Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Kebabbun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Kwararru Ta Yariman Bakura

Citation: Umar, M.A. & Bashir, A. (2024). Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(2), 167-175. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.020.

Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura

Muhammad Arabi UMAR

Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

07062052814

arabiumar@fugusau.edu.ng

Abdullahi Bashir

Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

abdullahi.bashir@fugusau.edu.ng

08036481158

Tsakure

Karin harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar sadarwa kamar yadda fassara ke da matuƙar muhimmnci a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a karkara da ƙauyuka.Wani binciken da aka gudanar ya nuna kashi 77% na ma’aikata da marasa lafiya da ke zuwa Asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura sun fi son amfani da harshen Hausa wajen sadarwa tsakanin marar lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a matakai mabambanta. Har wa yau, daga cikin kashi 77% ɗin kashi 44% sun fi amfani da karin harshen Zamfarci (Bashir & Umar sh. 38, 2024). Wannan dalilin ne ya sa aka yi ƙoƙarin fito da tasirin karin harshen Zamfarci wajen fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da ke Gusau. An yi amfani da Ra’in Fassara ta La’akari da Karin Harshe, wanda Giles & Johnson (1979) ya yi amfani da shi a aikinsa inda ya nuna yadda ake samun bambancin fassara ta la’akari da karin harshe da kuma waɗanda ake yi wa fassara. Binciken ya gano cewa ana samun bambanci ta fannin fassarar wasu keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya da suka shafi likitancin mata da na ƙananan yara tsakanin daidaitacciyar Hausa da kuma karin harshen Zamfarci ta fuskar tsarin sauti da gundarin kalmomi. Bayan da aka zaƙulo wasu kalmomin kiwon lafiya, aka fassara su tare da bayyana yadda ake faɗin su a Zamfarci, an ba wa ƙwararrun likitoci Zamfarawa domin tantancewa da ba da shawara saboda samun ingantacciyar fassara cikin karin harshen Zamfarci. Sakamakon ya kawo jadawali bakwai na wasu keɓaɓbun kalmomin da suka shafi likitancin mata da ƙananan yara. Ana sa ran a ci gaba da zaƙulo wasu keɓaɓbun kalmomi na wasu sassan kiwon lafiya domin taskace su da samar da wani ƙaramin kundi ko ƙamus na keɓaɓbun kalmomin kiwon lafiya cikin daidaitacciyar Hausa da karin harshen Zamfarci domin ƙara inganta sadarwa musamman a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da sauran asisibitocin da ke cikin ƙasar da ake amfani da karin harshen Zamfarci.

Fitilun Kalmomi: Kalmomin kiwon lafiya, Karin harshen Zamfarci, Cututtukan ƙananan Yara, Asibiti

Gabatarwa

Fassara tana taka muhimmiyar rawa wajen samun ingantacciyar sadarwa tsakanin marasa lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a matakai daban-daban. Domin ita fassara ta ƙunshi bayyana maana mafi kusa ko mafi dacewa daga harshen asali zuwa harshen karɓa ta fuskar ma’ana da salo (Nida, 1974). A taƙaice, fassara ita ce mayar da wani abu da aka faɗa ko aka rubuta daga harshen karɓa zuwa harshen bayarwa ba tare da sauya ma’anarsa ba. Fannin kiwon lafiya, fannin ne mai matuƙar muhimmanci wanda yake buƙatar ƙwarewa a kowane fanni, wanda ya haɗa da fassara. Ƙasashen duniya da suka ci gaba a fasahar sadarwa akan sami ƙwararrun maaikatan fassarar kiwon lafiya na dindindin ko na wucin gadi a manyan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, domin samun ingantacciyar sadarwa tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya. Saboda haka rashin fahimtar Ingilishi, bai zai zama wata barazana ga marar lafiya da ya je jinya ƙasar Turai ba domin akan tanadi ƙwararrun masu tafinta ko kuma aikin fassara. Bincike ya nuna kashi 77% na ma’aikata da marasa lafiya da ke zuwa Asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura sun fi amfani da harshen Hausa wajen sadarwa tsakanin marar lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a matakai mabambanta. Har wa yau, daga cikin kashi 77% ɗin kashi 44% sun fi amfani da karin harshen Zamfarci (Bashir & Umar, sh. 38, 2024). Bugu da ƙari, binciken su Bashir da Umar 2024 ya gano cewa kashi 5% ne kawai na ma’aikatan kiwon lafiya a YBSH suke amfani da kebaɓɓun kalmomin kiwon lafiya wurin sadarwa tsakaninsu da marasa lafiya. Wannan ne ya nuna akwai buƙatar a gudanar da wani keɓaɓɓen nazari a kan kalmomin kiwon lafiya a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura tare da fito da tasirin karin harshen Zamfarci. Sakamakon ya samar da fassarar wasu keɓaɓɓun kiwon lafiya da suka shafi sassa daban-daban da kuma yadda ake samun bambanci tsakanin daidaitacciyar Hausa da kuma karin harshen Zamfarci ta fuskar tsarin sauti da gundarin kalmomi. Wannan zai taimaka wa likitoci da nas-nas da ungozuma da sauran ma’aikatan kiwon lafiya domin samun ingantacciyar sadarwa tsakanin marar lafiya da likita ko ma’aikacin kiwon lafiya. An tsara wannan maƙalar zuwa sassa kamar haka: Bitar ayyukan da suka gabata, taƙaitaccen tarihin asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura, dabarun bincike, sakamakon bincike, kammalawa.

