Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Ya Sa Muke Gudun Sunayen Hausa Na Gargajiya? Illar Cancel Culture!

Kwanakin baya na yi rubutu da Ingilish a kan sunayen Hausawa na gargajiya. Mutane da dama sun nema in fassara zuwa Hausa domin ƙaruwar al’umma. To gashi nan!

Kusan shekaru 45 da suka wuce, matar wani amini na ta haifar mu su da ɗa. Aminin nawa ya ce da magabantan sa a sawa yaron suna Maikuɗi. Duka ɓangaorin – na matar sa da na sa – suka tirje  kan cewa ai ‘Maikuɗi’ ba suna ba ne. Shi kuma bai ga wani aibu da sunan ba, tunda sunan gargajiya ne na Hausawa. Kuma shi Bahaushe ne. Ya cije. Suka cije.

Kwanaki uku kafin ranar sunan jaririn dole ya haƙura, ya bada wani sunan. Ya ce a raɗawa yaron Ibrahim. Wannan suna ne mai daraja  wajen Musulmai, Kiristoci da kuma Yahudawa. Hankalin kowa ya kwanta da wannan sunan. Sai da suka farga cewa ashe sunan uban maihaifiyar yaron ne. To kaga kuwa ba wanda ya isa ya kira sunan yaron Ibrahim batso-batso saboda kunya da kara. Ala dole a ka dinga kiran yaron da sunan da uban ya so a ba shi tun asali: Maikuɗi. Yanzu dai Maikuɗi cikakken ɗan kasuwa ne a ƙasashen Gabas to Tsakiya. Allah Ya ba shi nasara sosai, kuma ya ci sunan sa – domin a Hausance Maikuɗi na nufin wanda aka haifa ranar sa’a, ko kuma wanda a ka haifa ranar Talata.

Amma ba a rabu da Bukar ba, wai an haifi Habu. Bayan shekaru kaɗan, matar aminin nawa dai ta haifar masa da ƴa mace. Kamar ka sani, sai ya ce a raɗa mata suna Tabawa, sunan Hausawa. Nan ma a ka ce ba a yarda ba. Tabawa ba suna ba ne. Kamar wancan lokacin, dole amini na ya haƙura, ya ce a sakawa yarinyar suna Hajara. Shi ma suna ne mai daraja. Hasali ma dai, Hajara sunan matar Annabi Ibrahim ne. Sai dai kuma sunan babbar yayar amini na ce, kuma mahaifiyar su ba ta furta sunan, saboda kunya irin ta mutanen da. Dole a ka haƙura aka dinga kiran jaririyar da Tabawa. Sunan asali a cikin al’ummar Hausawa wanda ke nufin uwar sa’a. Ko kuma wacce a ka haifa ranar Laraba (a Kano, a Katsina kuma ranar Talata). Yanzu haka tana koyarwa a babbar makaranta a Kano, kuma ta kusan gama PhD a ɗaya daga cikin jami’o’in Najeriya.  Yara guda biyu. Kowanne ya taki sa’a a rayuwa. Sunayen su suka zama jagora gare su.

Tambayar ita ce, mai ya sa muka tsani sunayen Hausawa na gargajiya? Ko don saboda “Aƙidar Danniya” ce, watau Cancel Culture inda ake ta rurutawa duk wani sunan da ya samo asali daga gargarjiyar Hausawa za a ce ai na Maguzawa ne?

Watau ba za ka raɗawa ɗan ka suna Maikuɗi ba, amma da zarar ka ce sunan sa Yasar sai a ce ka yi daidai, duk da cewa Yasar, sunan Larabawa, na nufi mai arziki. Ko Kamal (daidaito). Kira ɗan ka Damisa, ka shiga uku, in ka canza zuwa Fahad, ka gyara, duk da cewa sunan wani nau’i na damisa (panther) da Larabci. Mai ya sa Fahad ya fi Damisa daraja duk da cewa ma’anar su ɗaya?

Sunaye da yawa da mu ke amfani da su ba du da wata nasaba da Musulunci – kawai zaƙi ne da su; sai mu ɗauka mu ƙaƙabawa kan mu. Yanzu dubi waɗannan sunayen Larabawan, sannan ka kwatanta abin da zai faru in ka yi amfani da sunan fassarar su da Hausa: Fawaz (Nasara – Mainsara?), Farid (kaɗaitacce), Haydar (Zaki), Mumtaz (mai inganci), Usama (Zaki), Zafer (wanda ya yi nasara), da dai sauran su.

Kar ka ce Tabawa, amma ka ce Mahjuba (lullubabbe), ko Samira (surutu). “Dare? Sunan mace? Haba malam, menene haka?”,  “Afuwan, na canza, zan kira ta Laila” (dare, da Larabci).

