Za a iya rubuta manazartar wannan rubutu kamar haka: Sani, A-U. (2024). Dabarun gudanar da bincike a sauƙaƙe. https://www.amsoshi.com/2024/09/taken-binciken-ilimi-maanarsa-da.html
Taken Binciken Ilimi: Ma'anarsa Da Ƙa'idojinsa
Abu-Ubaida SANI
Department of Languages and Cultures,
Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria
Email: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng | abuubaidasani5@gmail.com
Site: www.abu-ubaida.com | www.amsoshi.com
WhatsApp: +2348133529736
Taken Bincike
Ana iya ɗaukar taken bincike a matsayin jagora ko limamin kowane aikin bincike. Dalili kuwa shi ne, ya kasance abin da ake fara gani yayin da aka ɗauki wani aikin bincike. A Hausa akan kira shi da sunaye daban-daban da suka haɗa da:
a. Taken bincike
b. Sunan bincike
c. Kan bincike
Ko ma dai yaya abin yake, taken bincike yana nufin sunan da aka raɗa wa wani aikin bincike wanda yake zuwa a sama a shafin farko kafin sunan marubuci ko marubuta binciken.
Zaɓen Taken Bincike
Akwai muhawarar masana dangane da daidai lokacin da ake zaɓen taken bincike. Akwai waɗanda suke ganin, kamar yadda sai an haihu ake saka sunan abin da aka haifa, to haka bincike yake. Ma'ana dai, dole sai an kammala bincike kafin a duba sunan da ya dace a saka masa ta la'akari da ƙunshiyarsa. Fahimtar wannan rubutu ta bambanta da ta masu wannan iƙirari.
Aikin nan ya fi gamsuwa da cewa, ana sanya taken bincike ne da zarar an ƙuduri yin sa. Duk da haka, ana iya sauya shi ko a yi masa gyara a kowace gaɓa yayin gudanar da bincike. Bayan an kammala bincike kuwa, a nan ne za a yi masa nazarin ƙwaƙƙwafi na ƙarshe domin tabbatar da cewa ya dace da ƙunshiyar binciken da aka gudanar.
Abubuwan Kiyayewa Yayin Zaɓen Taken Bincike
Yayin zaɓen taken bincike, akwai muhimman abubuwa da ya kamata a yi la'akari da su ko a kiyaye su. Sun haɗa da:
1. Dacewa Da Ƙunshiya: Dole ne ƙunshiyar bincike ta dace da taken binciken. Kuskure ne a samu take yana faɗin wani abu, ƙunshiyar binciken kuma tana bayani wani abu na daban.
2. Tsawo: Kada taken bincike ya yi tsawo da yawa. Akwai masana da suka taƙaita kalmomin taken bincike zuwa goma sha takwas (18). Duk da haka, tsarin APA 7th Edition ya kawo cewa, bai kamata a tilasta taƙaita kalmomin da ke cikin taken bincike ba, sai dai ana ba da shawarar a taƙaita ƙwarai idan hakan zai yiwu.
3. Tambaya: Ba a so taken bincike ya kasance tambaya. Misali, take ba ya iya kasancewa cikin sigogin da aka kawo a ƙasa:
a. Mene ne Amfanin Ganyen Kuka a Mahangar Hausawa?
A nan, taken yana iya kasancewa: "Amfanin Ganyen Kuka a Mahangar Hausawa" ko "Ganyen Kuka a Tunanin Hausa" da makamantansu.
b. Ta Yaya Ake Nazarin Waƙa?
A nan, taken yana iya kasancewa: "Nazarin Matakan Nazarin Waƙa" ko "Nazarin Dabarun Nazarin Waƙa" da dai makamantansu.
4. Raddi: Ba a so take ya kasance raddi. Misali:
a. Raddi Ga Wadda Ta Ce Duk Matan Hausawa Suna Da Burin Karuwanci
Yana iya kasancewa: "Bitar 'Karuwanci' a Mahangar Matan Hausawa" ko "Karuwanci a Tunanin Matan Hausawa" da makamantan wannan.
b. Ai Da Ma Mace Mutum Ce
Zai iya kasancewa: "Nazarin Mutuntakar Mace a Bahaushiyar Al'ada" ko "Mace a Mahangar Al'ada da Addini" da makamantan waɗannan.
5. Maimaici: A guji maimaita wata kalmo ko wasu kalmomi ko wani saƙo a cikin taken bincike.
6. Kuskuren Rubutu: Yayin gudanar da kowane rubutu, ana son a riƙe kiyaye ƙa'idojin rubutu. Dangane da taken bincike kuwa, samuwar kuskure a cikinsa babban al'amari ne. Akwai masanan da suke da ra'ayin cewa, duk taken binciken da yake ɗauke da kuskure, to bai kamata a ko nazarce shi ba.
7. Falsafar Zance: Yana da kyau kai tsaye a ga falsafar zance a cikin taken bincike. Hausar mai gunadar da bincike dole ta kai wani matakin nuna ƙwarewa, ba ta kasance sakaka kamar Hausar tasha ko ta yau da kullum ba.
8. Guje Wa Jirkita Zance: Dole ne a kauce wa tukuikuya zance a taken bincike. Kada ƙoƙarin amfani da salo da falsafar zance ya sa a sanyo kalmomi cikin tsarin da za su ruɗar da mai karatu.
9. Taƙaita Kadada: Ba a son taken binciken ilimi ya yi ɗibar karar mahaukaciya a wani al'amari. Ba a son ya ɗauki buɗaɗɗiyar kadada mai faɗi wadda manazarci ba zai iya nazartar ƙunshiyarta yadda ya kamata ba. Misali, kuskure ne take ya kasance kamar haka:
"Nason Koyarwar Addinai a Cikin Waƙoƙi"
Tambayoyin da manazarci ya kamata ya yi wa kansa su ne:
a. Shin zai iya nazartar dukkannin addinai tare da samun bayanan irin nason da koyarwarsu suka yi a cikin waƙoƙi? Kai tsaye ya kamata ya taƙaita wannan ɓangare na take, wato ya nuna wane addini yake nufi. Za ta iya yiwuwa yana nufin koyarwar addinin Musulunci.
b. Shin zai iya karaɗe waƙoƙin dukkannin al'ummun duniya? Idan ba haka ba, ya kamata manazarcin ya taƙaita kadadar zuwa waƙoƙin wata al'umma taƙamaimai. Waƙoƙin za su iya kasancewa na Hausawa.
c. Ko da an taƙaita ga waƙoƙin Hausawa, shin yana nufin nazartar dukkannin nau'ukan waƙoƙi? Da wuya, domin kuwa waƙoƙin Hausa suna da yawa.
Yayin da manazarci ya yi wa kansa ire-iren waɗannan tambayoyi, za ta yiwu ya sanya wa takensa kadada, ya mayar da shi kamar haka:
"Nason Koyarwar Addinin Musulunci a Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Jahadi"
Akwai nau'ukan kadadar bincike daban-daban waɗanda ana iya kallon su tun daga taken bincike. Misali:
i. Kadadar Wuri: "Hausar 'Yan Kabukabu a Gusau"
Lura: A nan an taƙaita binciken a garin Gusau. Da a ce an bar abin a sake, da wuya binciken ya samar da sakamako mai nagarta. Dalili shi ne, sana'ar kabukabu ta karaɗe garuruwa da dama a Nijeriya. Hausar da 'yan kabukabu sauke yi a wani gari tana iya bambanta sosai da na sauran garuruwan.
ii. Kadadar Shekara: "Kambamar Zulaƙe a Waƙoƙin Siyasar Shekarar 2015"
iii. Kadadar Ƙarni: "Tsattsafin Maguzanci a Rubutattun Waƙoƙin Ƙarni na Ashirin Da Ɗaya"
iv. Kadadar Zamani: "Nason Ƙin Jinin Turawa a Rubutattun Waƙoƙin Hausa: Keɓaɓɓen Nazarin Waƙoƙin Zamanin Mulkin Mallaka"
Sauran nau'ukan kadada da ake iya samu sun haɗa da shekaru da jinsi da ƙabila da addini da sauransu.
Madogara
Al-Shaibani, G. K. S. (2016). The language of academic writing [PowerPoint slides]. https://www.slideshare.net/DrGhayth2015/presentations.
APA. (2022). Updates and additions to APA style. American Psychological Association. https://apastyle.apa.org/style-grammar-guidelines/updates.
Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a farfajiyar adabi da al’adun Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(12), 720-727.
Bunza, A.M. (2017). Dabarun bincike (A nazarin harshe da adabi da al’adun Hausawa). Ahmadu Bello University Press Ltd.
Bunza, A.M. (2018, January 17). Mathematical heritage in Hausa number system: (A proposal for teachingmathematics using Nigerian languages). University Seminar Series, University Research Center, Federal University Gusau, ICT Twin Theatre 1, Federal University Gusau. https://www.amsoshi.com/2018/06/mathematical-heritage-in-hausa-number.html.
Charles, S. C. (2016). A Six Step Process to Developing an Educational Research Plan. https://medicine.ecu.edu/clinicalsimulation/wp-content/pv-uploads/sites/246/2019/02/SixStepProcessToDevelopingAn-EducationalResearchPlan.pdf.
Creswell, J. (2015). Educational research: Planning, conducting, and evaluating quantitative and qualitative research (5th ed.). Boston, MA: Pearson Education, Inc.
Gobir, Y. A. & Sani, A-U. (2019). Witchcraft in the Light of Hausa Culture and Religion. In Academic Journal of Current Research. Vol. 6, No. 12; Pp., 23-30. ISSN (2343–403X); p–ISSN 3244–5621. Available at: http://cird.online/AJCR/wp-content/uploads/2020/01/CIRD-AJCR-19-12033-final.pdf.
Johnson, B. & Christensen, L. (2004). Educational research: Quantitative, qualitative, and mixed approaches. (2nd ed.). Pearson Education, Inc.
Kabir, S.M.S. (2016). Writing research report. https://www.researchgate.net/publication/325546150_WRITING_RESEARCH_REPORT.
Kauru, A.I. (2015). A handbook for writing project reports, theses, and journal articles. ISBN: 978-937-850-0.
Livingston, S.A. (2012). How to write an effective research report. https://www.ets.org/Media/Research/pdf/RM-12-05.pdf.
Murdoch University. (2023). APA - Referencing guide. https://libguides.murdoch.edu.au/APA.
Online Library Learning Center (n.d.). Steps in the research process. https://www.usg.edu/galileo/skills/unit01/infoage01_04.phtml.
Purdue University. (n.d.). APA formatting and style guide (7th edition). https://owl.purdue.edu/owl/research_and_citation/apa_style/apa_formatting_and_style_guide/index.html.
Sani, A-U. & Kurawa, H.M. (2023). Kama da wane ba ta wane: Matakan rairaye bincike daga ba bincike ba. The Nasara Journal of Humanities, 11(1&2), 247-258. ISSN: 1118-6887.
Sani, A-U. & Jaja, M. B. (2020). Siddabarun zamani: Daga kimiyya da fasaha zuwa dabarbarun daburta tunanin bami. In Al-Nebras International Journal 4th Edition, 2, 28-41.
Sani, A-U., Buba, U. & Mohammad, I. (2019). Wanda ya tuna bara...: Biɗa da tanadi a tsakanin hausawa matasa a yau. Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences, 1(2), 44-50. www.doi.org/10.36348/gajhss.2019.v01i02.001.
Shehu, A. (2022). Jaki a rayuwar Bahaushe [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
Shehu, M. (2018). Matakan gudanar da binciken ilimi. https://www.amsoshi.com/2017/07/matakan-gudanar-da-bincike-na-ilimi-2_13.html.
Shibly, A. (2016). Referencing and Citation. https://www.researchgate.net/publication/305911163_Referencing_and_Citation.
Sidi, M. (2023). Bature a rubutattun waƙoƙin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
Sonmez, S. (2018). "11 Steps" Process as A Research Method. Universal Journal of Educational Research, 6(11), 2597-2603. https://www.doi.org/10.13189/ujer.2018.06112.
Strongman, L. (2013). Academic writing. Cambridge Scholars Publishing.
University of Michigan. (2017). Introduction to the research process. https://www.press.umich.edu/pdf/9780472036431-Sec1.pdf.
University of Otago. (2017). What is Referencing and why is it important? https://www.otago.ac.nz/hedc/otago615365.pdf.
Yahaya, S. U. (2021). Damben Hausawa a zamanance [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.