana da ciki.

(2)Ko kuma ta zama bata da ciki.

Idan har ta kasance tana da ciki: To iddarta zata ƙare ne in ta haife abinda ke cikinta; koda kuwa bayan wassu ‘yan-dakiƙoƙi ne daga rasuwar mijin nata, wannan kuma saboda faɗin Allah madaukakin sarki:

وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَنْ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ (الطلاق 4:65)

Ma’ana: (Su kuma ma’abota ciki lokacinsu na idda shine su sauke cikinsu) {dalaaƙ 4:}

kuma saboda da hadisin Almiswar dan Makhramata (r.d) yana cewa:

"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ(رضي الله عنها) نُـفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِلَيَال، فَجَاءَتِ النَّبِيَّ, فَاسْتَأْذَنَتْهُ أَنْ تَنْكِحَ، فَأَذِنَ لَهَا فَنَكَحَتْ" رواه البخاري (رقم/5320).

Ma’ana: (Haƙiƙah Subai’ah al-aslamiyyah {r.d} ta haihu bayan rasuwar mijinta da ‘yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi {s.a.w} tana neman izininsa akan za ta yi aure, sai yayi mata izini, sai kuma ta yi aure) {bukhari ne ya rawaitu shi a hadisi mai lamba ta 5320}.

kenan zamu fahimci ita mace mai ciki da zaran mijin ta ya mutu sai kuma ta haihu to ita ta gama takabar ta (iddar ta).

wannan ita ce fahimtar dukkan malaman sahabbai (Allah ya kara yarda da su) ban da (abdullahi dan abas da aliyu dan abi dalib) hakama dukkan malamai fahimtar su kenan, {Allah yai musu rahama)Ban da malan sahnuun almaalikey" {A duba sharhin muslim juz’i na 10 shafi na 109}

=Idan kuma ta kasance bata dauke da wani ciki: To iddar ta zata kasance ne tsawon watanni huɗu da kwanaki goma,(wato kwana dari da talatin 130) lallai matar da mijinta ya mutu ya barta ba tada ciki dole ne zata yi wannan takabar, da daya ne ya sadu da ita, ko kuma bai taba saduwa da ita ba; saboda gamewan fadin Allah ta’alah:

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِي أَنْفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (البقرة 234:2)

(kuma Wadanda suka rmutu daga cikinku, suka kuma bar mata na aure, (su mata) za su yi zaman jira na watanni gudu da kwana goma. (A matsayin takaba) to idan sun cika wa’adinsu, babu laifi a kanku (waliyyan su) cikin duk abun da suka aikata game da kawunan su ta HANYAR da aka saba (a shari’a). Kuma Allah mai cikakken sani ne game da abun da kike aikatawa [Baƙarah: 234].

Kuma babu wani dalili da ya zo da kebance wata mace daga hakan.

= IDDAR MARA CIKI A YAYIN DA MIJIN TA YA MUTU

Idan kuma ta kasance bata dauke da wani ciki: To iddanta zai kasance ne tsawon watanni huɗu da kwanaki goma, lallai matar da mijinta ya mutu ya barta ba ciki dole zata yi wannan takabar; sawa’un ya sadu da ita, ko kuma bai taba saduwa da ita ba; saboda gamewan faɗin Allah ta’alaa:

 

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِي أَنْفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (البقرة 234:2)

(kuma Wadanda suka rmutu daga cikinku, suka kuma bar mata na aure, (su mata) za su yi zaman jira na watanni gudu da kwana goma. (A matsayin takaba) to idan sun cika wa’adinsu, babu laifi a kanku (waliyyan su) cikin duk abun da suka aikata game da kawunan su ta HANYAR da aka saba (a shari’a). Kuma Allah mai cikakken sani ne game da abun da kike aikatawa [Baƙarah: 234].

babu wani dalili da ya zo da keɓance wata mace daga hakan.