Abin da nake son in nuna shi ne da yawa daga cikin sunayen da Hausawa Musulmai ke alfari da su ba su da wata dangantaka da Musulunci. Bama ma sanin ma’anar sunayen, kawai saboda zaƙin sunan da kuma Larabcin sa, sai mu ɗauko mu jibga wa ƴaƴan mu. An tirsasawa Hausawa yin amfani da sunayen Larabawa saboda Cancel Culture ta gama shelantawa duk sunan da ba na Larabawa ba ne (ko da ba shi da asali a Qur’ani ko Hadisi), to na ‘Haɓe’ (watau Hausawan asali) ne, kuma in dai na Haɓe ne, to Maguzanci ne. Wannan kuwa an yi ne domin a nunawa Hausawa ba su da tasiri a rayuwa tun daga 1804.

Ganin haka ya sa ni da aminin na, da kuma wani abokin mu muka ce gara mu yi fargar jaji  a kan sunayen Hausawa, duk da cewa mu kan mu daga baya ambaliyar Cancel Culture ta mamaye sunayen da muka bawa ƴaƴan mu. Amma duk da haka mukace bari mu zauna mu yi wani yunƙurin ankare mutane game da Cancel Culture a kan sunayen Hausawa na asali. Mun futo daga sinadiran halitta dabam-dabam (Kanuri, Balarabe, Fulani), amma mun watsar da wannan muna alfahari da cewa mu Hausawa ne, ba wani shashancin ‘Hausa-Fulani’.

Sai da mukayi shekaru fiye da goma muna tattaro sunayen Hausawa na asali waɗanda ba su da wata alaƙa da Maguzanci (rukunin da ƴan Cancel Culture ke saka duk Bahaushen da ba Musulimi ba ne, an manta akwai Hausawa da kuma sauran ƙabilu ma su bin addinin Kirista – su ma Maguzawa ne?). Sai muka haɗa da ƙalilan daga sunayen da suke da nasaba da Musulunci. A ƙarshe muka samu sunaye 1001 da Hausawa ke amfani da su. Daga ciki, 869 zunzuruntun  sunayen asali ne na Hausawa. Sannan sai 132 waɗanda suka samo asali daga zuwan Musulunci, harda waɗanda Hausawa suka narkar da su. Bari na yi bayanin kaɗan daga cikin duk rukunayen biyun.

Rukuni Rayuwa, Cututtuka da Mutuwa. A wannan rukunin, Hausawa na bawa ƴaƴan su sunayen da suka danganci akasin rayuwa. A wannan rukunin za a fahimce yadda Hausawa suka ɗauki rayuwa. Misalai sun haɗa da waɗannan:

Barbushe (wanda ba ya barci). Wannan shi ne sarkin Kano na farko kafin mulkin mallakar Daudawa (Bagauda da ayarin sa). Wataƙila ganin cewa wannan shi ne babban mai jagorancin bauta a tsakanin Kanawan da suka yarda da addinin sa a farkon samuwar alƙarya su ya sa ake danganta ire-iren waɗannan sunayen da wannan nau’in bautar.

Abarshi. An samo wannan da daga lafazin ‘Allah Ya bar shi’. Mace kuma Abarta.. Idan an haifi yaro, a kan rabu da shi, watau a bar shi shi kadai wani tsahon lokaci ta yadda ko iskokai ba za su kula da shi ba. Ana yin haka ne saboda kare shi. Dangogin sunan sun haɗa da Mantau, Ajefa, Barmani, Ajuji, Bawa, da Barau.

Ga kuma Shekarau, wanda aka samo daga Shekara. Wannan yaro ne wanda aka haifa bayan ya wuce lokacin haihuwa, watau kamar ya shekara a ciki kenan. Wani juyin sunan shi ne Ɓoyi (ɓoyayye). Ana kiran jaririya da wannan martabar Shekara. Shawai kuma sunan da a ke bawa yarinyar da ta sha wuya bayan haihuwar ta (ana sawa maza ma sunan). Anini yarinyar da ke ƙananuwan gaɓoɓi ne.

Sai kuma Tanko. Wannan jariri ne wanda ya biyo haihuwar mata uku a jere. Makamantan sunan sun haɗa Gudaji, Tankari, Yuguda/Iguda/Guda. Macen shi kuma ita ce Dela (da kuma Duduwa, Baranka, Kande) macen da ta biyo maza a haihuwa, kamar Tanko da matan da ya biyo.

Dukiya da kuma Bauta: Wannan rukunin sunayen da Hausawa ke gudu saboda dangantasu ta mummunar muzantawa al’umma ta hanyar bautarwa. Bayi na da muhimmanci a masarautun Kano, Zariya, Daura da Katsina. Kuma ana juya su yadda iyaygen gidan su suke buƙata.

