Nazarin Wakar Siyar/Sira (Tarihin Kyawawan Dabi’un Annabi SAW) Ta Abdullahi Fodiyo (Abdullahin Gwandu)

    Bayanin Takarda: Haruna Umar Maikwari and Habibu Lawali Ƙaura, (2021). Nazarin Waƙar Siyar/Sira (Tarihin Kywawan Dabi’un Annabi SAW) ta Abdullahi Fodiyo (Abdullahi Gwandu) Takardar da Aka buga a SHADAI JOURNAL OF CONTEMPORARY RESEARCH IN HUMANITIES. Published by Faculty of Humanities, Sule Lamiɗo University Kafin Hausa, Jigawa State. June, 2021 Volume 1 No. 1.

    Nazarin Waƙar Siyar/Sira (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi SAW) Ta Abdullahi Fodiyo (Abdullahin Gwandu)

    Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

    Tsakure

    Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙo cikin sauƙi. Marubuta/mawaƙa sukan yi amfani da ita domin jan hankalin mai sauraro ko karatu su isar da saƙo ta sigar rubutawa ko rerawa ga al'umma musamman abin da ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum. Sakamakon haka ne ma wannan muƙala za ta yi nazarin rubutacciyar waƙar nan ta Abdullahi Fodiyo mai takan Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi).An rubuta wannan waƙar a ƙarni na 19, kuma ta taɓo tarihin Annabi SAW da Iyalan gidansa, da Sahabbansa da abubuwan da suka faru a rayuwarsa kamar Hijira, da yaƙe-yaƙe da mu’ujizoji, da wahayi da makamantansu.

    GABATARWA

    Fagen adabi fage ne mai tarin yawa wanda masana da manazarta da yawa suka gudanar da aiki a kansa, kuma har a yau suna a kai wajen gudanar da bincike na duk wani abu da ya shafi adabi. Za a dai ɗan yi tsokaci ne dangane da abin da ya shafi Jigo da Gajerce Jigo da Warwarar Jigo, da wasu salailai da da zubi da tsari da amsa-amo/ƙafiya duk a cikin rubutacciyar waƙar nan ta Abdullahi Fodoyo (Abdullahin Gwandu) ta “Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi).

    Ra'ayoyi mabambanta na Masana adabi sun ta cin karo wajen tsayar da ma'ana guda ɗaya ta waƙa. Sai dai abin sha'awa, duk ma'anonin za a same su suna magana ne da siga iri ɗaya. Kaɗan daga cikin su sun haɗa da: MB Umar (1980) yana ganin "waƙar baka a Hausa kamar sauran harsuna tana zuwa ne a rere, cikin sautin murya ko rauji. Rerawar da ake yi wa waƙa ya sa ba ta zuwa a shimfiɗe gaba ɗayanta sai dai ta zo gunduwa-gunduwa tare da amshi a tsakaninsu".

    Ɗangambo (1982) a wajen wani taro mai suna 'ɗaurayar gadon feɗe waƙa' a cikin takarda ya bayyana ma'anar da cewa:-

    "Waƙa wani saƙo ne da ake gina shi kan tsararriyar ƙa'ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa'idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke ba".

    Waƙa ta bambanta daga taɗi ko magana ta yau da kullum. Aba ce wadda ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna ƙwarewar harshe. Harshen waƙa a bisa kansa cikakke ne duk da cewar ya kauce wa wasu ƙa'idojin nahawu. (Gusau 2005).

    Ƙamusun Hausa a tashi ma'anar waƙa na nufin "wata tsararriyar magana da ake yi kan kari ko rauji" (CHNH, 2006:466).

    Shi kuwa Yahya (2007) cewa ya yi "waƙa tsararriyar magana ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba".

    A irin gudunmuwa ta wannan aiki dangane da abin da ya shafi ma'anar waƙa da cewa, Waƙa tana nufin ƙololuwar hikima da fiƙira da basira da hazaƙa da fasaha ta sarrafa kalmomi bisa ga tsari madaidaici tare da amfani da baiti ko ɗiya a cikin rauji mai daɗin gaske domin nishaɗantarwa tare da jan hankalin mai sauraro ga abin da ake isarwa na saƙo a gare shi.

    NAZARIN WAƘAR SIYAR (TARIHIN KYAWAWAN ƊABI’UN ANNABI)

    Ta

    Abdullahi Fodiyo (Abdullahin Gwandu)

    Salsalar Waƙa:

    Wannan waƙa ta Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi) an tabbatar da Shehu Abdullahi Fodiyo ne ya rubuta ta da kan sa kamar yadda Sa’id ya kawo a littafinsa na ɗaya mai taken “Gudummuwar Masu Jihadi Wajen Haɓaka Adabin Hausa. (Sa'id 1978:53).

    Taƙaitaccen Tarihin Abdullahi Fodiyo (Abdullahin Gwandu)

     An haifi Abdullahi a shekarar 1180, wato 1766. Tsakaninsa da Shehu Usmanu, shekara 13. A hannu Shehu ya tashi shi ya yi tarbiyyarsa ya karantar da shi Alƙur’ani da ilimin Larabci da Fiƙihu da Hisabi da Tafsiri da sauransu. Tun randa Shehu ya fara talifi Abdullahi ne na farkon wanda zai karanta abin da ya wallafa, kafin kowa ya gan shi. Tun tashinsa ba su taɓa rabuwa da Shehu ba tare suke in ka fitar da tafiyar da ya yi a Kano a shekarar 1807. Shi ne ya fara yi wa Shehu mubayi’a sanda aka naɗa shi Sarkin Musulmi, ya kuma zama wazirinsa. Duk gwagwarmayar da aka sha ta jihadi, mafi yawan hare-hare ko mayar da martani ga abokan gaba duka Abdullahi ne ke jagorancinsu. Shahararren yaƙin nan na Tafkin Kwato da hare-haren da aka kai wa Alƙalawa har sau huɗu sun isa su zama misali. ya samu nasarori masu ɗimbin yawa ga hare-haren da ya kai.

     Abudullahi Jarumi ne wajen faɗa da kariya. Ba ya jin tsoron kowa wajen tabbatar da gaskiya komai wuya.

     Bayan ƙare yaƙin jihadi Shehu ya raba ƙasashen da aka ci da yaƙi kashi biyu ya ba Abdullahi yankin Yamma, ya ba Muhammadu Bello ɗansa yankin Gabas, ya damƙa masu ragwamar tafi da mulkinsu.

     Abdullahi ya karanci fannonin ilmi da dama a gurin wasu malamai ban da Shehu. Ya kuma karantu sosai har ma ana kamanta shi da kogin ilimi wanda ba a ga ƙarƙashinsa ba. shi mutum ne mai ƙwazo wajen binciken kowace matsala ta ilmi, ya haifar da fa’idojin masu tarin yawa. Yana da cikakkiyar amincewa da kansa idan dai wajen sha’anin ilmi ne, ga shi kuma da kaifin basira. Ya wallafa littatafai amsu ɗimbin yawa kan fannoni daban-daban na ilmi, musamman wajen siyasa da mulki da shari’a kai har ma da kimiyya. Ya kuma yi waƙoƙi masu yawa a cikin harshen Fillinci da Hausa ban da ma na Larabci.

     Abdullahin Gwandu Allah ya yi masa cikawa a Gwandu a shekarar 1245, wato 1829, yana ɗan shekara 72. (Sa’id 1978:49-50)

    Jigo.

    Ɗangambo (2007:12) Abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo, manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai.

     Jigo a fagen adabi yana nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa Jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke son sadarwa ga jama’a kuma duk wani salo da tsari ko wata dabara da marubuci zai yi amfani da su, zai yi hakan ne da nufin isar da saƙonsa ga jama’a. Sarɓi, (2007:71).

     Da wannan muke gani Jigo a matsayin igiya maɗaura kayan kowane rubutu da aka yi a fagen adabi ta kowane ɓangare wato Zube da Waƙa da Wasan Kwaikwayo in ba da shi ba to kayan za su kwance. A nan jigo na nufin burin zuciyar mawaƙi ko marubuci wanda yake son jama’a su fahimta.

     Kaftin Suru Ummaru Ɗa, Allah ya jiƙansa da rahama yana faɗa a waƙarsa mai suna Jigo. Ya ce:

       Kay yi waƙa ba jigo,

       Ya yi riga ba taggo,

       Yai awaki ba faggo,

       Ga amarya ba ango,

        Ban ga amfani nai ba.

     Wannan ya nuna kenan in aka yi waƙa ba a san jigonta ba to tana da rauni. To abin lura a nan shi ne, ba waƙa kaɗai ba koma wane irin rubutu ne in dai babu jigon da ya sa aka yi shi to aikin banza ne bai da wani amfani.

    A waƙar Abdullahi Fodiyo ta “Sira (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi) , da aka nazarta an gano cewa Jigon wannan waƙar dai shi ne TARIHI.

      Galibi idan mai rubutu bai fito a fili ya faɗi jigon waƙarsa ba to mai nazari yakan yi la’akari da wasu muhimman kalmomin fannu da waƙa ta ƙunsa don ya gane inda aka dosa. An gano jigon wannan waƙar tun daga sunan waƙar da mai ita ya ba ta suna “Sira” wato (Tarihin Kwawawan Ɗabi’un Annabi).

     Ko shakka babu idan mutum ya kalli baitocin waƙar zai ga cewa duk TARIHIN ANNABI take magana a kai, kamar dai yadda za a gani a gaba cikin warwarar jigo da zai biyo baya.

    Gajerce Jigo.

     Ɗangambo (2007:15) ya ce, “A nan wurin za a bi waƙa a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da mawaƙi yake faɗa. Za a yi haka ba tare da yin sharhi, bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Misali ana iya cewa a baiti na 1-3 ya ƙunshi yabon farawa, baiti na 4-7 ya ƙunshi gabatar da Jigo.

     Idan aka yi la’akari da abin da magabata suka faɗa dangane da Gajerce Jigo za a ga cewa, wannan wurin yana buƙatar a fito da hoton bayanin waƙar a taƙaice ana iya ɗaukar ɗiya ko baitoci na waƙar rukuni-rukuni a fito da muhimman abubuwan da take magana a kai.

     Anan wurin za a bi waƙa a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da marubucin waƙar ya rubuta/faɗa. Za a yi haka ba tare da yin sharhi ko bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Ga dai yadda abin yake a wannan waƙar ta “Sira/Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi).

    1.      Mabuɗin waƙar: Ya fara da godiya ga Allah Ubangiji a baiti na 1.

    2.      A baiti na 2-6 ya yi yabo ga Annabi tare da faɗin abin da zai gabatar.

    3.      Daga baiti na 7-12 ya zo da asali da nasabar Annabi Muhammadu SAW.

    4.      A baiti na 13-22 yana bayanin raino da ƙuruciyar Annabi SAW.

    5.      Daga baiti na 13-34 ya bayyana auren Annabi na farko da haihuwa da bayanin sauran iyalan gidan Annabi.

    6.      Daga baiti na 35-38 ya bayyana zuwan Annabi a Sham har zuwan sa a Al’arshi.

    7.      Daga baiti na 39-56 ya yi bayani a kan hijira, da wasu da aka yi hijira da su, tare da faɗin abin da ya auku a wajen hijirar, musamman waɗanda aka je da su.

    8.      A baiti na 57-74 ya kawo yabo da kyawawan halaye kamar kyauta, karrama baƙo, tsabta, neman halal, guje wa haram, sanya sutura, gaskiya, haƙuri, murmushi, da dai makamantansu.