HUKUNCE-HUKUNCEN IDDAR MACIN DA MIJIN TA YA MUTU YA BARTA

Lallai hukunce-hukuncen da suke tafe suna lazimtar matar da take iddar rasuwar mijinta:

1: Wajibi ne akanta ta yi takaba (idda) a gidan da mijinta ya rasu a cikin sa, alhalin tana cikinsa, koda kuwa gidan haya ne ko na aro, wannan kuma saboda faɗinsa (s.a.w) ga Furii’ah bnt Malik - رضي الله عنها-:

"امْكُثِي فِي الْبَيْتِ الَّذِي أَتَاكِ فِيهِ نَعْيُ زَوْجِكِ ..." {صحيح أبي داود الصفحة أو الرقم: 2300}خلاصة حكم المحدث : صحيح

Ma’ana: (Ki zauna a gidan da labarin mutuwarsa ya zo miki kina zaune a cikinsa). Kuma baya halatta ta fita daga wannan gidan; ta koma wani gidan na daban sai idan da akwai uzuri; kamar ta ji tsoron wata matsala in har ta ci gaba da wanzuwa a cikin wannan gidan, ko kuma a fitar da ita da ƙarfi, ko makamancin haka; to a nan ya halatta ta koma gidan da ta so, saboda wannan larurar.

2: Lazimtar gidanta da take takaba a cikinsa, da kuma haramcin fita daga cikinsa , sai dai in da buƙatar hakan, In kuma da buƙatar to yana halatta a gare ta, ta fita daga gidan da rana, ba da daddare ba, saboda dare lokaci ne da aka fi zaton barna a cikinsa, don haka baya halatta ta fita a cikinsa sai inda "larura"; saɓanin rana, saboda shi lokaci ne na fita biyan buƙatu.

3:Wajibi ne akanta ta dena yin ado na tsawon watannin iddah. Kamar yadda bayani mai fadi zai zo akansa lokacin bayani akan (Ihdaad).

4: Bata da haƙƙin ciyarwa, saboda aure na ƙarewa da aukuwar mutuwa.

Mas’ala ta biyu: Zaman takaba (Al-ihdaad):

Menene zaman takaba? da dalilai da suka shar’anta shi:

1: Bayani a kan "ihdaad":

"Ihdaad" a harshen larabci shine "hanuwa", Ana cewa: "Haa-ddun, Muhiddun" wa mace idan ta bar amfani da kayan ado, da tirare. A shari’ar Musulunci kuma: Shine mace ta bar yin ado, da fesa ko shafa turare, da wasun wannan na daga abubuwan da zasu sanya a yi kwaɗayinta, ya kuma jawo hankali zuwa ga saduwa da ita.

"2: Dalilai da suka shar’anta yin "ihdaad": Yin zaman takaba (Ihdaad) wajibi ne akan matar da mijinta ya rasu, saboda hadisinUmmu-habibah - رضي الله عنها- lallai Annabi (s.a.w) yace:

"لاَ يَحِلُّ لامْرَأَةٍ تُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَاليَوْمِ الآخِرِ أَنْ تُحِدَّ عَلَى مَـيِّتٍ فَوْقَ ثَلاَثِ لَيَالٍ، إِلا عَلَى زَوْج أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا" (متفقٌ عليه.)

Ma’ana: (Baya halatta ga wata mace da ta yi imani da Allah da kuma ranar karshe, da ta yi takaba (nisantar ado) ga rasuwar wani mutum na fiye da kwanaki uku, sai dai ga miji; wata huɗu da kwanaki goma).{bukhar da Muslim ne suka rawaitu shi}

Da kuma hadisin Ummu-aɗiyyah al-ansaariyyah - رضي الله عنها- tace:

"كُنَّا نُنْهَى أَنْ نُحِدَّ عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ ثَلاَثٍ إِلا عَلَى زَوْجٍ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ، وَلاَ نَـكْتَحِل وَلاَ نَتَطَيَّبَ وَلاَ نَلْبَسَ ثَوْبًا مَصْبُوغًا، إِلا ثَوْبَ عَصْبٍ..."الحديث(متفق عليه)

Ma’ana: (Mun kasance ana hana mu muyi takaba ga wani na fiye da kwanaki uku, sai dai miji, watanni huɗu da kwanaki goma, bama sanya kwalli, bama shafa tirare, bama sanya tufa da aka rina, sai dai tufan gwado –da aka rina zanensa gabanin a ɗinka shi-…).

