Shin Da Gaske Ne Kananan Yara Za Su Yi Ceto A Ranar Kiyama?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalam aleykum malam dagaske ne Yara kanana waɗanda suka rasu ko akayi barin su Allah SWT Zai Basu ceto? Gobe kiyama? Dan Allah a taimaka ayi Mani karin bayani.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

    Eh tabbas akwai hujjoji daga Sahihan Hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam dake nuni da cewa lallai akwai ladaddaki da darajoji masu yawa da muminai suke samu, yayin da kananan yaransu suka rasu alokacin kuruciya kuma sukayi hakuri suka jure.

    Misali akwai hadisin da Imamul Bukhariy da Imamu Muslim suka ruwaito ta hanyar Sayyiduna Abu sa'eed Alkhudriy (radhiyal-Lahu anhu) wanda yace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya gaya ma wasu mata cewa: "DUK MATAR DA 'YA'YANTA UKU SUKA RASU, TO ZASU ZAMA KARIYA GARETA DAGA SHIGA WUTA". Sai wata mata tace :"Ya Rasulallahi guda biyu fa"? Sai yace "KODA GUDA BIYUN NE".

    .

    Ga kuma hadisin da Imamut Tirmidhy ya ruwaito ta hanyar Abu Sinan daga Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (radhiyal-Lahu anhu) shi kuma daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam wanda acikin hadisin yace Allah zai umurci Mala'iku su gina wa mutum wani gida na musamman acikin Aljannah, saboda hakurinsa bisa rasuwar ɗansa ko 'yarsa.

    Acikin wani hadisin kuma wanda Imamu Muslim ya riwaito, (hadisi mai lamba 2,635) wani mutum ya zo wajen Sayyiduna Abu Hurairah (radhiyal-Lahu anhu) yace masa "Ya Aba Hurairah,  hakika 'ya'yana guda biyu sun rasu. Ina so ka gaya mun wani hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam wanda zai hakurkurtar damu" Sai Abu Hurairah yace masa "Ai Kananan yaransu, sune Ƙananan yaran gidan Aljannah. Idan ɗayan cikinsu ya haɗu da mahaifinsa ko mahaifansa (afilin Alƙiyamah) zai rike hannunsa ne kamar yadda nake rike da hannunka ɗin nan, bazai sakeshi ba har sai Allah ya shigar dashi da mahaifin nasa gidan aljannah.".

    Sannan Imam Ibnu Ƙayyimil Jauziyyah acikin littafinsa Tuhfatul Maudud akan shafi na 69 yana magana game sa fa'idodin dake cikin yiwa yaro yankan suna (AƘIƘAH), akan lamba ta biyu, yace : "Ita Aƙeeƙah fansa ce ga yaron da aka haifa. 'Aƙiƙarsa zata fansheshi aranar Alƙiyamah, domin yaje yayi ceto ga mahaifansa". Kuma malamai sun ce ba wai wanda aka haifa kaɗai ba, har wanda akayi 'barinsa shima zai ceci mahaifansa. Mutukar dai yakai matakin da an riga an busa masa rai kafin ayi barin nasa. Wato aƙalla yakai watanni huɗu zuwa sama.

    Da fatan Allah shi Ƙara mana hakurin jurewa. Ameen.

    WALLAHU A'ALAM.

    DAGA ZAUREN FIƘHU 07064213990 

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.