Ina Zuba Wa Mijina Maganin Karfin Maza A Shayi Ba Tare Da Ya Sani Ba

    TAMBAYA (159)

    Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Muna tare da mijina Muna zaman lfy amma Sai ya zamana ba ya iya gamsar da ni. Sai nake neman maganin Karfin maza nakesamasa a tea shi inada laifi. Kamin nayi amfani da shi sai na tambaya shin yana chutarwane Ina amfani da herbal ne

    AMSA

    Waalaikumus, warahmatullahi, wabarakatuhu

    Alhamdulillah

    Kusan sama da kaso 50% cikin 100% na Mazajen aure basa iya gamsar da matansu a mu'amalar aure hakan na faruwa ne sakamakon rashin cikakkiyar lafiya daga Mazan Wanda kusan kaso 30% basa damuwa da neman magani, indai zasu gamsu to basu damu da sai matannasu sun gamsu ba

    Wanda hakan Kuma kuskure ne babba Kuma shiga haƙƙin matar ne

    Kuma a kimiyyance masana ilimin Sexologist (saduwar aure) sunce Mata sunfi maza ƙarfin Sha'awa da Kuma daukar lokaci ba ta yi releasing ba, yawancin Mata yayin saduwa sukan kawo sau 2 ko 3 ko sama da Haka gwargwadon karfin halittar da Allaah yayi musu ta Sha'awa sabanin Maza

    Wanda wani namijin idan ya kawo sau 1 to fa shikenan zaiyi watsi da ke ya ƙyale ki anan cikin ƙunci da baƙin ciki Wanda wasu matan mostly suke amfani da yatsunsu don suma su kawo

    Rashin koyi da Sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ne yasa muke ta shan wahala al'amuranmu na yau da gobe. Kamata yayi mijinnaki yayi alwala bayan ya kawo, hakan zai sa ya ƙara samun energy a saduwa ta biyu kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya faɗa a cikin Sahihul Bukhari

    To amman tashin nan ya ƙyaleki shi kansa wata cutar ce mai zaman kanta wanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace ana son da mata da mijin dukkansu kowa ya gamsu, idan shi ya fara kawowa sai ya ci gaba da yi Mata wasa har ta kawo. Hakama ita

    Babban dalilan da suke saka mazan aure saurin kawowa yayin saduwa sune

    1) Idan matar tana yawan taba ko matsa mamansa (breast), zai saurin kawowa. Saboda nonon namiji is very sensitive point

    2) Yawan tuna kyawun matarsa, wanda Sexologists suka ce a wannan yanayin kamata yayi ka dinga tunanin kamar kana cinikin kasuwanci ne anan bawai saduwa ba

    3) Ƙololuwar jin dadin saduwar. Idan kaji kana ƙoƙarin kawowa sai kawai ka yi dogon Jan numfashi ta yanda yunƙurin releasing din zaiyi confusing maniyyin ya koma yaƙi fitowa

    4) Rashin sauka daga kanta at one time. Kana tsaka da Ibadar sai kawai ka sauka ka danyi tattaki ko da na 60 seconds ne, don kayi regaining energy

    5) Matar a sama Kai Kuma a kasa. Kamata yayi mostly ace matar ce a sama saidai gameda wannan fa da akwai illa Kamar Yanda magabata suka fada

    (Duba littafin: Dubbun Nabwy na Ibn al-Ƙayyim Aljauziyya da Dubbun Nabwy na Imamus Siyuti)

    Dangane da maganin ƙarfin maza (Herbal Medicine) da kike zuba masa a tea, indai har ba na cutarwa bane ya halatta inda zai haramta shine idan ya zamana zai cutar da lafiyarsa

    Da akwai wani littafi mai suna: "Guidelines To Intimacy In Islam" ma'ana: Shiriya akan alaƙar auratayya a musulunce, wallafar Mufti Ahmad Ibn Adam Alkautary)

    Yayi bayani sosai kuma daki-daki akan yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar da al'ummarsa yanda ake rayuwar auratayya

    Duk wasu tambayoyi da suke da alaƙa da irin wannan tambayar taki kusan duk akwai amsoshin su a cikin littafin wanda za'a samu Kai tsaye a group din: "MU'AMALAR AURE A MUSULUNCI" a karkashin: USMANNOOR ACADEMY

    Ga masu ra'ayi sai suyi magana a tura musu DOKOKIN group din, in Sha Allaah

    Wallahu taala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.