    9.      A baiti na 75-78 ya bayyana mu’ujizojin Annabi.

    10.   A baiti na 79 ya na bayani a kan yaƙin da Annabi ya yi.

    11.  A baiti na 80-81 yana bayanin Hijira zuwa Madina.

    12.   A baiti na 82 yana bayanin Rasuwar matar Annabi Khadijatu.

    13.  Baiti na 83-84 ya bayyana auren Saudatu da A’isha wanda Annabu SAW ya yi.

    14.   A baiti na 85-90 yana bayanin ɗiyan Annabi.

    15.   A baiti na 91-92 ya yi bayanin abinda ya faru a shekara ta biyu bayan Hijira kamar canza Alƙibla.

    16.  A baiti na 93-96 bayanin abin da ya faru a shekara ta uku.Ya bayyana auren Nana Faɗima ‘yar Annabi da Sayyidina Aliyu da haihuwar Hassan

    17.   A baiti na 97-100ya bayyana abin da ya faru a shekara ta huɗu bayan Hijira kamar auren Annabi da Zainab ‘yar Huzaimah, da kuma auren Hindu ‘yar Umayya. Haka muka ya yi bayanin an haramta giya, kuma wannan ya biyo bayan haihuwar Hussain.

    18.   A baiti na 101-106 marubucin ya zo da bayanin abin da ya faru a cikin shekara ta biyar kamar auren Zainab ‘yar Jahashu, da Juwairiya. Haka kuma a cikin wannan shekarar ne aka farlanta aikin Hajji, sannan a cikin ta ne aka saukar da taimama.

    19.   A baiti na 106-113 yana bayanin abin da ya faru a shekara ta shida bayan Hijira.

    20.   A baiti na 114-117 marubucin yana bayani ne na abin da ya faru a cikin shekara ta bakwai bayan Hijira.

    21.  A baiti na 118-121 bayani ne na abin da ya ƙunshi abubuwan da suka faru a cikin shekara ta takwas.

    22.   A baiti na 122-124 bayanin abin da ya faru a cikin shekara ta tara bayan Hijira.

    23.   A baiti na 125 an zo da bayanin abin da ya faru a cikin shekara ta goma bayan Hijira.

    24.  A baiti na 126 bayani ne na abin da ya faru a cikin shekara ta goma sha ɗaya bayan Hijira.

    25.  A baiti na 127-130 marubucin ya yi addu’a sannan ya koma bayanin Khulafa’ur Rashidin.

    26.   Baiti na 131 ya zo da bayanin waɗanda Annabi ya yi wa albishir da Aljanna.

    27.  Baiti na 132-138 bayanin rayuwa da asali da dahimmar Sayyidina Abubakar (RA).

    28.  Baiti na 139-144 ya ƙunshi bayanin rayuwar Sayyidina Umar (RA).

    29.  Baiti na 145-149 ya ƙunshi bayanin rayuwar Sayyidina Hamza (RA)

    30.   Baiti na 150-153 ya ƙunshi bayanin rayuwa Sayyidina Usman (RA)

    31.  Baiti na 154-159 ya ƙunshi bayanin rayuwar Sayyidina Aliyu (RA)

    32.  Baiti na 160-167 ya ƙunshi bayanin rayuwar Ɗalha Bn Ubaidu (RA)

    33.  Baiti na 168-171 ya ƙunshi bayanin rayuwar Sa’ad Bn Abu-Waqqas (RA)

    34.  Baiti na 172 ya na bayanin Sa’id Bn Zaidu

    35.  Baiti na 173-175 yana bayanin Abdurrahman Bn Auf

    36.  Baiti na 176-180 ya ƙunshi bayanin rayuwar Abu-ubaida (RA)

    37.   Baiti na 181-190 ya ƙunshi addu’o’i, da shirin naɗe waƙar.

    38.   Baiti na 191 kuma ya zo da marufin waƙarsa.

    Warwarar Jigo.

     Anan za a yi sharhi ne kan Jigo gaba ɗayansa. Za a duba shi dangane da jawaban jigo, da kuma abin da waƙar ta faɗa a taƙaice. To amma muhimmin abin shi ne za a duba lungu-lungu na waƙar dangane da jigo tare da ƙarin bayani daga dukkannin abin da za a iya danganta waƙar da shi. Misali ana iya kawo ƙarin bayani don kafa hujja da misalai daga Alƙur’ani, Hadisi, littattafai, muƙalu, da ra’ayoyi iri daban-daban da dai sauran bayanai da za su taimaka wajen gane abin da waƙar ta ƙunsa da inda aka dosa. Ɗangambo, (2007:16)

    A nan za a yi sharhi na gaba ɗaya tare da fitowa da saƙwannin wannan waƙa daki-daki domin ganin yadda abin yake wakana. Ga yadda abin yake.

    Addu’ar Rufewa

     Mawallafin wannan waƙar ya fara buɗe waƙarsa da godiya ga Allah. Ga dai yadda yake cewa:

    1. “Na gode Sarki Jalla don rahama tasa,

      Na yo salati ga Annabi Manzo nasa.”

     Wannan tana ɗai daga cikin hanyoyin da mafi yawan marubuta waƙoƙi suke amfani da ita.

    Babban Jigon Waƙar Siyar (Tarihin Kywawan Ɗabi’un Annabi SAW)

     Bayan mawaƙin ya fara da sunan Allah a baiti na farko, sai ya fara gabatar da gundarin jigon waƙar a baiti na huɗu, wato TARIHI, inda yake cewa:

    4.  Sannan mu tsara Siyar na Annabi Ɗahiri,

      Don masu bege nai su ƙaru da so nasa.

     Idan muka lura da kalmar Siyar wato mai nufin Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabida Abdullahi Fodiyo ya yi amfani da ita a wannan baiti, za mu fahinci cewa ya fito da jigon waƙarsa a fili. Daman akwai hanyoyi uku da ake bi a gano jigo. Kamar ta hanyar sunan waƙa ko marubucin ya rubuta a cikin waƙarsa (ya faɗa) ko a yi amfani da kalmomin fannu a gano. Wannan waƙa dai Abdullahi Fodiyo ya bayyana jigon tun ga sunan da ya ba waƙar. Haka kuma a cikin waƙar ya bayyana a baiti na huɗu (4).

    Nasabar Annabi Muhammadu SAW

     A baiti na 7-11 ne mawallafin ya fara warwarar wannan jigo inda ya ce:

    7. Shi ɗa ga Abdullahi Abdulmuɗɗalib,

      Ɗan Hashimi, Abdulmunafi uba nasa.

     .....................................................................................................

    11.  Sannan uwa tai Amina ‘ya wahhabu

      Abdulmunafi ɗan Kilabu ka gam masa.

     Daga baiti na 8-11, ya ci gaba da warwarar wannan jigo yana nuna nasabar Annabi (SAW) yana cewa , “ Shi Fiyayyen halitta ɗa ne ga Abdullahi, shi kuma Abdullahi ɗa ne ga Abdulmuɗallibu, shi kuma ɗanHashimu, Hashimu ɗan Abdulmunafi, shi kuma ɗa ne ga Ƙusayyu, shi ko ɗa ne ga Kilabu, shi kuma ɗan Marratu, shi kuma ɗan Ka’abu, Ka’abu ɗan Luwayyu, shi kuma ɗan Galibu Fihru, shi kuma ɗan Maƙuraisha, haka dai yabi salsala har sai da ya dangane ga Adnan. Kamar dai yadda abin ya ke a Littafin Umar Abdujabbar (ba kwanan wata) littafi mai suna Khulasatul Nurul YaƙinDarasi na 2 shafi na 6. Haka kuma idan aka duba Mukhtasar Siratul Rasul SAW na Imamu Muhammad Bin Abdulwahab shafi na 36. Kamar yadda yake cewa a wasu baituka kamar haka:

    8. Shi ko Ƙusayyu Kilabu Marratu Ka’abu ɗa,

      Ga Luwayyu Galibu Firhu maƙuraisha tasa.

    9.  Ɗan Maliki ɗan Nalaru ɗa ga Kinanatu,

       Ɗa gun Huzaimatu ɗa ga Madrikatu ka sa.

    10. Iliyasu ɗan Mulari Nizami Mu’addi ɗan,

       Adnana nan garai tsayin sihha tasa.

    11. Sunan Uwa tai Amina ‘yar Wahhabu,

      Abdulmunafi ɗan Kilabu ka gam masa.

     Daga jin yadda marubucin waƙar ya tsaro sunayen kakannin Annabi za ka ce dai ya san Annabi kuma ya karanci tarihinsa. Kuma wannan yana cikin tarihi haka tsarin zuri’ar Annabi yake kamar dai yadda ya zo a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin a darasi na 2 shafi na 3. Kuma wannan tarihi akwai shi a littattafin Mukhtasar Siratul Rasul SAW na Imamu Muhammad Bin Abdulwahab shafi na 36.

    Haihuwar Annabi SAW

     Abdullahi Fodiyo ya zo da bayanin haihuwar Annabi SAW a baiti na 12. Ga dai abin da yake cewa:

    12.  Ran Attanin biyu dagga Gani ga Shekara,

      Koran Sahabul fili Makka ka haifa sa.

     Wannan ko shakka babu tarihin ya inganta idan aka duba littafin Khulasatul Nurul Yaƙin a darasi na 3 shafi na 6.

    Rainon Annabi Muhammadu SAW

     Marubucin ya bayyana tarihin rainon Annabi a wasu baitoci, misali a baiti na 13-15

    13. Ya tsotsi nono gun Suwaibatu ta zamo,

      Ta sam ɗiyauci barkacin reno nasa.

    14. Ai ɗanta Masruhu da Hamzatu sunka sha,

      Da uba na Salmatu don suna wari nasa.

    15. Sannan fa Sa’adiyya Halimatu tar riƙa,

      Tab ba shi nono har sa’ar yaye nasa.

     A waɗannan baituna marubucin bayyana yadda aka raini Annabi SAW, kuma ya bayyana waɗanda suka raine shi wato Suwaiba da kuma Halimatu Sa’adiyya. Waɗannan sun ba shi nono kuma sun rene shi bayan rasuwar mahaifiyarsa. Kuma wannan ya zo a Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 2 shafi na 8.

    Tarihin Auren Annabi Muhammadu SAW

     Annabin Allah ya yi aure yana ɗan shekara shekara 25. Aurensa na farko ya yi shi da Nana Khadija, kuma ya haihu da ita. Kamar yadda ya zo a a Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 8 shafi na 11. Haka kuma Marubucin waƙar ya zo da wannan bayani a baiti na 23. Ga dai yadda lamarin yake gudana.

    23. Ya kai biyat bisa shekara ishirina yai,

      Amren Hadijatu don tana mai so nasa.

    24. Sun haifi Ƙasimu yay yi biu ɗai yar rasu,

      Bayansa sun sam Zainabu ƙanwa tasa.

    Tarihin Auren Ruƙayya da Sahabi Usman Ɗan Affan.

     Annabi Muhammadu SAW ya ba da auren ‘yarsa Ruƙayya ga Sahabi Usman ɗan Affan. Kamar yadda ya zo a Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na12 shafi na 24. Abdullahi Fodiyo ya bayyana wannan tarihi a cikin waƙarsa. Ga dai abin da yake cewa:

    28. Mai bi ma Zainabu ko Ruƙayyatu ta ku san,

      Ta amri Usmanu da an ka mayas masa.

    29. Bayan fa ta rasu, Ummul Kulsumi na’am,

      Ƙanwa ga Faɗima yad daɗo nuri nasa.

     Wannan ya zo a tarihi cewa Sayyadina Usmanu ɗan Affan ya aure Ruƙayya, ‘yan Annabi Muhammadu, bayan ta rasu kuma aka aurar masa da Ummul Kulsum, wannan ma ya sa ake kiransa da haske bisa haske (Nurun-Ala_Nur). Kuma ya zo a cin Alƙur’ani Mai girma a Suratul Baƙara, aya ta 90-91.