Matar da take zaman "Ihdadi" da takaba yana wajaba akanta: Ta nisanci kayan ado da tirare, tare da hanuwa daga sanya tufofi ma’abota launuka masu ƙayatarwa, haka kuma ba za ta sanya tozali ba, ba za ta sanya sarkar ado na zinare ko azurfa ko wassunsu ba, kamar yadda baya halatta ta sanya wani abu na kayan da aka rina, saboda hadisin Ummu-salamah - رضي الله عنها-, daga Annabi (r) yace:

""الْمُتَوَفَّى عَنْهَا لا تَلْبَسُ الْمُعَصْفَرَ مِنَ الثِّيَابِ، وَلا الْمُمَشَّقَةَ، وَلا الْحُلِيَّ وَلا تَخْتَضِبُ وَلا تَكْتَحِلُ".. [المحدث:الألباني

المصدر: صحيح أبي داود الصفحة أو الرقم: 2304 *خلاصة حكم المحدث:صحيح]

Ma’ana: (Macen da mijinta ya rasu a kwanakin takaba bata sanya kayan da aka rina su da "asfar" launin ɗorawa-", da wanda aka rina da "mishƙu", wani launi ne ja", da kayan awarwaro, haka kuma bata yin lalle, ko sanya tozali).

Da kuma saboda hadisin Ummu-aɗiyyah al-ansaariyyah - رضي الله عنها-, wanda ba da jimawa ba ya gabata. Wajibi ne ta lazimci gidanta da take idda ko takaba a cikinsa, kuma ba zata fita daga cikinsa ba sai dai idan akwai buƙatar hakan, saboda hadisin Furii’ah bnt Malik رضي الله عنها- wanda ambatonsa ya gabata.

2=IDDAR RABUWAR AURE

Na biyu: Iddar rabuwar aure: Wannan kuma itace iddar da take wajaba akan matar da ta rabu da mijin ta, ko don saboda raba auren, ko don saki, ko don "khul’in" da ya mata bayan saduwa, lamari irin na rabuwar aure ba ya fita daga dayan wadannan halaye:

=Ko mijinta ya rabu da ita alhalin tana da ciki

=Ko babu ciki.

=Ko ya zama bata ganin haila:- ko saboda ƙan-ƙanta, ko ta debe tsammaninsa; saboda tsufa.

IDDAR MAI CIKI

In har ta kasance tana da ciki: To iddarta zata ƙare ne idan ta haife cikinta; wannan kuma saboda gamewar faɗin Allah ta’alah:

وَأُو۟لَـٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن یَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ

[Surah A-alāƙ: 4]

Kuma mata da suke da ciki lokacin fitar su daga idda shi ne su haife abin da ya ke cikin su [Surah A-alāƙ: 4].

IDDAR MACI MARA CIKI WADDA TAKE YIN AL,ADA (JININ HAILA)

In kuma bata da ciki, alhalin kuma wannan matar tana cikin masu yin haila: To iddarta zata kammalu ne idan ta yi tsarki guda uku, bayan rabuwansu; wannan kuma saboda faɗinsa Allah madaukakin sarki:

وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ ثَلَاثَةَ قُرُوءٍ ۚ وَلَا يَحِلُّ لَهُنَّ أَنْ يَكْتُمْنَ مَا خَلَقَ اللَّهُ فِي أَرْحَامِهِنَّ إِنْ كُنَّ يُؤْمِنَّ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۚ (البقرة 228:2)

Ma’ana: (Mata da aka sake suna zaunar da kansu na tsawon tsarki guda uku, kuma baya halatta a gare su da su ɓoye abinda Allah ya halitta a cikin mahaifarsu, matuƙar sun yi imani da Allah da kuma ranar ƙarshe) [Baƙarah: 228].