Bitar Ayyukan Da Suka Gabata

Azare (2002) a kundinsa mai taken “Fassara da Bayanan Wasu Fannoni na Aikin Likita cikin Hausa” Aikin ya tattaunawa muhimmancin fassara fannonin kimiya da fasaha cikin harshen Hausa saboda a bunƙasa harshen ta yadda zai tafi da zamani da sauye-sauyen zamani. Binciken ya kawo ra’ayoyin masana dangane da aikin fassara da kuma matsalolinta da shawarwari ga mai aikin fassara. Babbar manufar wannan aikin ta fito ne, inda mawallafin ya fassara kalmomi da suka shafi halittar mata da kuma yanayin bugun zuciya. Aikin ya ƙara zuɓo wasu kalmomin da suka danganci aikin likitanci tare da fassara su da kuma bayanansu.

Manazarta da dama sun gudanar da bincike da ayyuka a ɓangaren nazarin karin harshen Hausa ta fuskoki daban-daban, kamar: Bargery (1934), Ahmed da Bello (1970), Dogo (1977), Malka (1978), Muhammad (1978), Abubakar (1983), Sani (2003), Sani & Adamu (2023). Bugu da ƙari akwai waɗanda suka yi ayyuka a Zamfarci, Sakkwatanci da Hausar Yamma kamar Abbas (2000 da 2019) da Adamu (2020) da Maru (2015) da Umar (2024) sun bayyana yadda ake samun bambanci ta fuskar tsarin sauti da tasarifi da ginin jumla da gundarin kalmomi. Ayyukan za su taimaka wajen tsamo keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya na Zamfarci musamman ta fuskar tsarin sauti da gundarin kalmomi.

Wannan aikin yana da alaƙa da nawa aikin saboda a kan fassara kalmomi likitanci ne aka yi shi kuma an ɗora shi a kan daidaitacciyar Hausa, sai dai kuma ya bambanta wannan aikin domin an gudanar da binciken ne a kan fassarar wasu kalmomin kiwon lafiya ne a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakaura tare da kawo yadda suke a karin harshen Zamfarci.

Taƙaitaccen Tarihin Asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura, Gusau (Yariman Bakura Specialist Hospital, Gusau)

An fara gudanar da ayyukan kiwon lafiya a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da ke Gusau, jihar Zamfara ranar 18 ga watan Maris, 2013. An fara da manyan sassan kiwon lafiya na kamar: sashen tiyata da kula da majinyata da sashen cututtun ƙananan yara da ɓangaren gani ko sashen likitancin cututtukan mata na haihuwa da sashen ba da magani da sashen bincike da gwaje-gwaje da sashen kula da haƙora da sashen gwaji hoto da kuma sashen adana bayanan marasa lafiya.

An tanadi ƙwararrun likitoci a ɓangarori daban-daban da kuma nas-nas da unguzomomi da masu kula da majinyata da masu gudanar da asibitin a matakai daban-daban. Har wa yau, an tanadi kayayyaki na zamani a sashen tiyata da sashen kula da haɗurra da sashen ƙananan yara da sahen mata masu juna biyu da sashen likitancin cututtukan mata na haihuwa. Haka kuma, an tanadi wurin ba da magani da kuma sashen bincike da gwaje-gwaje. Akwai ma’aikata masu tsaftace ɗakunan jinya da tsaftace muhalli ciki da waje domin samar da ayyukan kiwon lafiya mai inganci. A watan Fabarairu na 2014 aka fara gudanar da sashen wankin ƙoda wanda shi ne na farko a tarihin jihar Zamfara.