      A wannan shekarar ne Annabi Muhammadu ya auri Hafsat ‘yar Sayyidina Umar da Zainab Bintu Huzaimatu. Haka kuma a wannan shekarar ce aka haifi Hussain ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib. Kuma a wannan lokaci aka haramta shan giya. Ga dai misalai na abin da Abdullahi ya rubuta a waƙarsa.

     Haka kuma Abdullahi ya ci gaba da bayar da labarin auren ɗiyar Annabi Faɗimatu matar Sayyadina Aliyu in da ya ci gaba da bayar da tarihi a baiti na 30. Ga dai abin da yake cewa:

    30. Kun san Aliyu shi ka amren Faɗima,

      Sunsam Hasan da Husaini muhusinu bisa sa.

    31. Haka Zainabu da uwa ta Kaltumi Umar,

      Ya amri wannan don shi sam nasaba tasa.

     Haka dai ya yi ta bayar da tarihin ‘ya’yan Annabi da waɗanda suka aura da waɗanda aka haifa. Kuma wannan tarihin ya zo a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. A darusa daban-daban.

    Tarihin Hijirar Annabi SAW

     Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hijira daga garin Makka zuwa Madina. Wannan ya zo a cikin littafinKhulasatul Nurul Yaƙin. Abdullahi ya zo da tarihin hijira daga Makka zuwa Madina da abubuwan da suka faru a cikin jihirar. Kamar da yadda Abduljabbar ya zo da bayani a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. Ga dai yadda bayanin yake a cikin waƙar Sira.

    39.                          Hijiram Musulmi Makka ta yi Madinata,

      Daga Annabi sai Bubakar ka jira nasa

    40.                          Su goma sha ɗai az zumai ga uba nasa,

      Gada Hamza Abbas sunka samu biya tasa.

    41.                          Su az Zaubairu Liraru Harisu Jahlu sai,

      Da Muƙawwimu da uba na Ɗalibu bisa sa.

     Bayan Marubucin ya gama bayyana waɗanda aka yi hijira da su sai ya shiga bayar da tarihin halayen Annabi SAW. Ga dai abin da yake faɗa:

    72. Uzuri shi ka wa ‘yan Adam bisa ya sano,

      Hali shina ƙyale su don rahama tasa.

    ..............................................................................................................................

    74.  Mai murmushi na lokacin gamuwa da shi,

      Halinsa yin shiu, sai zikir himma tasa.

     Marubucin kuma ya shiga bayar da tarihin Mu’ujizojin Annabi SAW. Kamar yadda yake cewa a waɗannan baitikan.

    75. Kuma mu’ujiza tai ta wuce haddin ƙida,

      Ƙur’anu ya isu mu’ujiza aiki nasa.

    76. Mashi biyat da baka biyat garki ɗaya,

      Haka nan takubba goma an ka ƙidai masa.

    77.  Kibiya kwari nai an ka jefa rijiya,

      Taɓ ɓuɓɓugo da ruwanta don barka tasa.

     

     Bayan Marubucin ya gama bayar da tarihin mu’ujizojin Annabi SAW. Sai ya sake mayar da hankali a wajen bayanin Hijira. Ga dai abin da yake cewa:

    80. Ya shekara sha ukku Makkata duk shina,

      Manzo sa’annan ya nufo hijira tasa.

    81.  Ta Madina shi da Abubakar sai Amiru,

      Su am Musulmi ɗan Uraiƙidu ƙad asa.

     Marubucin ya shiga bayyana abin da ya faru a cikin Hijira tun daga shikara ta farko har zuwa shekara ta sha ɗaya da yin hijira. Ga dai yadda lamarin yake a cikin waƙar.

    82.  Rasuwar Hadijatu dud da baban Ɗalibu,

      Bayanta goma ga shekara aike nasa.

    .....................................................................................................................................

    85.  Ya zo Madina gida na Halidu yash shiga,

      Har anka gyra wurin sala da gida nasa.

     A wannan shekara ne aka gyara salla ta koma huɗu kamar dai yadda Marubucin ya faɗa a baiti na (89).

    89.  Nan anka gyara sallarmu tak koma fuɗu,

      Yaf fori muminai jiyayya don nasa

    Shekara ta Biyu

     Abdullahi Fodiyo ya bayyana abubuwan da suka faru a shekara ta biyu. Ga dai abin da yake faɗa:

    91.  Ga ta biu ga hijira anka jirkita ƙiblatu,

      A cikinta ko Ramalana anka farlata sa.

    92.  A cikinta kono yaw wajabta, Ruƙayyatu,

      Nan taw wuce dagab Badar sa’a tasa.

    93.  Amren Aliyu da Faɗimah nan yay yi ya-,

      Ƙin Ƙainiƙa’a da idi sa lahaya tasa.

     A wannan shekarar ta biyu marubucin ya zo da tarihin abubuwan da suka faru. Kamar yadda muka gani. Sannan tarihin ya zo a littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. Na biyu, a Darasi na bakwai (7) shafi na 16.

    Shekara ta Uku

     A wannan shekara ta uku da hijirar Annabi SAW. Wasu abubuwa sun auku kamar yadda Abdullahi Fodiyo ya zo da su a cikin waƙarsa.

    94.  Ga ta ukku yai amre na Hafsatu ‘yar Umar,

      Don abida ta mai biyas Sunna tasa.

    95.  Ƙauran Naliru faɗa na Uhudu cikinta na,

      Nan anka haifi Hasan, haramta giya tasa.

    96.  Sannan Fiyayye yay yi amren Zainabu,

      Ce, ‘yar Huzaimah wata takwas ɗai tag gusa.

     Wannan tarihi da Abdullahi Fodiyo ya bayyana abubuwan da suka faru wato auren Hafsat da yaƙin Uhudu, da haihuwar Hasan ɗan Sayyidina Aliyu da haramta giya, da auren Zainab Bintu Huzaimah. Wannan tarihi ya zo a Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 8 shafi na 18.

    Shekara ta Huɗu

     Abudullahi Fodiyo (Rahima hil Lahu lahu) ya bayyana duk abubuwan da suka faru a wannan shekara.

    97. Ya shekara ta fuɗu yay yi amren Hindu ‘yar,

      Baban Umayyata ɗan Mugiratu ce masa.

    ..........................................................................................................................

    99. Nan anka haifi Hussaini an ce nan giya,

      Daɗa tah haramtaNaliru nan ƙaura tasa.

     A wannan shekara kamar yadda muka gani Abdullahi ya bayyana muna cewa a cikin wannan shekara ne Annabi SAW ya aure Hindu kuma a ciki ne aka Haifi Hussaini ɗan Sayyadina Aliyu, a duk a wannan shekarar aka haramta shan giya. Wannan ya zo a cikin Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 12 shafi na 24.

    Shekara ta Biyar

     A shekara ta biyar an samu wasu abubuwa masu muhimmanci sun faru na tarihi kuma su waɗannan abubuwa sun zo a cikin tarihi a littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. Ga dai abin da Abdullahi ke faɗa a cikin waƙarsa.

    101.  Ta biyat ga hijira tai Madina Ubangiji,

      Yaɗ ɗamra amre nai da ‘yar goggo nasa.

    102. Ita Zainabu ‘yar Jahashu bayan ta fito,

      Gun Zaidu yaro nai ɗiyautacce nasa.

    103.  Nan anka yo fama da Dauma da Hanɗaƙu,

      Da Ƙuraizatu da ta Masɗalaƙ nan A’isa.

    104.  Tas samu barra anka kama Juwairiya,

      Tas sam ɗiyauci nan da yin amre nasa.

    105.  A cikinta Hajji yaf faralta da shamakin,

      Mata, tayammamu nan garat jiɗa tasa.

     A wannan shekarar kamar yadda Abdullahi Fodiyo ya ba mu tarihin abin da ya faru ya bayyana cewa Annabi ya auri ‘yar gwaggonsa wato Zaiban ɗyar Jahashu. Bayan ta fito ga Zaidu yaronsa wanda ya ɗiyauta. Kuma ya bayyana a cikin shekarar ne aka wanke Sayyada A’isha daga zargin da aka yi mata. Kuma duk a cikin shekarar aka auri Juwairiyya, aka kuma ‘yanta ta. Wannan tarihi ya zo a littafin Khulasatul Nurul Yaƙin.Darasi na 15 shafi na 30.

    Shekara ta Shida

     Bayan shekara ta shida da hijira Annabi SAW ya yi roƙon ruwa, kuma a shekarar ne aka saukar da Surar Ƙad Sami. Sannan duk a wannan shekara ya yi aike ga wasu sarakuna su shidda duk suka bi shi suka yi mubayi’a. ga dai abin da Abdullahi Fodiyo ya faɗa a cikin waƙwarsa:

    106.  Ga ta shidda yai roƙon ruwa da gudummuwa,

      Yaƙi na gaba Huɗaibiyya bai’a tasa.

    107.  Tuba ta Dausi sa da jiɗaƙ Ƙad Sami,

      Hukuncin muharibbai garat jiɗa tasa.

    108.  A cikinta ya aika zuwa ga sarakuna,

      Su shidda sashe sun ka karɓi kira nasa.

     Abubuwan da Marubucin wannan waƙa ya faɗa a wannan shekara bayan an yi hijira zuwa Madina sun tabbata, kamar dai yadda suka zo a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 22 shafi na 42.

    Shekara ta Bakwai

     A wannan shekara Marubucin ya zo da bayanin yaƙin Haibar, wanda a dalilin wannan yaƙi ne aka auri Habiba. Sannan ya auri Safiyya. Kuma a cikin wannan shekarar ne aka auri Maimunatu. Ga dai abin da yake cewa:

    114.  Ta bakwai yai amren Habibatu ‘yar Abu,

       Safiyanu Abdu Munafi nan gamuwa tasa.

    ................................................................................................................................

    116.  Can Haibara nan anka kana Safiyyatu,

       Ya bar ta ya amre ta don rahma tasa.

    117.  Ya amri cana zuwansa Makka na Umratu,

       Maimunatu ƙarshe na yin amre nasa.

     Abdullahi ya zo da tarihin abin da ya faru a wannan shekara, musamman ya zo da yaƙin Haibar da kuma auren Habiba da Safiyya da Maimunatu. Wannan tarihi ya zo a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 23 shafi na 48.

    Shekara ta Takwas

     A shekara ta takwas bayan hijira an samu wasu sun shiga addinin Musulunci. Kuma wasu daga cikin Musulmi sun rasu/mutu a wannan shekara. Kuma a wannan shekarar ne aka yi yaƙin Ɗa’ifa da Hunaini. Ga dai abin da Abdullahi Fodiyo yake cewa:

    118.  Ta takwas ga Hijira Amru Asi da Khalidu,

      Usmanu Ɗalhatu sun shigo dini nasa.

    119.  Nan Zaidu, Ja’afaru dud da ɗan Affanu nan,

      Suka sam shahada hari na Mu’utatu don nasa.

    120.  Sannan fa yai yaƙi na Makka da Ɗa’ifa,

      Da Hunaini Ibrahimu nan aka haifa sa.

      A wannan shekarar ce Annabi ya samu wasu suka karɓi addinin Musulunci, sannan akwai wasu da suka rasa rayukan su a sakamakon yaƙin da aka yi na Mu’utatu. Kuma a wannan shekarar ne aka yi yaƙin Makka da Ɗa’ifa. Wannan ya zo a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 29 shafi na 55.

    Shekara ta Tara

     Bayan shekara ta tara ga Hijira an yi yaƙin Tabuka, kuma a wannan shekarar ne Sayyidina Abubakar ya yi aikin Hajji. Haka kuma Ummu Khulsum ɗiyar Annabi ta rasu a wannan shekarar ita da najashi. Ga dai abin da Abdullahi Fodiyo ke faɗa a cikin waƙarsa.

    122. Yaƙin Tabuka zuwa Haji na Abubakar,

      Sannan Li’an ta tara ga yin Hijira tasa.

    123.  Nan Ummu Kulsumi ɗiya tai tar rasu,

      Hakanan Najashi Mumini ma so nasa.

     Wannan tarihi da Abdullahi Fodiyo ya zo da ya tabbata a cikin littafin Khulasatul Nurul Yaƙin.Darasi na 37. Shafi na 68.

    Shekara ta Goma

     Bayan shekara ta goma ɗan Annabi SAW mai suna Ibrahim ya yi aikin Hajji. Ga dai abin da Abdullahi Fodiyo yake cewa.

    125. Ga ta goma ɗa nai yaw wuce Ibrahi nan,

      Yaz zo shi Hajji nan cikin dini nasa.

     Wannan ya zo a tarihi musamman idan aka duba littafin Khulasatul Nurul Yaƙin.Darasi na 40. Shafi na 74.

    Shekara ta Goma Sha Ɗaya

     Rasuwar Annabi SAW bayan shekara ta goma sha ɗaya. Abdullahi Fodiyo ya zo da wannan a cikin waƙarsa. Ga dai abin da yake cewa:

    126.  Sha ɗai ga Hijira Gani yaj ji jiki nasa,

      Ran Attanin sha biu garai ƙaura tasa.

     Annabi SAW ya yi wafati/rasu bayan shekara goma sha ɗaya ga hijira, kamar da yadda Abdullahi Fodiyo ya ba mu tarihi a cikin waƙarsa. Haka kuma wannan tarihi ya zo a littafinKhulasatul Nurul Yaƙin. Darasi na 45 shafi na 81.

    Tarihin Khulafa’ur Rashidin a Taƙaice

     Abdullahi Fodiyo ya bayyana Khulafa’ur Rashidin a cikin waƙarsa. Inda har ya kawo su huɗu kamar yadda suke. Ga dai abin da yake cewa:

    128.  Zaidun Ubayyu da Amiru da Mu’awiya,

      Kulafa’u su fuɗu kun ji marubuta nasa.

     Bayan ya kawo Khulafa’u a baiti na 131 sai ya ƙudurci ya zo sunayen waɗanda Annabi SAW ya yi wa albishir da Aljanna tun nan duniya, kuma su waɗannan sahabbai su goma ne. yayin da ya zo da bayanin kowanensu a taƙaice yadda za a iya gane su. ya ɗan gutsuro tarihin rayuwara wasu kaɗan daga cikinsu, kuma ya faɗi irin himmomin wasu da. Ga dai yadda abin yake gudana a cikin waƙar

    131. Ku ji goma zaɓaɓɓu da yaw wa albishir,

      Babbansu Abdullahi as sunan nasa.

     A nan marubucin waƙar ya yi matashiya, yayin da ya faɗa da bakinsa cikin waƙar cewa waɗanda aka yi wa albishir da Aljanna su goma ne, don haka sai ya shiga kawo su.

    Taƙaitaccen Tarihi Game da Sayyidina Abubakar (R.A)

     Abdullahi Fodiyo ya kawo taƙaitaccen tarihin Sayyidina Abubakar (RA). Yayin da ya zo da nasabarsa da kuma irin halayensa da himmarsa wajen taimaka wa addinin Musulunci. Fodiyo ya fassara Sahabi Abubakar (RA) daidai da yadda aka zo da tarihinsa a cikin littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. Ga dai tarihin da Fodiyo ya zo da shi a cikin waƙarsa.

    132.  Shi a’ Abubakari Abu na Ƙuhafatu,

      Tsohonsa na Usumanu ko aka ce masa.

    133.  Ɗan Amiru Ɗan Amru Ka’aba da Sa’adu ce,

      Ɗan Taimu ce Ɗan Marratu magana tasa.

    134.  Salma uwa ta ga Abubakar ta silmi kau,

      ‘Yar Saharatu kakansa ɗai da uba nasa.

    135.  Shi ya rigsi gaskata Annabi yar ragai,

      Kowa ga tanyo tsai da addini nasa.

    136.  Shi yar rigai kowa bayassa cikin sala,

      Shi yar ragai tanyon masallaci nasa.

    137.  Ya bada Jumlad dukiya tai don biɗa,

      Yarda ta Allah anka ko karɓa masa.

    138.  Wat tanyi Annabi yin zaman kogon hira,

      Sai shi da Allah yaf faɗo suhuba tasa.

     

     Daga baiti na 132 har zuwa baiti na 138 marubucin ya zo da taƙaitaccen tarihin Sayyidina Abubakar, a ciki ya zo da asalinsa/nasabarsa, kuma ya faɗi irin himmarsa da ƙwazonsa wajen taimaka wa addinin Musulunci, da biyayya ga Annabi SAW. Wannan tarihi ya zo a cikin littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. A shafi na 15-18.

    Taƙaitaccen Tarihi Game da Sayyidina Umar (RA)

     Umar (RA) yana daga cikin Sahabban Annabi SAW kuma yana daga cikin waɗanda Annabi ya yi wa albishir da shiga Aljanna tun nan duniya. Abdullahi Fodiyo ya zo da taƙaitaccen tarihinsa a cikin waƙarsa daga baiti na 139-144. Ga dai abin da ya ke cewa a cikin baitukan.

    139. Sanna Umaru Faruƙu ɗan Haɗɗabi ɗa,

      Ga Nufailu shi ko Abdu Uzza bi nasa

    140. Ga Rahabu Abdullahi Garɗo Razahu ɗa,

     Ga Adiyyu Ka’abu Luwayyu nan gamuwa tasa.

    141.  Sannan uwaf Faruƙu Hannatu Hashimu,

      Yah haifa ta Mahazumu ad dangi nasa.

    142.  Ranad da yam Musulunta addin fai-da-fai,

      Aka yinsa bayan can ana ɓoyo nasa.

    143.  Jama’am Musulmi sun yi murna kafirai,

      Sun tsorta don ƙarfi da zarumci nasa.

    144.  Can radda Uthatu yat tarai domin faɗa,

      Yak kada Uthatu yah haye ga ciki nasa.

     Fodiyo ya zo da taƙaitaccen tarihin Sayyidina Umar (RA) a cikin baiti na 139-144. Kuma ya bayyana asalinsa da halayesa da zaruntakarsa. Wannan tarihi ya bayyana a cikin littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. A shafi na 18-22.

     Bayan Fodiyo ya zo da bayanin Sayyidina Umar (RA) ya kuma kawo taƙaitaccen tarihin Sayyidina Hamza (RA). Duk da cewa, wasu malamai suna ganin Sayyidina Hamza ba ya cikin waɗanda aka ce an yi wa albishir da Aljanna amma Abdullahi Fodiyo ya zo da shi a cikin jerin waɗanda aka yi wa Albashir. Haka kuma ya zo da tarihin zaruntakarsa da himmarsa ga addinin Musulunci. Ga dai yadda ya bayyana a waƙar.

    145. Zaki na Annabi Hamza ko hakana shike,

      In ya yi rura kafirai su ruƙurƙusa.

    146.  Tambai Abujahalin da yag gilma masa,

      Yash sha shi gora nan ga kai yat tartsa masa.

    147.  Shaiɗanu ko inwat Umar tsoro shi kai,

      Bai yarda dacewa da shi hanya tasa.

    148.  Biyuɗin ga su na at takubban Annabi,

      Kwat tashi gilma mai su kaste wuya nasa.

    149.  Hatta Mala’iku fa sun yi farin ciki,

      Ranad da yam musulunta don himma tasa.

     Waɗannan baitoci sun zo da tarihin Sayyidina Hamza da jarumtarsa da himmarsa ga addinin Musulunci. Wannan ko shakka babu idan aka lura Sayyidina Hamza ya yi lokaci da annabi kuma ya sha fama, ya taimaki addinin Musulunci.

    Taƙaitaccen Tarihin Sayyidina Usman (RA)

     Sayyidina Usmanu ɗan Affan ya riƙa Khalifa bayan Umar ɗan Haɗɗab ya yi wafati, kuma shi Sahabi ne wanda ya auri wasu daga cikin ‘ya’yan Annabi SAW. Wanda ma har aka yi masa laɗabi da Zunuraini. Abdullahi Fodiyo ya zo da bayanin taƙaitaccein tarihin Sayyidina Usman a cikin waƙarsa kuma ga abin da yak faɗa:

    150.  Sanna ka ce Usmanu ɗan Affanu ɗan,

      Asi Umayyatu Abdu Shamsi ka gam masa.

    151.  Mai Hijirataini ta gun Habash da Madinatu,

      Ya amri biu ‘yan Annabi mata nasa.

    152.  Harda ta Alƙur’anu anka sanam masa,

      Yin Bai’atul Rilwanu Annabi yai masa.

    153.  Kyauta garai mai yawa da kumya mai yawa,

      Hatta Mala’ikku suna kumya tasa.

     Abdullahi Fodiyo ya zo tarihin Sayyidina Usman ɗan Affan yayin da ya faɗa cewa, ɗan Affa ne ɗan Asi ɗan Umayyah a nan ya zo da nasabarsa. Haka kuma ya zo da tarihin auren ‘ya’yan Annabi da Sayyidina Usman ya yi, wato auren da ya sa aka kiransa Zunuraini (Ma’abuci haske biyu) ya ƙara da cewa wannan auren har a Alƙur’ani Mai tsari an faɗa a suratul Baƙara aya ta 90-91. Haka kuma ya zo da bayanin Hijirar da ya yi har sau biyu wato ta Habasha da kuma ta Madina da aka yi da shi. Wannan tarihi ya tabbata kuma idan aka duba littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. A shafi na 23-26 ya a samu wannan.

    Taƙaitaccen Tarihin Sayyidina Aliyu (RA)

     Sahabi Aliyu (RA) yana daga cikin waɗanda Annabi ya yi wa albishiri da Aljanna, kuma shi ka kasance daga cikin zuri’ar Annabi SAW. Haka kuma Aliyu (RA) shi zarumi ne kuma suruki ga Annabi SAW, ya riƙa Khalifa shi ma kamar sauran sahabbai, ya yi adalci ya yi hidima ga Annabi SAW. Abdullahi Fodiyo ya zo da shi a cikin jerin waɗanda suka samu albishir na Aljanna tun nan duniya ga Fiyayye Annabi SAW. Ga dai abin da yake cewa.

    154.  Sanna Aliyu ubansa farda na uwa,

      Tasa Faɗima kakanta ɗai da uba nasa.

    155. Shi an na farko yara duk ga musulumtaka,

      Mabiyi na Annabi na sa’ah Hijira tasa.

    156. Was samu auren Faɗima face shiya,

      Wah haifi ɗa tamka Hasan da zumu nasa.

    157.  Ba tamkacinsa cikin maza ranaf faɗa,

      Ɗan Abdu Wodi ya tarai ya kai ƙasa.

    158.  Can Haibara ƙyauren garin nan yac cire,

      Yai garkuwa ta faɗansa don ƙarfi nasa.

    159.  Ƙarfi da yaji an sano su gare shi duk,

      Dangi na Hashimu babu mai woba tasa.

     Daga baiti na 154-159 Abdullahi Fodiyo ya zo da tarihin Sayyidina Aliyu (RA), kuma ya faɗi dangantakarsa da Annabi SAW ya kuma himmarsa wajen tsayar da Musulunci da ƙafafunsa. Haka kuma ya zo da bayanin zarumtakarsa duk a cikin waƙar. Wannan bayani da zo a littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. a shafi na 27-30.

    Taƙaitaccen Tarihin Ɗalha Ɗan Ubaidullah (RA)

     Ɗalha ɗan Ubaidullah (RA) yana daga cikin Sahabban da Annabi SAW ya yi wa albishir da Aljanna tun nan duniya. Abdullahi Fodiyo ya zo da taƙaitaccen tarihinsa a cikin waƙarsa. Ga misalin yadda Abdullahin Gwandu ya zo da baitukan.

    160.  Baicinsa Ɗalhatu ɗan Ubaidullahi ɗan.

      Usmanu wanda Abubakar shike ɗa nasa.

    161.  Ce Saudatu ‘yar Hadrani tah haife sa,

      Ranah Hunainu ga judu anka ɗafanta sa.

    162.  An ce da shi ran Uhudu Khairu Tabuka ko,

      Fayyadu duk laƙanin ga Annabi yai masa.

    163.  Bai kau ba ranar Uhudu yab bar Annabi,

      Halbi da fama ɗai shikai a gaba nasa.

    164.  Da Zubairu ɗa ga Awamu ɗa ga Khuwailidu,

      Baban Khadijatu gun Ƙusayyu gamo nasa.

    165. Yannan uwassa Safiyya goggon Annabi,

      Shi yar rigai kowa haminya don nasa.

    166.  Shi anka ba tuta ga fatahu kaza Badar,

      Shi Annabi yac ce farantacce nasa.

    167.  Ya gadi ƙarfi dud da zarumci jihat,

      Kawunsa Hamza kaza jiha ta uba nasa.

     Abdullahi Fodiyo ya zo da tarihin Ɗalhatu ɗan Ubaidulli, a cikin baiti na 150-167 kuma ya zo ta taƙaitaccen tarihin asalinsa da himmarsa wajen tabbatar da addinin Musulunci. Wannan tarihi ya zo a cikin littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. 2 a shafi na 1-5.

    Taƙaitaccen Tarihin Sa’adu Ɗan Abu-Waƙƙas (RA)

     Sa’adu Ɗan Abu-waƙƙas yana daga cikin sahabban Annabi SAW. Kuma yana daga cikin waɗanda Annabi SAW ya yi wa albishir da Aljanna tun nan duniya. Abdullahi Fodiyo ya zo da wannan tarihi a cikin waƙarsa. Ga dai yadda batun yake:

    168.  Baicinsa sai Sa’adu ɗan Abu-waƙƙasi shi,

      Ɗan Maliki ga Kilabu nan gamuwa tasa.

    169.  Ɗa ko ga Annabi shi uwa tai Hannatu,

      Ai ‘yar Abu Sufuyanu nan kaka gam masa.

    170. Shi yar riga kowa ga halbawa sabad-

      Da Jihadi Rabi’u tanbaya ka sanm masa.

    171.  Biɗi sabiƙina ka sa shi Zaidu ubansa kau,

      Tun jahiliyya yay yi imanci nasa.

     Daga baiti na 168-171 Abdullahi Fodiyo ya zo da bayanai na asali/nasabar Sa’ad Bin Abu-waƙƙas. Ya bayyana cewa shi ɗan Malik ne. Wannan tarihi ya tabbata a littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. 2 a shafi na 16-19.

    Taƙaitaccen Tsokaci a Kan Sa’idu Ɗan Zaidu (RA)

     A wannan waƙar Abdullahi Fodiyo ya sa Abdurrahman ɗan Auf a cikin jerin waɗanda Annabi SAW ya yi wa albishir na Aljinna tun nan duniya. Ga dai abin da yake cewa:

    172.  Sanna Sa’idu na Zaidu Amru Nufailu ce,

      Kakan Umar shi a’ uban kaka nasa.

     Wannan nasaba ce ta Sa’id Bin Zaid. Wannan nasaba da Abdullahi Fodiyo ya faɗa, ta zo a cikin littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. 2 a shafi na 20-23.

    Taƙaitaccen Tsokaci a Kan Abdurrahman ɗan Auf (RA)

     Abdulrahman ɗan Auf yana daga cikin sahabban Annabi SAW da aka yi wa albishir da shiga Aljanna tun nan duniya. Wannan ma ya sa Abdullahi Fodiyo ya ambace shi a cikin baiti na 173-175. Ga dai abin da yake cewa.

    173.  Ɗan Aufu shi ne Abidur Rahmani sa,

      Shi cikinsu na ga Kilabu ko kaka gam masa.

    174.  Shaffa’u ko ita ce uwa tai taz zamo,

      ‘Yar Abdu Aufu goggo ta ga uba nasa.

    175.  Rawaninsa Annabi yan naɗa mishi shi ga kai,

      Ga Tabuka kau yas sa shi limanci nasa.

     

     Wannan tarihi da Abdullahi Fodiyo ya zo da shi, ya tabbata a citin littafan tarihi musamman littafin Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. 2 a shafi na 11-15.

    Taƙaitaccen Tarihin Abu-ubaida (RA)

     `Sayyidina Abu-ubaida ya kasance daga cikin sahabban Annabi SAW. Kuma yana daga cikin waɗanda Annabi SAW ya yi wa albishir da Aljanna. Abdullahi Fodiyo ya zo da shi a sahun waɗanda aka yi wa albishir a cikin jerin waɗanda ya kawo a waƙarsa. Ga dai abin da yake cewa:

    176.  Da Abu Ubaida Amiru suka ce mashi,

      Ɗa na ga Abdullahi shi ko bi nasa.

    177.  Sunan uwatai Ummu Gunmi can Badar,

      Yak kas ubansa da yag ga kafirta tasa.

    178.  Har anka jiɗas mai da ayat “La tajid”,

      Sura ta Ƙad Sami nan sabadda yabo nasa.

    179. Daga ta Uhudu da anka jefo Annabi,

      Bisa kwalkwali har yad dune ga jiki nasa.

    180. Shi yac cire ƙarfe ga Fuskat Annabi,

      Shi anka ce ma Amin ga al’umma tasa.

     Abudullahi Fodiyo ya zo da bayanin asali da jarumta da biyayya na Abu-ubaid. Haka kuma ya bayyana cewa, an saukar da aya a cikin suratul Ƙad Sami domin yabo ga Abu-ubaida. Wannan tarihi ya bayyana a cikin littattafan tarihi musamman idan aka duba Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. 2 a shafi na 24-28.

    Shirin Kammala Waƙar da Addu’a.

     Marubucin waƙar ya fara naɗe tabarmar wannan waƙa tun a baiti na 181 zuwa na 190, inda ya yi ta gudanar da addu’a. ga dai abin da yake cewa:

    181.  Allah Shi ba mu da mu da su yarda tasa,

      Kowanmu nai gurin shi samu gani nasa.

    182.  Allah Shi ba mu hawa mu zo can Makkata,

      Domin mu bauta gun bigen da ka haifa sa.

    183.  Mu biyo Safa har Marwa har wajjen Ƙudus,

      Da Abu Ƙubaisu har Hira da Mina tasa.

    ..........................................................................................................................

    190.  Gurinmu kenan Jalla bamu cika tasa,

      Tarshe mu can Firdausi Aljanna tasa.

    Addu’ar Rufewa

     Marubucin ya yi amfani da salon zamani wanda dukkan rubutacciyar waƙa ya dace ta hau, sai ya yi amfani da marufi ya rufe waƙarsa. Ga dai yadda ya rufe waƙar.

    191. Na gode Allah nai salati da sallama,

       Bisa Annabinmu da tarsashin allai nasa.

     Wannan ita ce hanyar da kowane marubucin waƙa ke amfani da ita wan rufe waƙarsa.

    Salo

     Salo wani ƙari ne na daraja a cikin karatu ko furuci wanda ba lalle ne a same shi cikin kowane rubutu ba. Ɗangambo (2007).

     Idan muka lura za mu fahimci cewa, salo dai dabara ce ta isar da saƙo a cikin sauƙi tare da jan hankalin mai sauraro ko rubutun abin da aka faɗa ko rubuta.

     Wannan waƙar ba ta ƙunshi wasu salailai masu yawa ba. amma ga ɗan abin da aka kalato daga waƙar.

    Salon Nassi

     Salon nassi salo ne in da mawaƙi ko marubu ci kan yi amfani da wani sashe da ke cikin Alƙur’ani ko Hadisin Manzon Allah (SWA), a cikin waƙarsa domin ya yi wa waƙarsa kwalliya ko ya ja hankalin mai saurare. A nan mai waƙar zai iya ya kawo wani bayani wanda Allah (SWA) ya faɗa a cikin Alƙur’ani ko kuma ya kawo wani bayani wanda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce. Waton abin da Hadisi ya zo da shi.

     A wannan waƙa ta “Siyar” Abdullahi Fodiyo ya yi amfani da irin wannan salo na nassi. Inda ya kawo wasu baituka da suka zo a cikin Alƙur’ani Mai girma da Hadissan Manzon Allah SAW. Ga dai wasu daga cikin waɗanda ya kawo:

    151.  Mai Hijirataini ta gun Habash da Madinatu,

      Ya amri biu ‘yan Annabi mata nasa.

    152.  Harda ta Alƙur’anu anka sanam masa,

       Yin Bai’atul Rilwanu Annabi yai masa.

     Wannan nassi ne, saboda abin da Abdullahi ya faɗa ya zo a cikin Alƙur’ani Mai girma a Suratul Baƙara aya ta 90-91.

     

     Bayan wannan ma akwai da yawa wuraren da ya yi bayani kuma abin ya zo a cikin Alƙur’ani Mai girma. Kamar bayanin yaƙi da aka yi da da Hijira, da shiga kogon hira da tarihin gidan Annabi SAW, sun zo a surori kamar Anfal,da Taubah, da Ahzab, da Tahrim da Baƙra da dai sauransu.

    Kamancen Fifiko

     Marubuci kan ɗauki abubuwa biyu ya nuna ɗaya ya fi ɗaya. Ana gane wannan kamance ta hanyar amfani da kalmomin fannu kamar ya fi, ko ɗara, tsere ma da dai makamantansu. Ga yadda Malam Abdullahi ya kawo nasa misalin a wannan waƙa cikin baiti na 2,57 da 58.

    2. Shi yaf fiyas tas duk ga tahlikkai nasa,

      Shi yag gabatas duk ga Manzanni nasa.

     A wannan baitin idan aka lura da kalmomin da aka ja ma layi za a fahimci suna nuna fifikon Annabi a kan Tahlikai. Haka kuma a ɗangon ƙasa akwai nuna fifikon Annabi SAW a kan Manzanni.

    Saɓi Zarce

     Wannan wani nau’in salo ne da mawaƙa/marubuta ke amfani da shi a cikin waƙa. Ana gane wannan salon a cikin baiti. Wato tsakanin ɗango da ɗango. Abdullahin Fodiyo ya yi amfani da irin wannan nau’in salo. Kuma wannan ya zo a cikin baiti na 7,8,9,10,11, da 13,14, da ,17, da 19, da 21. Misali.

    17. Bab na Ɗalibu don shaƙiƙi na ga Ab-

      Dullahi dud da fa Atiku gwaggo nasa.

     Wannan baitin yana da salon saɓi zarce musamman idan aka lura da abin da ya faru a wannan baiti. An fara faɗar sunan Abdullahi a ɗango na farko can da ƙarshen gaɓa, sai aka ƙarasa a farkon ɗango na biyu.

    Salon Gangara

     Wannan nau’in salo ne wanda ya ƙunshi yadda marubuci/mawaƙi zai faro zance a wani baiti ya ƙarasa a shi a wane baiti. Irin wannan salon Abdullahi ya yi amfani da shi a baiti na 7-11. Misali.

    7. Shi ɗa ga Abdullahi Abdulmuɗɗalib,

      Ɗan Hashimi, Abdulmunafi uba nasa.

     .....................................................................................................

    11. Sannan uwa tai Amina ‘ya wahhabu

      Abdulmunafi ɗan Kilabu ka gam masa.

    Salon Kirari

     Wannan wani nau’in salo ne da marubuta suke amfani da shi wajen jan hankalin masu sauraro. Abdullahin Fodiyo ya yi amfani da wannan salo. Ga abin da yake cewa.

    61.  Shi Zarubi na ba shi jiuya gaba nasa,

      Ga wurin faɗa ko zarumawa sun gusa.

    Lalurar Waƙa

     Wannan wani tsari ne da marubici kan tsinci kansa a ciki, a madadin ya faɗi kalma yadda ya dace da nahawunta sai ya gutsure ta, ko ya sauya ta domin ta dace da karin da ya yi amfani da shi. A wannan waƙa an ci karo da irin wannan lalura a baiti na 77,82,91,105.

    77.  Kibiya kwari nai an ka jefa rijiya,

      Taɓ ɓuɓɓugo da ruwanta don barka tasa.

     Wannan kalma da aka ja wa layi kalma ce da ke nufin “Albarka” amma lalurar waƙa ta sa an gutsure ta ta koma “barka”

    Salon Aron Kalma

     Aron kalma wani nau’in salo ne da marubuta/mawaƙa ke amfani da shi domin jan hankalin mai sauraro. Ana yin aron kalma daga wani harshe daban ko dai larabci, ko Turanci, ko Fulatanci da dai sauran harsuna. Abdullahi ya yi amfani da wannan nau’in salo ya aro kalmomin Larabci da yawa ya gina wannan waƙa. An samu wannan salo a baiti na 12, 91, 104, da sauransu.

    12.  Ran Attanin biyu dagga Gani ga Shekara,

      Koran Sahabul fili Makka ka haifa sa.

    ...............................................................................................................

    Zubi da Tsarin Waƙar Siyar ta Abdullahi Fodiyo

     Kalmomi biyu ne suka haɗu suka bayar da “zubi da tsari” wato “Zubi” da kuma “Tsari”. Waɗannan kalmomi kowace da ma’anarta. Misali.

    Zubi: Wannan ya ƙunshi yadda marubuci ya zuba baitocin waƙarsa.

    Tsari: Shi kuma ya ƙnshi yadda aka tsara ƙafiya, ko ɗangon waƙar.

     Da wannan zan iya cewa, Abdullahi Fodiyo ya zuba waƙarsa bisa ga baituka 191. Kuma ya tsara ɗangayensa bisa ga tsari na ‘yar tagwai/ƙwar biyu. Inda ya yi amfani da gaɓar “sa” a ƙarshen kowane baiti.

    Mabuɗin Waƙar

     Mawallafin wannan waƙar ya fara buɗe waƙarsa da godiya ga Allah. Ga dai yadda yake cewa:

    1. “Na gode Sarki Jalla don rahama tasa,

      Na yo salati ga Annabi Manzo nasa.”

     Wannan tana ɗai daga cikin hanyoyin da mafi yawan marubuta waƙoƙi suke amfani da ita.

    Marufin Waƙar

     Marubucin ya yi amfani da salon zamani wanda dukkan rubutacciyar waƙa ya dace ta hau, sai ya yi amfani da marufi ya rufe waƙarsa. Ga dai yadda ya rufe waƙar.

    191.  Na gode Allah nai salati da sallama,

       Bisa Annabinmu da tarsashin allai nasa.

     Wannan ita ce hanyar da kowane marubucin waƙa ke amfani da ita wan rufe waƙarsa.

    Amsa- Amo (Ƙafiya)

    Amsa-amo wanda a nazarin waƙoƙin Larabci aka sani da ‘ƙafiya’ shi ne sautin (gaɓar) ƙarshen kowane ɗango. Shi wannan ya kasu kashi biyu: amsa-amon waje da amsa-amon ciki ko kuma babban amsa-amo da ƙaramin amsa-amo. Amsa Amo ya kasu gida biyu wato babba da ƙarami.

    Babban amsa-amo: Shi ne sautin ƙarshe na gaɓar kalmar ƙarshe na ɗangon ƙarshe a kowane baiti. Shi wannan a koyaushe bai cika canjawa ba, ga ƙa’ida. (Ɗangambo 2007: 31).

     Abdullahi ya yi amfani da amsa-amo gaɓa na “sa”.Idan aka duba waɗannan misalai za a fahimci haka. Misali.

    181.  Allah Shi ba mu da mu da su yarda tasa,

      Kowanmu nai gurin shi samu gani nasa.

    182.  Allah Shi ba mu hawa mu zo can Makkata,

      Domin mu bauta gun bigen da ka haifa sa.

    183.  Mu biyo Safa har Marwa har wajjen Ƙudus,

      Da Abu Ƙubaisu har Hira da Mina tasa.

     Duk gaɓar da aka yi wa layi a ƙasa tana nufin ita ce babban amsa-amo.

    Ƙaranin amsa-amo: Shi ne sautin gaɓa ƙarshe na kalmar ƙarshe na ɗango ko ɗangayen da suka zo kafin na ƙarshe. Idan waƙa mai ƙwar biyu ce shi ne sautin gaɓar ƙarshe na ɗangon farko, idan kuma mai ƙwar uku ce to shi ne ɗango na farko da na biyu, in kuma mai ƙwar huɗu ce, ɗanwaye uku na farko, idan kuwa muhammasa ce ɗangwaye huɗu na farko. Wannan amsa-amo shi yana iya canjawa a kowane baiti, amma kuma wani lokaci a kowane baiti yana iya zama bai ɗaya.(Ɗangambo 2007: 31)

     Wannan Waƙa ta Abdullahi Fodiyo tana da Amsa-amon iri biyu. Akwai babba da kuma ƙarami. Babban amsa-amon shi ne “sa”, kuma ba ya canzawa. Haka kuma tana da ƙarami na ciki wanda yana canzawa. Misali:

    173. Ɗan Aufu shi ne Abidur Rahmani sa,

      Shi cikinsu na ga Kilabu ko kaka gam masa.

    174  Shaffa’u ko ita ce uwa tai taz zamo,

      ‘Yar Abdu Aufu goggo ta ga uba nasa.

     Idan an lura za a fahimci cewa amsa-amon yana sauyawa daga baiti zuwa baiti misali abin da ya faru a baiti na 173 da na 174.

    Karin Waƙar Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi)

     Kari wani tsari ne da aka aro shi daga Larabawa. A wannan waƙar an yi amfani da karin Rajaz. Wato inda ƙafa ta shida take maimaita kanta. Wato Mustaf’ilun-Mustaf’ilun. Misali a waƙar.

    37. Sammai shina/ shiwɗe su har/Al’arshi har,

      Yas sami jin/ salla cikin/ foro nasa.

     Idan aka lura za a fahimci karin ya hau daidai ƙafa ta shida wato Mustaf’ilun-Mustaf’ilun.

    Kammalawa.

      A cikin kalen nazarce-nazarcen da aka yi dangane da abin da ya shafi rubutacciyar waƙa. An zo da bayani dangane da ma’anar waƙa. Da muhimmancin waƙa, da tarihin marubucin waƙar, da salsalar waƙar. An gano cewa a kowane rubutu na wannan ɓangare, jigo shi ne ƙashin bayansa. A ɗan nazarin da aka yi a wannan waƙar wadda Abdullahi Fodiyo ya rubuta mai suna “Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi” an gano cewa babban jigon waƙar shi ne Tarihi. Muƙalar ta ƙara da gajerce jigon waƙar da warware jigon. An kuma kafa hujjoji da baitukan waƙar dangane da abin da marubucin ya faɗa a waƙar. Haka kuma an danganta abin da ya faɗa da wasu littattafai na Musulunci da suka tabbatar da abin da ya faɗa a waƙar, hasali ma littattafan ne ya ɗauka ya waƙe su don al’umma su fahimci abin da ke cikin littattafan cikin sauƙi. An yi tsokaci dangane da zubi da tsarin waƙa da amsa-amon waƙar, da salailan kamar na Nassi, da Aron Kalma, da saɓi Zarce, da Gangara, da Kamance. An zo da Mabuɗi da Marufin Waƙar.

    Manazarta

    Abduljabbar, U. (No Date),Khulasatul Nurul Yaƙin 1. Don ‘Yan Makarantar  Firamare. Jizi’i na 1.

    Abduljabbar, U. (No Date),Khulasatul Nurul Yaƙin 2.Don ‘Yan Makarantar  Firamare. Jizi’i na 2.

    Abdulwahab, M. (2003), Mukhtasar Siratul Rasul Sallallahu Alaihi Wasallam.  Madina: Jam’itaul Islamiyya Press.

    Al’ashir, A (No date), Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. Jizi’i na 1

    Al’ashir, A (No date), Murshidu Ɗullab Ila Ma’arifatus Sahaba. Jizi’i na 2

    Bunguɗu H.U. da Maikwari H.U (2016) Waƙa Zancen Hikima. Gusau: Nasara Printing Press.

    CNCH, (2006), ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Zaria: Ahmad Bello Uniɓersity Press

    Ɗangambo A. (2007), Ɗorayar GadonFeɗe waƙa, (Sabon Tsari) Zariya, Amana   Publishers Limited.

    Ɗangambo A. (1981) Ɗaurayar gadon feɗe waƙa, SHN BUK, Kano

    Ɗanjuma, S. (1982) Rabe-raben waƙoƙin Hausa da Tasirinsu ga Rayuwar  Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company

    Idris Y (2010), Waƙoƙin Addini Na Siyasa: Nazarin Waƙoƙin Emmanuel Wise Mai Molo, Kundin Digiri Na Biyu. Sashen harsunan Najeriya da Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

    Idris Y (2013) Falsafar Zaman duniya a cikin wakar Duniya ta Yusuf Kantu: Zauren Waka vol 1 No 1 p189, Sokoto.

    Khuduri, M. (2003), Nurul Yaƙin. Labanon: Darul Fiƙra Perss. 

    Sarɓi S. A. (2007), Nazarin Waƙar Hausa, Samarib Publishers Kano.

    Sa’id, B. (1978) “Gudummuwar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa”,  kundin digiri na biyu a Sashen koyar da harsnan Nieriya na  jami’ar Bayero, Kano.

    Yahya, A. B. (1995), Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo Cikin Nazarin  Waƙa. In  Studies in Hausa Language Literature and Culture, (The  Fift Hausa International  Confrence) (e.d) Bichi A. Y Kafin Hausa,  A.U. and Yalwa L. D. (2002)

    Ratayen Waƙar Siyar (Tarihin Kyawawan Ɗabi’un Annabi) Ta Abdullahi Fodiyo.

    1. “Na gode Sarki Jalla don rahama tasa,

      Na yo salati ga Annabi Manzo nasa.

    2. Shi yaf fiyas tas duk ga tahlikkai nasa,

      Shi yag gabatas duk ga Manzanni nasa.

    3. Na sallama bisa alu har da sahabatu,

      Na sallama bisa kullihin mai bi nasa.

    4. Sannan mu tsara Siyar na Annabi Ɗahiri,

      Don masu bege nai su ƙaru da so nasa.

    5.  Mu ƙidai mahaifa nai zumai da riƙo nasa,

      Da hari da yaƙi nai kaza da sifa tasa

    6.  Mu ƙidayi goma waɗanda yay yi ma albishir,

      Haka masu bauta mai da marbuta nasa.

    7. Shi ɗa ga Abdullahi Abdulmuɗɗalib,

      Ɗan Hashimi, Abdulmunafi uba nasa.

    8. Shi ko Ƙusayyu Kilabu Marratu Ka’abu ɗa,

      Ga Luwayyu Galibu Firhu maƙuraisha tasa.

    9. Ɗan Maliki ɗan Nalaru ɗa ga Kinanatu,

      Ɗa gun Huzaimatu ɗa ga Madrikatu ka sa.

    10. Iliyasu ɗan Mulari Nizami Mu’addi ɗan,

      Adnana nan garai tsayin sihha tasa.

    11. Sunan Uwa tai Amina ‘yar Wahhabu,

      Abdulmunafi ɗan Kilabu ka gam masa.

    12. Ran Attanin biyu dagga Gani ga Shekara,

      Koran Sahabul fili Makka ka haifa sa.

    13. Ya tsotsi nono gun Suwaibatu ta zamo,

      Ta sam ɗiyauci barkacin reno nasa.

    14. Ai ɗanta Masruhu da Hamzatu sunka sha,

      Da uba na Salmatu don suna wari nasa.

    15. Sannan fa Sa’adiyya Halimatu tar riƙa,

      Tab ba shi nono har sa’ar yaye nasa.

    16. Rasuwar ‘uba nai biyu garai ya kai fuɗu,

      Au ya wuce rasuwar uwa ta riska ta.

    17. Bab na Ɗalibu don shaƙiƙi na ga Ab-

      Dullahi dud da fa Atiku gwaggo nasa.

    18. Tun Annabinmu shina maraye an tsarai,

      Aiki ɓata tun cana anka aminta sa.

    19. Sha biyu garai da ƙanen uba nai yan nufo,

      Tafiya da shi Sham nan Bahira yag ga sa.

    20. A gari na Busra yat tuna shi da yag gano,

      Dutsi itace na sujuda gu nasa.

    21. Yak kama hannu nai da yac ce wanga nan,

      Allahu yaz zaɓai ga tahlikkai nasa.

    22. Yac ce ma ammi nai ka maisai ni ina,

      Shakka Yahudu da yin mugunta gu nasa.

    23.  Ya kai biyat bisa shekara ishirina yai,

      Amren Hadijatu don tana mai so nasa.

    24. Sun haifi Ƙasimu yay yi biu ɗai yar rasu,

      Bayansa sun sam Zainabu ƙanwa tasa.

    25. Ta amri ɗan ƙanwah Hadijatu Halatu,

      Shi a’ Abdul Asi Rabi’u uba nasa.

    26. Sun sam Umamatu wadda Annabi ya’ aza,

      Ga wuya shina salla fa don rahama tasa.

    27. Tag girma tai amren Aliyu uban Hasan,

      Bayan fa yakumbonta Faɗima ta gusa.

    28. Mai bi ma Zainabu ko Ruƙayyatu ta ku san,

      Ta amri Usmanu da an ka mayas masa.

    29. Bayan fa ta rasu, Ummul Kulsumi na’am,

      Ƙanwa ga Faɗima yad daɗo nuri nasa.

    30. Kun san Aliyu shi ka amren Faɗima,

      Sunsam Hasan da Husaini muhusinu bisa sa.

    31. Haka Zainabu da uwa ta Kaltumi Umar,

      Ya amri wannan don shi sam nasaba tasa.

    32. ‘Ya’yan Hadijatu su waɗanda biyat don ku san,

      Duka haihuwassu tana gaban aiki nasa.

    33. Ya haifi Abdullahi Ɗahiru, Ɗayyibu,

      Da Hadija nan ga sa’a ta manzanci nasa.

    34. Duka shidda ɗan ɗiyansa na da Hadijatu,

      Ibrahi ɗan sa makuliya tah haifa sa.

    35. Loto da yac cika arba’in aka aika sa,

      Yaɗ ƙare ɗai da rabi aka aika sa.

    36. Da Buraƙa yah hau ta ‘isa har Sham da shi,

      A cikin dare ɗai nan ga Sham aka hausa sa.

    37. Sammai shina shiwɗe su har Al’arshi har,

      Yas sami jin salla cikin foro nasa.

    38. Ya yo kiran addin ga dangogi nasa,

      Wasu sun ƙiya Lansaru sun karɓa masa.

    39. Hijiram Musulmi Makka ta yi Madinata,

      Daga Annabi sai Bubakar ka jira nasa

    40. Su goma sha ɗai az zumai ga uba nasa,

      Gada Hamza Abbas sunka samu biya tasa.

    41. Su az Zaubairu Liraru Harisu Jahlu sai,

      Da Muƙawwimu da uba na Ɗalibu bisa sa.

    42. Ƙusamu abi Lahabi da Abdul Ka’abati,

      ‘ya’ya na Harisu zay yawa mabiya nasa.

    43.  Na Zubairu Abdullahi ya musulunta nan,

      Yas sam shahada ran Hunaini gaba nasa.

    44.  Matansa Ummu Hakam gami da Luba’atu,

      Suwa sun ka sam shiriya da karɓa kira nasa.

    45.  Baba na Ɗalibu ce Aliyu da Ja’afaru

      Da Aƙilu Ummu Tihami sunka abuta sa.

    46.  A cikin na Abbas goma Abdullahi shi,

      Da Ƙusum da Falalu sunka sam dini nasa.

    47.  Da guda ta Hamza Umamatu ta Abu lahab,

      Durrum mu’attabu Utbu sun karɓa masa.

    48.  Ya iske shidda ga goggiraɓe Safiyatu,

      Ta sami imanci cikinsu da so nasa.

    49.  Amma fa Arwa nan cikinsu da Atikah,

      Biyuɗin ga imancinsu an fa riwaita sa.

    50.  Ai ɗanta Abdullahi ya musulunta shi,

      Da Ɗulaibu ɗan Arwa Badar ƙabri nasa.

    51.  Gwaggonsa Baila ta ƙiya haka Barratu,

      Da Umaimatu duk sun ƙi bin sunna tasa.

    52.  Baila’u ko ta haifi Arwa nan uwa,

      Usumanu Annabi yaz zamo kawu nasa.

    53.  Abdul Asad ya amri Barratu taz zamo,

      Ta haifi Abdullahi wanda ka ce masa.

    54.  Baba na Salmata a’ uba da munka ce,

      Abdul Asad Mahazumu ad dangi nasa.

    55.  Ga ɗayan Umayyatu kun ji Abdullahi shi,

      Yas sami tuba Uhudu nan ƙabri nasa.

    56.  Da uwam musulmi Zainabu haka Hannatu,

      Da Habibatu sun sam sahabbanci nasa.

    57.  Kyawon Fiyayye ya wuce a sifanta sa,

      A mu yo kwatamci nan kaɗan don so nasa.

    58.  Haskensa ya gota ma rana, kyan ido,

      Kuma ag garai da tsawon wuya gashi nasa.

    59.  Bai duƙu tsab shike mai tsakaitaccen tsayi,

      Ƙamshin jikinsa na wardi na, kumya tasa.

    60.  Halinsa mai kyawo fa bashi sifantuwa,

      Mu taɓa kaɗan don masu son koyi nasa.

    61.  Shi Zarubi na ba shi jiuya gaba nasa,

    Ga wurin faɗa ko zarumawa sun gusa.

    62.  Kyauta garai, kyautassa ba ta misaltuwa,

      Bai ce a’a ko babu in anka roƙa sa.

    63.  Kumya gare shi da hankurin komi idan,

      Bai zam na saɓo ba shi motsa fushi nasa.

    64.  Baƙo shina daidai gare shi da ɗan gida

      Mai arziki bai gota moro gu nasa.

    65.  Tsabta garai ko da ga wajjen cimaka,

      Daga mai zuma shika so da kyaukyawa tasa.

    66.  Amma shina cin wanda ba daɗi idan,

      Ya zam halal don ba shi zaɓen ci nasa.

    67.  Hakanan tufa bai tara mai kyawo kaɗai,

      Ɗumki shikai da fiton tufansa da kai nasa.

    68.  Da yawa shina bauta ma kansa shi gai da mai,

      Ciwo shi zo gun wanda yay yi kira nasa.

    69.  Ya hau dawaki alfadarai raƙuma,

      Jakai shikan aza wasu ko baya nasa.

    70.  Da yawa shikan tafi babu takalmi nasa,

      Wata ran shi sa su wata ran shi hau bisa.

    71.  Mai yin bananci na shi kau faɗi gaskiya,

      Sarki na duniya shi daɗai bai tsorta sa.

    72.  Uzuri shi ka wa ‘yan Adam bisa ya sano,

      Hali shina ƙyale su don rahama tasa.

    73.  Alfatima farce na dama na ƙyauye na,

      Shika sa ta dud da na hauni shi sunna tasa.

    74.  Mai murmushi na lokacin gamuwa da shi,

      Halinsa yin shiu, sai zikir himma tasa.

    75.  Kuma mu’ujiza tai ta wuce haddin ƙida,

      Ƙur’anu ya isu mu’ujiza aiki nasa.

    76.  Mashi biyat da baka biyat garki ɗaya,

      Haka nan takubba goma an ka ƙidai masa.

    77.  Kibiya kwari nai an ka jefa rijiya,

      Taɓ ɓuɓɓugo da ruwanta don barka tasa.

    78.  Sanda mashaci Shantali duka ya yi su,

      Da matsokaci da siwaku almakashi nasa.

    79.  Ishirina har da bakwai zuwan yaƙi nasa,

      Ya aiki sau hamsin harin maƙiya nasa.

    80.  Ya shekara sha ukku Makkata duk shina,

      Manzo sa’annan ya nufo hijira tasa.

    81.  Ta Madina shi da Abubakar sai Amiru,

      Su am Musulmi ɗan Uraiƙidu ƙad asa.

    82.  Rasuwar Hadijatu dud da baban Ɗalibu,

      Bayanta goma ga shekara aike nasa.

    83.  Sannan Fiyayye yay yi amren Saudatu,

      ‘Yaz zamatu nan Makka yai biko nasa.

    84.  Ga ta gomaɗin nan yay yi amren A’ishah,

      Ku ji shidda shekarrunta raɗ ɗamri nasa.

    85.  Ya zo Madina gida na Halidu yash shiga,

      Har anka gyra wurin sala da gida nasa.

    86.  Yam mai da Zaidu da baba Rafi’u sunka zo,

      Ɗauka ‘iyali nai gami da ɗiya tasa.

    87.  Siddiƙu Abdullahi ɗansa da Ɗalhatu,

      Su sunka kawo raƙuma ta gida nasa.

    88.  Da isa Madinatu yay yi bikon A’ishatu,

      Haka ɗan Salamun nana imanci nasa.

    89.  Nan anka gyara sallarmu tak koma fuɗu,

      Yaf fori muminai jiyayya don nasa

    90. Salmanu ya musulunta Abdullahi ko,

      Ya yo mafalki an kirai salla tasa.

    91.  Ga ta biu ga hijira anka jirkita ƙiblatu,

      A cikinta ko Ramalana anka farlata sa.

    92.  A cikinta kono yaw wajabta, Ruƙayyatu,

      Nan taw wuce dagab Badar sa’a tasa.

    93.  Amren Aliyu da Faɗimah nan yay yi ya-,

      Ƙin Ƙainiƙa’a da idi sa lahaya tasa.

    94.  Ga ta ukku yai amre na Hafsatu ‘yar Umar,

      Don abida ta mai biyas Sunna tasa.

    95.  Ƙauran Naliru faɗa na Uhudu cikinta na,

      Nan anka haifi Hasan, haramta giya tasa.

    96.  Sannan Fiyayye yay yi amren Zainabu,

      Ce, ‘yar Huzaimah wata takwas ɗai tag gusa.

    97.  Ya shekara ta fuɗu yay yi amren Hindu ‘yar,

      Baban Umayyata ɗan Mugiratu ce masa.

    98.  Ɗan Amru Abdullahi ɗan Mahazumu ce,

      Ɗan Yaƙazatu ɗan Marratu na gamo nasa.

    99.  Nan anka haifi Hussaini an ce nan giya,

      Daɗa tah haramtaNaliru nan ƙaura tasa.

    100.  Nan ɗan Ruƙayyatuyaw wuce da uwar Alu,

      Baba na Salmatunan sa’ar rasuwa tasa.

    101.  Ta biyat ga hijira tai Madina Ubangiji,

      Yaɗ ɗamra amre nai da ‘yar goggo nasa.

    102.  Ita Zainabu ‘yar Jahashu bayan ta fito,

      Gun Zaidu yaro nai ɗiyautacce nasa.