 IDDAR MACIN DA BATA GANIN JININ AL’ADA (JININ HAILA)

In kuma ta kasance bata ganin haila: saboda kasancewarta mai kananan shekaru, ko kuma ta Ɗebe tsammanin ganinsa saboda yawan shekarunta: To iddarta zai ƙare ne idan watanni uku suka shige bayan rabuwan ta da mijinta, wannan kuma saboda faɗinsa maɗaukaki:

{ وَٱلَّـٰۤـِٔی یَىِٕسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِیضِ مِن نِّسَاۤىِٕكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَـٰثَةُ أَشۡهُرࣲ وَٱلَّـٰۤـِٔی لَمۡ یَحِضۡنَۚ}[Surah A-alāƙ: 4]

Ma’ana: (Waɗanda suka ɗebe tsammani daga haila daga cikin matanku, iddarsu watanni uku ne, haka suma yara mata da basu fara haila ba) [ɗalaƙ: 4].

HUKUNCIN MATAR DA AKA SAKE TA GABANIN SADUWA DA ITA

Idan miji ya rabu da matarsa; ko don saboda raba aurensu da aka yi, ko kuma saki ne gabanin saduwa da ita, to a nan babu wani idda akanta: wannan kuma saboda faɗinsa madaukakin sarki:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِنْ قَبْلِ أَنْ تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّةٍ تَعْتَدُّونَهَا ۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا (الْأحزاب 49:33)

Ma’ana: (Yaku waɗanda suka yi imani idan har kuka auri mata muminai, sa’annan sai kuka sake su gabanin ku sadu da su, to baku da wata idda da zaku nemi su yi, sai ku jiyar da su daɗi, sai ku sake su saki mai kyau) [Ahzaab: 49].

A wannan hukunci (rashin idda ga wacce aka rabu da ita alhalin ba a sadu da ita ba) babu banbancin tsakanin mata muminai da ahlul-kitaabi, kamar yadda maluma suka yi ittifaƙi. Shi kuma ambaton "mata muminai" a cikin ayar da aka yi don rinjayar da su ne akan sauran.

MAS’ALA TA UKU:

 HAƘƘOƘIN DA SUKE CIKIN IDDA, DA ABUBUWAN DA SUKE RATAYA AKANSA:

1-Iddan aka saki mace zata kasance tana idda ne ga mijinta iddah ta saki, to halinta baya fita daga ɗayan lamari guda biyu:

1: Sakinta ya kasance na kome ne.

2: Sakin da aka yi mata ya zama ba na kome ba ne (ba’inu).

Na farko: Matar da take idda daga saki da ake iya kome a cikinsa: Wannan matar hukunce-hukuncen da suke tafe suna rataya akan iddarta:

1: Wajabcin bata gurin zama tare da mijinta, matuƙar babu wani abinda zai hana haka a shari’ance.

2:Wajabci ciyar da ita, da tufatar da ita, da makamantansu.

*3:Kuma wajibi ne akanta ta lazimci wajen zamanta, ya zama bata rabuwa da shi, sai dai idan da larura; wannan kuma saboda faɗinsa madaukakin sarki:

أَسْكِنُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ سَكَنْتُمْ مِنْ وُجْدِكُمْ (الطلاق 6:65)

Ma’ana: (Ku zaunar da su a wurin da kuke zaune gwargwadon samunku) [Ɗalaƙ: 6]. Da kuma saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki:

لَا تُخْرِجُوهُنَّ مِنْ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخْرُجْنَ إِلَّا أَنْ يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ ۚ (الطلاق 1:65)

Ma’ana: (Kada ku fitar da su daga ɗakunansu, kada suma su fita sai dai in sun zo da wata alfasha mabayyaniya) [Ɗalaƙ: 1].

4:Haramun ne akanta ta riƙa bijiro da kanta ga wasu mazaje don su nemi aurenta, saboda kasancewar ta killatacciya ce ita ga mijinta wan da ya sake ta, domin tana ɗauke da hukunci matarsa, saboda faɗinsa maɗaukakin sarki:

وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَٰلِكَ إِنْ أَرَادُوا إِصْلَاحًا ۚ (البقرة: ٢٢٨)

Ma’ana: (Kuma mazajensu su suka fi cancantar dawo da su a cikin iddar, in har sun nufi yin sulhu) [Baƙarah: 228].

Na biyu: idan kuma ya zama an yi mata sakin da ba kome a cikinsa ne: To a nan halinta ba zai fita daga lamura guda biyu ba:

1:Ta zamto tana da ciki.