Wannan asibitin yana samar da ayyukan kiwon lafiya ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara da kewayenta kuma ya sauƙaƙa zuwa manyan asibitoci da ke jihohin da ke maƙwabtaka da Zamfara.

Kasancewar, mafi yawan marasa lafiya da ke mu’amala da wannan asibitin Hausawa ne ko kuma masu jin harshen Hausa. Hakan ya sa, masu gudanarwa suka fassara sassa daban-daban da ke cikin asibitin domin ya zama jagora ga marasa lafiya kamar haka:

Hoto 1: Hutunan Fassara Sassa Daban-daban na YBSH










Wannan ya nuna irin ƙoƙarin da hukumar gudanarwa ta yi wajen fassara wasu sassa daban-daban domin sauƙaƙa wa majiyanta da ba su jin harshen Ingilishi. Duk da yake akwai wasu sassa da ba a fassara ba kamar:






Waɗannan wasu sassa ne daga cikin sassan da ba a fassara ba.

Dabarun Gudanar da Bincike

Kasancewar wannan maƙala ce ta biyu daga jerin maƙalu uku da aka ƙuduri rubutawa a kan “Tasirin Aikin Fassara a Fannin Kiwon Lafiya: Keɓaɓɓen Nazari A Asibitin Ƙwarraru ta Yariman Bakura, Gusau’’. A maƙala ta farko, an gudanar da bincike ta hanyar raba tambayoyin bincike ga maaikatan kiwon lafiya da kuma marasa lafiya da masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya. An gano cewa kashi 77% na ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya sun fi amfani da harshen Hausa. Sannan kuma binciken ya gano giɓi wajen amfani da keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya. An nemi shawarar masana da ƙwararrun likitoci a kan jerin kalmomin da aka fi yawan ta’ammuli da su a sassa daban-daban. An zaƙulo keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya daga manyan ƙamusun keɓaɓɓun kalmomi da aka rubuta da Ingilishi da suka shafi sashen likitancin cututtukan mata da sahen kula da ƙananan yara. An yi ƙoƙarin fassara waɗannan kalmomi ta hanyar tuntuɓar ƙwararru da masana kiwon lafiya da kuma ƙwararru a fannin aikin fassara. Haka kuma an dubi ayyukan masana kamar Azare (2002). An yi amfani da kafafen sadarwa na intanet kamar Whatsapp da Facebook domin aika wa da tambayoyi don jin ra’ayin masana a kan wata fassara. Bugu da ƙari, an dubi fassarar da aka gudanar a wasu ayyuka da suka shafi kiwon lafiya. Kuma an dubi ƙamusu na Ingilishi zuwa Hausa domin samun haske da daidaita fassara. Har wa yau, an tuntuɓi likitoci da nas-nas da ke amfani da Zamfarci domin samun ingantacciyar fassara. Bayan an kammala tattara fassarar, an miƙa ta ga wasu ƙwararrun likitoci da masana harshen Hausa da al’adu domin tantance ingancin fassarar. An yi amfani da Ra’in Sadarwa a Fannin Kiwon Lafiya, wannan ra’in an ɗora shi a kan yadda ake ƙirƙira, watsawa, karɓa, da fahimtar saƙonnin da suka shafi kiwon lafiya. Yana mayar da hankali kan sadarwa tsakanin maaikatan kiwon lafiya da majinyata ko marasa lafiya . Wannan ra’i ya taimaka wajen samun nasarar fassara wasu keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya daga ingilishi zuwa Hausa.

Sashen Kula da Ƙananan Yara (Paediatric)

Sashen kula da ƙananan yara wani reshe ne daga rassan likitanci wanda ke da alhakin kula da lafiyar ƙananan yara. Akwai ƙwararrun likitoci waɗanda suka samu horo a fannin kula da ƙananan yara da jarirai. Waɗannan likitocin su ke tantance cututtuka da suka shafi ƙananan yara ta hanyar gwaje-gwaje, sannan su ba da magani da shawarwari. Kasancewar yanayin jiki da halayyar yara sun bambanta da na manyan mutane, don haka ne aka ware wannan sashe na kula da cututtuka da matsalolin ƙananan yara. Likitocin ƙananan yara kan yi ƙoƙarin gano cututtukan da ke addabar yara, da kuma ba da magani da yin allurar riga-kafi da ba da shawarwarin kiwon lafiya. Misali, idan yaro yana fama da zazzaɓi, nan take likitan yara zai yi masa tambayoyi domin gano matsalar. Don haka, akwai buƙatar samun ingantacciyar sadarwa tsakanin ƙananan yara da likitocin ƙananan yara domin Bahaushe yana cewa mai renon jinjiri shina sumbanta tasa. Don haka, fassara kalmomin kiwon lafiya da suka shafi fannin likitanci ƙanan yara tamkar ido ne ga makauniya musamman ga asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da ke taammuli da ƙananan yara daga karkara. Wannan zai sauƙaƙa tare da samun ingantacciyar sadarwa tsakanin likita da marasa lafiya.

