TAMBAYA (162)❓
Slm Allah ya karawa Malan imani da lapia Allah yakareka dakai da iyalan ka ya karamaka ilimi mai albarka Malan tambayana shine mijina yana bari yan uwansa maza suna zuwa gidanmu sukanzo suyi wata 1 2 harfi Malan kuma gidan ba babba bane hasalima ga dakina ga wanda suke kwana aciki kuma ina shayarwa Allah yasani idan sukazo da farko ina kare kanna idan zanshayar da babyna amma idan suka kwana biyu nakansaki jikina sabida zafi wata sa'i kuma Allah yasani suna takurani yanzu haka kusan shekara biyar kenan suna haka Kumafa baligaine maza idan nacemasa bakyau zuwansu saiyace bazai iya hanasuba dan Allah Malan ina neman karin bayani da zan tinkari mijina dashi yazanyi
AMSA❗
Ki same shi ki ce masa My sweetheart me zaka fada
gameda wannan ayar da Allaah ya saukar ?
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتَ النَّبِيِّ
إِلَّا أَن يُؤْذَنَ لَكُمْ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيْرَ نَاظِرِينَ إِنَاهُ وَلَٰكِنْ إِذَا
دُعِيتُمْ فَادْخُلُوا فَإِذَا طَعِمْتُمْ فَانتَشِرُوا وَلَا مُسْتَأْنِسِينَ لِحَدِيثٍ
ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ يُؤْذِي النَّبِيَّ فَيَسْتَحْيِي مِنكُمْ ۖ وَاللَّهُ لَا
يَسْتَحْيِي مِنَ الْحَقِّ ۚ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِن
وَرَاءِ حِجَابٍ ۚ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ ۚ وَمَا كَانَ
لَكُمْ أَن تُؤْذُوا رَسُولَ اللَّهِ وَلَا أَن تَنكِحُوا أَزْوَاجَهُ مِن بَعْدِهِ
أَبَدًا ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ عِندَ اللَّهِ عَظِيمًا )
الأحزاب (53)
Al-Ahzaab
Yã kũ waɗanda suka yi
ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga
wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to,
ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu
hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin
kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku
tambaye su waɗansu kãyã, to, ku
tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da
zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya
halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance
babban abu a wurin Allah.
Asbabin nuzul (dalilin saukar ayar) yana da alaqa
da yanda wasu Sahabbai suke shiga gidan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ba
tareda izininsa ba
Ki bincika Littattafan tafisiri irinsu: Ibn
Khathir (dalibin Ibn Taimiyya), Tafsir na Ibn Jarir at-Tabari da Tafsir Imamul
Qurtubi da sauran malaman Salaf
Malamai sunyi Ijma'i, ba kyau shiga gida saida
izinin masu gida. Wannan ayar itace hujja a kansa. Ki nuna masa kiji me zai ce
Rashin koyi da SUNNONIN fiyayyen halitta ne yasa
muketa tafka kura kurai a lamuranmu
Karin bayani Kuma zai zo filla filla a cikin
karatun da muka Fara last 2 weeks na littafin SUNNONI 1,000+ da sauransu
Mai buqatar shiga USMANNOOR ONLINE ACADEMY, sai
yayi magana ta private don kada karatun da muka fara yayi maka nisa
Wallahu taala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha
illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa:
✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.