An kasa bayi rukuni biyu a Kano: na gida, da kuma na gona. Yardaddun bayi aka fi bari a gidan  Sarki saboda sadaukarwa su ga mai sarautar. Bayin gona kuwa waɗanda ana kamo su ne lokacin rarumar yaƙi, ko kuma ba a yarda da su ba saboda ganin cewa za su iya tsere wa da zarar sun samu dama. Irin waɗannan bayin an fi samun su a gidajen attajirai, ko kuma manyan manoma.

Duk da dai cewa ba a cinikin bayi yanzu (hasali ma kifar da cinikin ne ginshiƙin zuwan Turawan mulkin mallaka a 1903 zuwa Kano) amma har yanzu bauta na nan da ranta a gidajen Sauratar ƙasashen Hausa.

A Kano dai bayin an sake raba su gida biyu – kammmun bayi (rukunin farko wanda kamo su a ka yi a raruma) da kuma cucunawa ƴaƴan bayi, waɗanda su ma bayi ne). Sunayen da ake danganta su da bayi sun haɗa da:

Nasamu. Wannan bawan farko ne da matashi ya mallaka a kan hanyarsa ta zama hamshafin attajiri. Sai Arziki, baiwar farko da mutum ya mallaka. Ga kuma Nagode, baiwar da a ka bawa mutum kyauta. Idan mahaifi na son kyautatawa ɗan sa, sai ya ba shi bawa namiji, wanda ake kira Baba da Rai. Suna Dangana na da tushe biyu. Na farko shi ne yaron da ƴan uwansa suka rasu da jaririntaka (sunan macen shi ne Nadogara). Na biyu shi ne bawan da manomin da ya fara nasara bayan ya sha wahalar noman. Sai Baubawa, bawan da ke daga addini dabam da na mai shi.

Tun zuwan Turawa aka fara zaizaye sunayen da ke da dangantaka da cinikin bayi. Amma duk da haka, akwai sunayen da ke alamta ko sana’a ko matsayin bawa. Misalai sun haɗa da sarautun bayi a gidajen Sarauta, duk da ba a cika yawan amfani da su ba. Kaɗan daga cikin sun haɗa da:

Shamaki (mai kula da bayin sarki da kuma dawan sa). Ɗan Rimi (Babban bawan sarki, kuma yana kula da makaman yaƙin sarki). Kasheka (mai kula da cikin gidan sarki, akasari ‘baba’ ne, watau dai ‘zarmalulu no work’ saboda gudun raɗe-raɗen shaiɗan), Jarmai (shugaban runduna), Kilishi (mai kula da kujerar Sarki). Waɗannan sunayen a gidan Sarauta kawai ake samun su ba jama’ar gari ba sai dai a matsayin laƙabi.

Rukunayen Sunayen Yanayi. Hausawa na bawa ƴaƴan su sunaye da ke da alaƙa da yanayi na shekara, sati, ko zagoyawar yanayin. Misali, Sammako (wanda aka haifa da asuba), Ranau (haihuwar rana), Na-Hantsi (da hantsi), Dare (cikin dare), Shuka (lokacin shukar gona), Nomau (da kuma Ɗankaka, Kakale, Kaka duk lokacin girbi), Marka (kamar damina).

Musulunci bai hana baiwa mutum sunan da ya dace ba. Illa dai ba a son abin da ya yi nuni ga wani abun da Musulunci ya haramta. Zuwan Musulunci sai ya kawo sunayen da aka fi danganta su da Musuluncin kamar sunayen Annabawa, ko Sahabbai. Waɗansu sunayen kuma sai Hausawa suka lanƙwasu zuwa nasu furucin. Misali Guruza (Ahmad), Da’u (Dawud), Gagare (Abubakar), Auwa (Hauwa), Daso (Maryam), Babuga (Umar), Ilu (Isma’il), Jibo (Jibrin), Dijangala, Dije (Khadijah), Unku (Amina), Jibaje (Jibrin), Hansai (Hafsat), Burungu (Amina), Abba (Abun).

Wannan taƙaitaccen bayani ne a kan waɗannan sunayen. Ga cikakken jerin sunayen a rariyar kasa in mutum ya na so ya samu. Sannan kuma akwai cikakkiyar maƙala ta Ingilishi da a ka buga bayanai masu zurfi a kan lamarin. Rariyar ta na ƙasa ita ma.

Suna Linzami: Hausa Names as Ethnographic Identifiers: https://bit.ly/3XHmf1I

1001 Authentic Traditional Hausa Names: https://bit.ly/4e42es2

Daga shafin
Prof. Abdalla Uba Adamu

Post a Comment

0 Comments