Cututtuka Masu Saurin Yaɗuwa (Communicable Disease)

Abin da ake nufi da cututtuka masu saurin yaɗuwa, su ne cututtukan da ƙwayoyin cuta kan samar. An halicci biliyoyin ƙwayoyin cututtuka masu iya kawo cututtuka da ɗan’adam ke iya kamuwa da su. Ana iya kamuwa da su ta hanyar shaƙar iska ko ruwa ko abinci ko ta hanyar taɓa wanda ya kamu da mai ciwo ko hanyar cizon wata dabba ko ƙwaro kamar zazzaɓin cizon sauro. Wadannan cututtuka suna yaɗuwa idan wani ya ɗauka daga wani, misali idan wani ya yi tari ya watsa ƙwayoyin cututtukan a iska, waɗansu da dama na iya kamuwa da cutar ta hanayar shaƙar wannan iska. An zaɓo wasu keɓaɓɓun kalmomi da suka shafi wannan aka fassara su kamar yadda yake a jadawalin da ke ƙasa.

Jadawali na 1: Cututtukan Masu Saurin Yaɗuwa Da Suka Shafi Ƙananan Yara

Lamba

Ingilshi

Hausa

Zamfarci

1

Malaria

Zazzaɓin cizon sauro

Zazzaɓin cizon sauro/janti

2

Tuberculosis

Tarin fuka/tibi

Twarin huka

3

HIV/AIDS

Cutar SIDA

Cuta mai karya garkuwa

4

Measles

Ƙyanda/ Baƙon dauro

Gaida/ ciwon dussa/na kwangwalo

5

Diarrhea

Gudawa

Zawo/amai da zawo

6

Pneumonia

Namoninya/rangaza

Ciwon haƙarƙari/sanyin haƙarƙari

7

Meningitis

Sanƙarau

Ɗan sanƙarau

8

Typhoid fever

Zazzaɓi

Zazzaɓin tayifod/shawara

9

Fever

Zazzaɓi

Masassara

10

Yellow fever

Zazzabin ciwon sauro

Rawaya

11

Ebola Fever

Zazzaɓin Ibola

Masassarar Ibola

12

Lassa fever

Zazzaɓin lasa

Masassarar lasa

13

Echovirus

Ƙuraje

Ƙuraje

 A waɗannan misalai an samu tasirin Zamfarci ta fuskar furuci da gundarin kalmomi, misali a fassarar “Tuberculosis” a DH, ‘Tarin fuka’ a Zamfarci kuma’ ‘twarin huka’ (/t/®/tw/) (/f/®/h/).  sai kuma A ɓangaren gundarin kalmomi, akwai tasiri Zamfarci, kamar inda a Zamfarci, ake da “Gaida, ciwon dussa, ciwon na kwangwalo’’.

Cututtuka Marasa Saurin Yaɗuwa

Cututtuka marasa saurin yaɗuwa, su ne cututtukan da sukan sami ɗan’adam haka kawai a sakamakon yanayin ci gaban zamani da halayya da zamantakewa da bambancin muhalli ko ƙwayoyin halittu da aka gada a wasu lokuta. Ga jerin wasu keɓaɓbun kalmomi da aka fassara da suka shafi fannin likitancin ƙananan yara.

Jadawali na 2: Cututtuka Masu SaurinYaɗuwa da Suka Shafi Ƙananan Yara

Lamba

Ingilishi

DD Hausa

Zamfarci

1

Diabetes

Ciwon Sukari

Ciwon Shuga

2

Heart Disease

Ciwon Zuciya

Ciwon Zucciya

3

Hypertention

Ciwon Hauhawar Jini

Ciwon Hawan Jinni/Borin Jini

4

Polio

Shan Inna

Shan Inna/Riga-Kahi

5

Asthma

Ciwon Asma

Ciwon Huka

6

Cancer

Ciwon Daji/Sankara

Ciwon Daji

7

Obesity

Ciwon Ƙiba

Ciwon Ƙiba

8

Chronic Kidney Disease

Ciwon Ƙoda Mai Tsanani

Ciwon Ƙoda Mai Tsanani

9

Mental Health Disorders

Rashin Lafiyar Taɓin Hankali

Ciwon Hauka

10

Sickle Cell Disease

Cutar Sikila

Cutar Sikila

11

Epilepsy

Farfaɗiya

Hwarhwaɗiya

12

Eczema

Ƙyasfi

Ƙyasfi

13

Stroke

Bugun Zuciya

Mutuwar Sashe

14

Wooping Cough

Tarin Shiƙa

Lala

15

Jaundice

Shawara

Shawara

A nan ma akwai tasirin karin Zamfarci inda ’’farfaɗiya” ta koma “hwarhwaɗiya”. (/f/®/hw/)