2:Ko ta zamto ba ta da ciki.

Na daya: In ta zama tana da ciki, to a nan hukunce-hukunce da suke tafe suna rataya a kan sakin ta:

1:Wajabcin bada wajen zama a gare ta daga mijinta, wannan kuma saboda faɗinsa madaukakin sarki:

يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحْصُوا الْعِدَّةَ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ رَبَّكُمْ ۖ لَا تُخْرِجُوهُنَّ مِنْ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخْرُجْنَ إِلَّا أَنْ يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ ۚ. (الطلاق 1:65)

Ma’ana: (Ya kai wannan annabi idan zaku sake mata to ku sake su a yanayin da za su fara iddarsu, kuma ku ƙididdige iddah, ku ji tsoron Allah Ubangijinku; kada ku fitar da su daga dakunansu, kada kuma suma su fita, sai dai in sun zo da wata alfasha mabayyaniya) [Ɗalaƙ: 1].

2: Ciyarwa: Wannan kuma saboda faɗinsa maɗaukakin sarki:

 وَإِنْ كُنَّ أُولَاتِ حَمْلٍ فَأَنْفِقُوا عَلَيْهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ الطلاق: ٦

Ma’ana: (Kuma idan suka kasance ma’abota ciki to sai ku riƙa ciyar da su, har su haife cikinsu) [Ɗalaƙ: 6].

3: Lazimtar ɗakin ta da take takaba, da kuma rashin fita daga cikinsa, sai dai in akwai wata buƙata; Allah ta’alah yana cewa:

لَا تُخْرِجُوهُنَّ مِنْ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخْرُجْنَ إِلَّا أَنْ يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ ۚ. (الطلاق 1:65)

Ma’ana: (Kada ku fitar dasu daga ɗakunansu, kada suma su fita sai dai in sun zo da alfasha bayyananniya) [Ɗalaƙ: 1].

Kuma zata iya fita daga cikin gidan da ake yin iddar idan da dalili da Shari’a ta yarda da shi saboda dalilai masu zuwa.

Amma dalilin halaccin fitanta kuma daga ɗakinta, a lokacin buƙata shine: Hadisin Jabir (dr) yace:

عن جابر بن عبد الله قال: "طُلِّقَتْ خَالَتِي، فَأَرَادَتْ أَنْ تَجُدَّ نَخْلَهَا ، فَزَجَرَهَا رَجُلٌ أَنْ تَخْرُجَ ، فَـأَتَتِ النَّبِيَّ r، فَقَالَ: بَلَى فَجُدِّي نَخْلَكِ، فَإِنَّكِ عَسَى أَنْ تَصَدَّقِي، أَوْ تَفْعَلِي مَعْرُوفًا" {رواه مسلم 1483

Ma’ana: (Lallai an saki "ummata" (wato yar’uwar mahaifiyar sa)Sai ta so ta fita don yanke ‘ya’yan dabinonta, sai wani mutum ya tsawatar mata kan fita, sai ta zo wajen annabi {s.a.w} sai yace: Babu laifi, ta fita ta tsinke ‘ya’yan dabinonta; saboda ta yiwu kiyi sadaka, ko ki aikata wani abu mai kyau da sashi). {Muslim ne ya rawaitu shi 1483}

Na biyu: Idan kuma bata da ciki, to a nan shima duk abinda ya ke tabbata ga mai ciki yana tabbata a gare ta na hukunci-hunce, sai dai ciyarwa, da abinda ke biye masa na tufatarwa, wadannan kam basa tabbata a gare ta; saboda hadisin Faɗinsa bnt Ƙais - رضي الله عنها- a lokacin da mijinta ya sake ta sauran sakin nan guda ɗaya da ya rage mata, sai Annabi (r) yace:

"لا نَفَقَةَ لَكِ إِلا أَنْ تَكُونِي حَامِلا" رواه مسلم (1480)

Ma’ana: (Ba ki da haƙƙin ciyarwa akansa, sai dai in kina da ciki).

Allah she ne mafi sani

AMSAWA

(ABU ABDULLAH)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments