TAMBAYA ❓
Assalamualaikum malam Dan Allah addu'ar mutum ya
dinga jin alamun Yana wa wani hassada
AMSA❗
ALHAMDULILLAH
TUNATARWA GA MASU YIN HASSADA
Hassada babban ciwone da ya ke chutar da mai yinsa
sama da Wanda akeyiwa hassadar, domin hassadar mai hassada bata hana faruwar
abin da Allah ya tsara zai faru da bawan sa, don haka wajibi ne a gare mu, mu
zama masu farin ciki akan dukkan abun da Allah ya bawa yan'uwan mu, kuma muma
mu naimi rabanmu daga wajan Allah sai Allah ya rufamana asirin mu ya kuma
fuwace mana ya wadata mu, kuma hakan shine abun da zai sa mu sami kwanciyar
hankali a rayuwar mu.
YA kai mai hassada ka sani kamar kana tuhumar
Allah ne akan mai ya sa yabawa wani kaza kai bai baka ba, alhalin Allah shine
mai rabawa kowa abin da ya dace da shi, kuma ba mai sa shi ya chanza abin da ya
tsara sai dai in shi ya so ya chanza, to don haka kai mai hassada kasani babu abin da zai chanza sai abin da Allah ya
so ya chanza, in ka ci gaba da hassadar kai ne zaka cigaba da zalunta da chutar
da kaka.
WADANNAN ADDU'O'IN SUNA DA TASIRI SOSAI WAJAN
ALLAH YA MAGANCEWA MAI YINSU DUKKAN WASU CHUTUTTUKAN DA KE ZUCIYAR SA IN SHA
ALLAH, MU KARANTA SU DA YAQININ ALLAH ZAI YAYE MANA MATSALAR DA TAKE CIKIN
ZOCIYAR DUKKAN WANDA YA LAZIMCI YINSU SOSAI
اللَّهُمَ طَهِّرْ قَلْبِي
مِن كُلِّ سُوءٍ، اللَّهُمَ طهر قَلْبِي مِن كُلّ مَا يَغْضَبُكَ اللَّهُمَ طَهِّر
قَلْبِي مِنْ كُلِّ غِلِّ وَحِقْدٍّ وَحَسَدٍ وكِبَرٍ وَ نَحو ذَلِكَ،
YA ALLAH KA TSARKAKE MIN ZUCIYATA DAGA DUKKAN ABU
MUMMUNA, YA ALLAH KA TSARKAKE MIN ZUCIYA TA DAGA DUKKAN WANI ABUN DA ZAI
SANYAKA MUFUSHI, YA ALLAH KA TSARKAKE MIN ZUCIYA TA DA GA DUKKAN QETA DA HIQDU
DA HASADA DA GIRMAN KAI DA MAKAMANTAN
SU.
اللَهُمَّ يَا مُقَلِّبُ
القُلُوبَ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلىٓ دِينِكَ، وَيَا مُصَرِّفُ القُلُوبَ صَرِّفْ قَلْبِي
عَلَى طَاعَتِكَ.
YA ALLAH MAI JUJJUYAR DA ZUKATA KA TABBATAR DA
ZUCIYA TA AKAN ADDININ KA, YA MAI
SARRAFA ZUKATA KA SARRAFA ZUCIYATA AKAN BIYAYYAR KA.
اللَهُمَّ أَصْلِحْ قَلْبِي وَعَمَلِي
YA ALLAH KA GYARAMIN ZUCIYA TA DA KUMA AIYUKANA
WALLAHU A'ALAM
AMSAWA {ABU ABDULLAH}
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.