Jadawali na 3: Kalmomin Da Suka Shafi Alamomin Cututtukan Ƙananan Yara

Lamba

Ingilishi

DD Hausa

Zamfarci

1

Fever

Zazzaɓi

Masassara

2

Cough

Tari

Twari

3

Sneezing

Atishawa

Attishawa

4

Sore Throat

Ciwon Maƙoshi/ Bushewar Maƙogwaro

Ciwon Maƙoshi

5

Runny Nose

Mura, Zubar Da Majina

Mura/ Zubar Da Majina

6

Vomiting

Amai

Maiso, Mazallaƙo, AmaiHaraswa

7

Diarrhea

Zawo

Zawo/Amai da Zawo

8

Rash

Ƙuraje

Ƙurarraji/Ƙurajen Zuhwa

9

Fatigue

Gajiya

Kasala

10

Lethargy

Mutuwar Jiki

Macewar Jiki

11

Drowsiness

Gyangyadi

Angaje/Juwa/Jiri

12

Irritability

Rashin Nutsuwa

Rashin Sukuni

13

Poor Appetite

Rashin Ɗanɗano

Rashin Ɗanɗwano

14

Earache

Ciwon Kunne

Ciwon Kunne

15

Weight Loss

Ramewa

Ramewa

16

 Headache

Ciwon Kai

Ciwon Kai

17

Abdominal Pain

Ciwon Ciki

Ciwon Ciki

18

Nasal Congestion

Toshewar Hanci

Toshewar Hanci

19

Constipation

Ƙullewar Ciki

Bushewar Ciki

20

Difficulty Breathing

Wahalar Yin Numfashi

Wahalar Yin Sheɗa

21

Nightmares

Mafarkin Abin Tsoro

Mafarkin Dare

22

Night Sweats

Zufan Dare

Zuhwan Dare

23

Joint Pain

Ciwon Gaɓoɓi

Ciwon Gaɓɓai

24

Muscle Pain

Ciwon Gaɓoɓi

Ciwon Gaɓɓai

25

Blurred Vision

Gani Gara-Gara

Gani Garaye-Garaye

26

Frequent Urination

Yawan Fitsari

Hitsari A kai-A kai

 

Jadawali na 4: Wasu Kalmomin Da Suka Shafi Ƙarancin Abinci Da Sinadari

Lamba

Ingilishi

Hausa

Zamfarci

1

Malnutrition

Rashin Isasshen Abinci Mai Gina Jiki

Tamowa

2

Stunting

 Tsumburewa

Tsimbirewa

3

Micronutrient Deficiency

Ƙarancin Sinadarin Gina Jiki

Ƙarancin Sinadarin Gina Jiki

4

Kwashiorkor

Kwashako

Tarƙoshi/Ƙaton Kai/Ta-Ƙauye

5

Marasmus

Kumburin Ciki

Kumburin Ciki

6

Dehydration

Ƙarancin Ruwan Jiki

Ƙarancin Ruwan Jiki

7

Developmental Delay

Tawayar Girma

Tawayar Girma

8

Failure To Thrive

Rashin Saurin Girma

Rashin Saurin Girma

9

Growth Monitoring

Bibiyar Girman Yaro

Bibiyar Girman Yaro

10

Infant Mortality Rate

Yawaitar Mutuwar Jarirai

Yawaitar Mace-Macen Jarirai

11

Immunization

Rigakafi

Riga-kahi

12

Low Birth Weight

Haihuwar Jarirai Marasa Nauyi

Haihuwar Jarirai Marasa Nauyi

13

Neonatal Period

Kwana 28 Bayan Haihuwar Jariri

Kwana 28 Bayan Haihuwar Jinjiri

14

Neonatal Jaundice

Shawarar Jarirai

Shawarar Jarirai

15

Oral Dehydration Theraphy

Ruwan Gishiri Da Sukari

Ruwan Gishiri Da Shuga

16

Stunted Growth

Cuta Mai Tauye Tsawo

Cuta Mai Tauye Tsawo

17

Zinc Deficiency

Ƙarancin Sinadarin Zink

Ƙarancin Sinadarin Zink

18

Vitamin A Deficiency

Ƙaranci Sinadarin Bitamin A

Ƙaranci Sinadari Bitamin A

19

Breastfeeding

Shayarawa

Shayarwa

20

Food Insecurity

Ƙarancin Abinci

Ƙarancin Abinci

21

Food Safety

Wadatar Abinci

Wadatar Abinci

 

Sashen Likitancin Mata/Gani (Gynaecology)

Likitancin Mata, wani ɓangare ne na sassan kiwon lafiya da ake samu a manyan asibitoci, da asibitin ƙwararru. Likita ne da yake da ƙwarewa a ɓangaren lafiyar mata wanda ya haɗa da bangarorin haihuwa da ba da kariya a ɓangaren matantaka ko kuma ba da magani da yin tiyata da ta shafi ɓangaren mahaifa. Ita wannan kalma, wato Gynaecology ta keɓanta ne da irin ciwuka da matsaloli da kuma magani na mata. Ma’ana, duk wani ciwo ko wata matsala ko magani wanda yake ya keɓanta ne kurum ga mata, to ya faɗo cikin wannan ɓangaren, musamman abubuwa da suka shafi matanci, da haihuwa da sauransu. Saboda haka, ganin irin abubuwa da ke ƙunshe cikin wannan kalma mun yi ƙoƙarin fassara ta da ‘’Ilimin Ciwuka da Lafiyar Mata Azare (sh. 50, 2022)

Jadawali na 5: Keɓaɓɓun Kalmomin Likitancin Cututtukan Mata

Lamba

Ingilishi

Hausa

Zamfarci

1.       

Amenorrhea

Jinkirin Haila

Ɗaukewar Alada

2.       

Dysmenorrhea

Ciwon mara na Al’ada

Ciwon mara na Al’ada

3.       

Ovulation

Ƙyanƙyasar Ƙwai

Ƙyanƙyasar Ƙwan Halitta

4.       

Dysmenorrhea

Zazzafar Haila

Ciwon Mara Na Al’ada

5.       

Endometriosis

Cutar Ƙuryar Mahaifa

Cutar Ƙuryar Mahaihwa

6.       

Pelvic Inflammatory Disease (PID):

Ciwon Kogon Mahaifa

Ciwon Kogon Mahaihwa/Sanyin Mata

7.       

Cervical Dysplasia

Alamun Kansar Mahaifa

Alamun Kansar Mahaihwa

8.       

Ovarian Cysts

Kumburin Ƙwanson Ƙwai

Kumburin Ƙwanson Ƙwan Halitta

9.       

Cervical Cancer

Kansar Bakin Mahaifa

Dajin/Kansar Bakin Mahaihwa

10.   

Ovarian Cancer

Kansar Ƙwanson Ƙwai

Dajin Ƙwanson Ƙwan Halitta

11.   

Vaginal Infections

Cututtukan Sanyin Mata

Cututtukan Sanyin Mata

12.   

Urinary Incontinence

Ciwon Mafitsara

Ciwon yoyon hitsari

13.   

Evacution

Wankin Mahaifa

Wankin Mara

14.   

Amniosynthesis

Awon Lafiyar Tayi

Gwajin Lahiyar Tayi

15.   

Cervical Semear

Gwajin Bakin Mahaifa

Gwajin Bakin Mahaihwa

16.   

Contraceptive Pills

Ƙwayoyin Tazarar Iyali

Ƙwayoyin Tsarin Iyali

17.   

Cordocentesis

Gwajin Mikin Ciki

Gwajin Gymbon Ciki/Gwajin Cibiya

18.   

Dilatation & Curratage

Wankin Ciki

Wankin Ciki

19.   

High Vaginal Swab

Binciken Lafiyar Matanci

Binciken Lahiyar Matantaka

20.   

Gravidity

Adadin Ɗaukar Ciki

Yawan Ɗaukar Ciki

21.   

Hysterectomy

Cire Mahaifa

Cire Mahaihwa

22.   

Intra Uterine Devine

Tsarin Iyali Ta Cikin Mahaifa

Tsarin Iyali Ta Cikin Mahaihwa

23.   

Injectables

Tsarin Iyali Ta Allura

Tsarin Iyali Ta Allura

24.   

Airophic Vaginities

Ƙeƙeshewar Gaba

Ƙeƙeshewar Gaba/Bushewar Farji

25.   

Erosion Of The Cervix

Ƙazuwar Bakin Mahaifa

Ƙazuwar Bakin Mahaihwa

 

Jadawali na 6: Keɓaɓɓun Kalmomin Likitancin Cututtukan Mata

Lamba

Ingilishi

Hausa

Zamfarci

1.       

Abdominal Pregnancy

Sabauɗin Ciki

Ciki Bayan Mahaihwa

2.       

Anistomastia

Ƙarancin Mama

Ƙarancin Nono

3.       

Antepatum Haemorrhage

Ɓallewar Mabiyiya

Ɓallewar Uwa

4.       

Bi-Cornate Uterus

Kaucin Mahaifa

Kaucin Mahaihwa

5.       

Blastomer

Bunƙasar Tayi

Bunƙasar Tayi

6.       

Cryptomenorrhea

Kumamiyar Al’ada

Kumamiyar Al’ada

7.       

Hemoperitoneum,

Tararren Jinin Ciki

Tararren Jinin Ciki

8.       

Hyperemesis Gravidarum

Zazzafan Amai

Lalurar Amai

9.       

Menorrahagia

Yalwar Al’ada

Yalwar Al’ada

10.   

Metrorrhagia

Ballagazar Al’ada

Wasar Al’ada

11.   

Oligomenorrhea

Bahaguwar Al’ada

Ƙarancin Alada

12.   

Placenta Previa

Azarɓaɓin Mabiyiya

Uwa Bayan Mahaihwa

13.   

Polyhydramnious

Tumbatsar Mahaifa

Tumbatsar Mahaihwa

14.   

Post-Partum

Mai Jego

Mai Jego/Biƙi

15.   

Tubal Blockage

Cushewar Hannayen Mahaifa

Cushewar Hannayen Mahaihwa

16.   

Utero-Vaginal Prolage

Zazzagowar Mahaifa

Zazzagowar Mahaihwa

17.   

Poetitis

Ƙwarin Dubura

Ƙwarin Dubura

18.   

Salphingitis

Ciwon Hannan Mahaifa

Ciwon Hannun Mahaihwa

19.   

Vesico-Vaginal-Fistula (V.V.F)

Ciwon Yoyon Fitsari

Ciwon Yoyon Hitsari

20.   

Vaginal Atrophy

Ciwon Tsimburewar Farji

Ciwon Tsumburewar Gaba

21.   

Vulvar Dermatitis

Ƙaiƙayin Mara

Ƙaiƙayin Mara

22.   

Volvo Vaginitis

Ƙaiƙayin Gaba

Ƙaiƙayin Gaba

 

Jadawali na 7: Keɓaɓɓun Kalmomin Likitancin Cututtukan Mata    

Lamba

Ingilishi

Hausa

Zamfarci

1.       

Ingilishi

DD Hausa

Zamfarci

2.       

Abdominal Colic

Murɗewar Ciki

Murɗewar Ciki

3.       

Asherman's Syndrome

Rufewar Mahaifa

Rufewar Mahaihwa

4.       

Batholinitis

Kumburin Jijiyar Maiƙo

Kumburin Jijiyar Maiƙo

5.       

Dysfunctional Uterine Bleeding

Yoyon Jini

Yoyon Jini

6.

Mastitis

Ciwon Mama

Kumburin nono

7.

Abdominal Pain

Ciwon Ciki

Ciwon Ciki

8.

Pelvic Pain

Ciwon Ƙugu

Ciwon Baya

 

Sakamakon Bincike da Shawarwari                                  

a.      Wannan bincike ya gano cewa ana samun tasirin karin harshe wajen fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya.

b.      An gano cewa karin harshen Zamfarci wanda yake ɗaya ne daga cikin rukunin Hausar Yamma yana taka muhimmiyar rawa wajen yadda likitoci da marasa lafiya ke fassara wasu keɓaɓbun kalmomi da suka shafi ɓangare kula da yara da kuma likitancin mata a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura.

c.       Karin harshen Zamfarci yana da tasiri ƙwarai a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura.

d.     Fassara kalmomin kiwon lafiya cikin Zamfarci zai taimaka wa likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya na asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura

e.      Fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya a dukkan sassan kiwon lafiya na da tasiri wajen samun ingantacciyar sadarwa tsakanin marasa lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya.

Kammalawa

Binciken ya nuna cewa kashi 60 sun fi son sadarwa a cikin Daidaitacciyar Hausa da kuma Zamfarci. Fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya cikin Zamfarci zai taimaka wajen bunƙasa karin harshen Zamfarci da kuma inganta fagen fassara da sadarwa. Har wa yau, zai taimaka wa likitoci da ɗalibai Hausawa da masu amfani da Zamfarci da ke aiki a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da sauran cibiyoyin kula da kiwon lafiya. Ana fatan a ci gaba da tattara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya cikin Hausar Yamma da kuma Zamfarci domin samar da wani ƙaramin daftari ko ƙamusu. Ana ba da shawara cewa ya kamata a samu ƙwararru a fanni fassara da suka samu horo a kan fannin kiwon lafiya, su zama masu tafinta ko aikin fassara a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura.

Manazarta    

Abbas N.I. (2000) .The Study of Zamfarci Dialect Unpublished B.A. Dissertation, Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Abbas N.I. (2019). “Nazarin Wasu Nau’o’in Kare-Karen Hausar Yamma da Siffofinsu.” Unpublished Ph.D. Thesis, Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Abubakar, A. (1983). Generative Phonology and Dialect Variation: A Study of Hausa Dialects, Unpublished PhD Thesis, University of London.

Adamu, S. (2020). The Study of Phonological Variations Between Garewanci and Zamfaranci Sub-dialects of Zamfara” Unpublished M.A Dissertation, Department of Linguistics and Foreign Languages, Bayero University, Kano.

Ahmed, U. and Daura B. (1970). An Introduction to Classical Hausa and the Major Dialects. Zaria, Northern Nigeria Publishing Company.

Azare, Y. M. (2004). Fassara da Bayanan Wasu Fannoni na Aikin Likita Cikin Hausa Unpublished M.A. Dissertation, Department of Nigerian Languages. Bayero University, Kano.

Bashir, A., & Umar, M. A. (2024). Hausa in Hospitals: Exploring Healthcare Communications in Yariman Bakura Specialist Hospital Gusau, Zamfara State, Nigeria. Middle East Research Journal of Linguistics and Literature, 4(02), 35–42. https://doi.org/10.36348/merjll.2024.v04i02.003

Bello, A. (2016). Hausa Dialects and Distinctive Feature Analysis. Zaria: Ahmadu Bello University Press, Ltd.

Concise Medical Dictionary. (2023). Oxford University Press

Dogo, A. M. (1977). A Comparative Study of Sakkwatanci and Kananci. Unpublished M.A. Dissertation, Ibadan, University of Ibadan

Giles, H., & Johnson, P. (1979). Speech accommodation theory: A social psychological perspective. In H. Giles & R. N. St. Clair (Eds.), Language and social psychology (pp. 145-205). John Wiley & Sons.

Malka, J. (1978). “Nazarin Bambance-Bambance da ke Tsakanin Daidaitacciyar Hausa (Nijeriya) da Hausa Filinge (Jamhuriyar Nijar) ta Fuskar Tsarin Fannin Furuci”. Harshe 1 Journal of Department Nigerian and African languages Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria. Shafi na 19-51

Maru, A.M. (2015), “Morpho-Lexical Variation in Zamfarci”. Unpublished M.A. Dissertation: Department of Linguistics Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Miller, B. F., & Keane, C. B. (1972). Encyclopedia and Dictionary of Medicine and Nursing. http://books.google.ie/books?id=PSlrAAAAMAAJ&dq=Medical+Dictionaries+and+Encyclopedias&hl=&cd=1&source=gbs_api

Nida, E. A., & Taber, C. R. (1974). The Theory and Practice of Translation. Brill Archive. http://books.google.ie/books?id=odoUAAAAIAAJ&printsec=frontcover&dq=Nida+1974+The+Theory+and+Practice+of+translation&hl=&cd=1&source=gbs_api

Sani, A-U. & Adamu, S. (2023). Daga Hausar Rukuni Zuwa Ɓoyayyiyar Alada: Keɓaɓɓen Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 2(2), 115-123. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.013.

Sani M.A.Z. (2003). Alfiyyar Mu’azu Sani 3 Karorin Harshen Hausa A Waƙe. Kano: Benchmark Publishers

Stedman, T. L. (2005). Stedman’s Medical Dictionary for the Health Professions and Nursing. Lippincott Williams & Wilkins. http://books.google.ie/books?id=XzvU0qd4IQkC&printsec=frontcover&dq=Medical+Dictionary&hl=&cd=3&source=gbs_api

Umar, M. A. (2024). Acoustic Features of Hausa Consonants: A Study of Sokoto Dialect. Unpublished M.A. Dissertation, Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University, Zaria.

Post a Comment

0 Comments