    103.  Nan anka yo fama da Dauma da Hanɗaƙu,

      Da Ƙuraizatu da ta Masɗalaƙ nan A’isa.

    104.  Tas samu barra anka kama Juwairiya,

      Tas sam ɗiyauci nan da yin amre nasa.

    105.  A cikinta Hajji yaf faralta da shamakin,

      Mata, tayammamu nan garat jiɗa tasa.

    106.  Ga ta shidda yai roƙon ruwa da gudummuwa,

      Yaƙi na gaba Huɗaibiyya bai’a tasa.

    107.  Tuba ta Dausi sa da jiɗaƙ Ƙad Sami,

      Hukuncin muharibbai garat jiɗa tasa.

    108.  A cikinta ya aika zuwa ga sarakuna,

      Su shidda sashe sun ka karɓi kira nasa.

    109.  Ya aiki Dihiyyatu cana wajjen Ƙaisara,

      Ya kasa tuba don biyar dangi nasa.

    110. An kai takarda tai ga Kisara don shi bi,

      Yar ridda yak kece ta anka ruɓusta sa.

    111.  Ya aiki Haɗibu gun Muƙai ƙisu bai bi ba,

      Ya ba da sirrin Mariya jizya tasa.

    112.  Ya sa su Shuja’u su zo ga Harisu cana Sham,

      Bai tuba ya ƙi biye shi sam shiriya tasa.

    113.  Ya sa Saluɗu shi zo Yamamu ga Hauzatu,

      Ya ce idan bai sam rabi ba bai bi nasa.

    114.  Ta bakwai yai amren Habibatu ‘yar Abu,

      Safiyanu Abdu Munafi nan gamuwa tasa.

    115.  Usumanu yaɗ ɗamre shi cana shi ne Habash,

      Biko sadaki nai Najashi yay yi sa.

    116.  Can Haibara nan anka kana Safiyyatu,

      Ya bar ta ya amre ta don rahma tasa.

    117.  Ya amri cana zuwansa Makka na Umratu,

      Maimunatu ƙarshe na yin amre nasa.

    118.  Ta takwas ga Hijira Amru Asi da Khalidu,

      Usmanu Ɗalhatu sun shigo dini nasa.

    119.  Nan Zaidu, Ja’afaru dud da ɗan Affanu nan,

      Suka sam shahada hari na Mu’utatu don nasa.

    120.  Sannan fa yai yaƙi na Makka da Ɗa’ifa,

      Da Hunaini Ibrahimu nan aka haifa sa.

    121.  Da Abu Kuhafatu su Abu Sufiyanu nan,

      Suka sulmi Uzza nan risɓewa tasa.

    122.  Yaƙin Tabuka zuwa Haji na Abubakar,

      Sannan Li’an ta tara ga yin Hijira tasa.

    123.  Nan Ummu Kulsumi ɗiya tai tar rasu,

      Hakanan Najashi Mumini ma so nasa.

    124. Yaka ɗan Ubayyu nan Fiyayye yai fushi,

      Ƙimar wata bai zo begen mata tasa.

    125.  Ga ta goma ɗa nai yaw wuce Ibrahi nan,

      Yaz zo shi Hajji nan cikin dini nasa.

    126  Sha ɗai ga Hijira Gani yaj ji jiki nasa,

      Ran Attanin sha biu garai ƙaura tasa.

    127.  Allah Shi dawwama sallama da salati na-

      Na garai shi ba mu ganin sa don barka tasa.

    128.  Zaidun Ubayyu da Amiru da Mu’awiya,

      Kulafa’u su fuɗu kun ji marubuta nasa.

    129.  Asma’u Hindu Anas Rabi’atu su ka bau-

      Tamai Bilalu shina kiran salla tasa.

    130.  Mariƙi na takalminsa ɗan Masa’udu na,

      Mai jan bisa tai Uƙubatu mai so nasa.

    131.  Ku ji goma zaɓaɓɓu da yaw wa albishir,

      Babbansu Abdullahi as sunan nasa.

    132.  Shi a’ Abubakari Abu na Ƙuhafatu,

      Tsohonsa na Usumanu ko aka ce masa.

    133.  Ɗan Amiru Ɗan Amru Ka’aba da Sa’adu ce,

      Ɗan Taimu ce Ɗan Marratu magana tasa.

    134.  Salma uwa ta ga Abubakar ta silmi kau,

      ‘Yar Saharatu kakansa ɗai da uba nasa.

    135.  Shi ya rigsi gaskata Annabi yar ragai,

      Kowa ga tanyo tsai da addini nasa.

    136.  Shi yar rigai kowa bayassa cikin sala,

      Shi yar ragai tanyon masallaci nasa.

    137.  Ya bada Jumlad dukiya tai don biɗa,

      Yarda ta Allah anka ko karɓa masa.

    138.  Wat tanyi Annabi yin zaman kogon hira,

      Sai shi da Allah yaf faɗo suhuba tasa.

    139.  Sanna Umaru Faruƙu ɗan Haɗɗabi ɗa,

      Ga Nufailu shi ko Abdu Uzza bi nasa

    140.  Ga Rahabu Abdullahi Garɗo Razahu ɗa,

      Ga Adiyyu Ka’abu Luwayyu nan gamuwa tasa.

    141.  Sannan uwaf Faruƙu Hannatu Hashimu,

      Yah haifa ta Mahazumu ad dangi nasa.

    142.  Ranad da yam Musulunta addin fai-da-fai,

      Aka yin sa bayan can ana ɓoyo nasa.

    143.  Jama’am Musulmi sun yi murna kafirai,

      Sun tsorta don ƙarfi da zarumci nasa.

    144.  Can radda Uthatu yat tarai domin faɗa,

      Yak kada Uthatu yah haye ga ciki nasa.

    145.  Zaki na Annabi Hamza ko hakana shike,

      In ya yi rura kafirai su ruƙurƙusa.

    146.  Tambai Abujahalin da yag gilma masa,

      Yash sha shi gora nan ga kai yat tartsa masa.

    147.  Shaiɗanu ko inwat Umar tsoro shi kai,

      Bai yarda dacewa da shi hanya tasa.

    148.  Biyuɗin ga su na at takubban Annabi,

      Kwat tashi gilma mai su kaste wuya nasa.

    149.  Hatta Mala’iku fa sun yi farin ciki,

      Ranad da yam musulunta don himma tasa.

    150.  Sanna ka ce Usmanu ɗan Affanu ɗan,

      Asi Umayyatu Abdu Shamsi ka gam masa.

    151.  Mai Hijirataini ta gun Habash da Madinatu,

      Ya amri biu ‘yan Annabi mata nasa.

    152.  Harda ta Alƙur’anu anka sanam masa,

       Yin Bai’atul Rilwanu Annabi yai masa.

    153.  Kyauta garai mai yawa da kumya mai yawa,

      Hatta Mala’ikku suna kumya tasa.

    154.  Sanna Aliyu ubansa farda na uwa,

      Tasa Faɗima kakanta ɗai da uba nasa.

    155.  Shi an na farko yara duk ga musulumtaka,

      Mabiyi na Annabi na sa’ah Hijira tasa.

    156.  Was samu auren Faɗima face shiya,

      Wah haifi ɗa tamka Hasan da zumu nasa.

    157.  Ba tamkacinsa cikin maza ranaf faɗa,

      Ɗan Abdu Wodi ya tarai ya kai ƙasa.

    158.  Can Haibara ƙyauren garin nan yac cire,

      Yai garkuwa ta faɗansa don ƙarfi nasa.

    159.  Ƙarfi da yaji an sano su gare shi duk,

      Dangi na Hashimu babu mai woba tasa.

    160.  Baicinsa Ɗalhatu ɗan Ubaidullahi ɗan.

      Usmanu wanda Abubakar shike ɗa nasa.

    161.  Ce Saudatu ‘yar Hadrani tah haife sa,

      Ranah Hunainu ga judu anka ɗafanta sa.

    162.  An ce da shi ran Uhudu Khairu Tabuka ko,

      Fayyadu duk laƙanin ga Annabi yai masa.

     163.  Bai kau ba ranar Uhudu yab bar Annabi,

      Halbi da fama ɗai shikai a gaba nasa.

    164.  Da Zubairu ɗa ga Awamu ɗa ga Khuwailidu,

      Baban Khadijatu gun Ƙusayyu gamo nasa.

    165.  Yannan uwassa Safiyya goggon Annabi,

      Shi yar rigai kowa haminya don nasa.

    166.  Shi anka ba tuta ga fatahu kaza Badar,

      Shi Annabi yac ce farantacce nasa.

    167.  Ya gadi ƙarfi dud da zarumci jihat,

      Kawunsa Hamza kaza jiha ta uba nasa.

    168.  Baicinsa sai Sa’adu ɗan Abu-waƙƙasi shi,

      Ɗan Maliki ga Kilabu nan gamuwa tasa.

    169.  Ɗa ko ga Annabi shi uwa tai Hannatu,

      Ai ‘yar Abu Sufuyanu nan kaka gam masa.

    170.  shi yar riga kowa ga halbawa sabad-

      Da Jihadi Rabi’u tanbaya ka sanm masa.

    171.  Biɗi sabiƙina ka sa shi Zaidu ubansa kau,

      Tun jahiliyya yay yi imanci nasa.

    172.  Sanna Sa’idu na Zaidu Amru Nufailu ce,

      Kakan Umar shi a’ uban kaka nasa.

    173.  Ɗan Aufu shi ne Abidur Rahmani sa,

      Shi cikinsu na ga Kilabu ko kaka gam masa.

    174.  Shaffa’u ko ita ce uwa tai taz zamo,

      ‘Yar Abdu Aufu goggo ta ga uba nasa.

    175.  Rawaninsa Annabi yan naɗa mishi shi ga kai,

      Ga Tabuka kau yas sa shi limanci nasa.

    176.  Da Abu Ubaida Amiru suka ce mashi,

      Ɗa na ga Abdullahi shi ko bi nasa.

    177.  Sunan uwatai Ummu Gunmi can Badar,

      Yak kas ubansa da yag ga kafirta tasa.

    178.  Har anka jiɗas mai da ayat “La tajid”,

      Sura ta Ƙad Sami nan sabadda yabo nasa.

    179.  Daga ta Uhudu da anka jefo Annabi,

      Bisa kwalkwali har yad dune ga jiki nasa.

    180.  Shi yac cire ƙarfe ga Fuskat Annabi,

       Shi anka ce ma Amin ga al’umma tasa.

    181.  Allah Shi ba mu da mu da su yarda tasa,

      Kowanmu nai gurin shi samu gani nasa.

    182.  Allah Shi ba mu hawa mu zo can Makkata,

      Domin mu bauta gun bigen da ka haifa sa.

    183.  Mu biyo Safa har Marwa har wajjen Ƙudus,

      Da Abu Ƙubaisu har Hira da Mina tasa.

    184.  Mu biyo ta Arfa kaza wurairan Hajji duk,

      Mu gano Madinatu can garin Hijira tasa.

    185.  Hanyarmu kenan har mu shuɗe can Ƙuba,

      Har Raula cana cikim masallaci nasa.

    186.  Mu ziyarci Ƙubba tai da shi da Abubakar,

      Da Umar mu yo roƙo mu sam ceto nasa.

    187.  Mu shigo kufaifan ɗakunasa mu yawata,

      Mu biyo ta Uhudu ga Hamza Basambo nasa.

    188.  Sannan mu zo mu Baƙi’u can ga sahabatu,

      Sanna Iraƙ ga Aliyyu don mu ziyartasa.

    189.  Sanna mu zo ga Annabawa cana Sham,

      Mu ziyarci kowa don biɗar barka tasa.

    190.  Gurinmu kenan Jalla bamu cika tasa,

      Tarshe mu can Firdausi Aljanna tasa.

    191.  Na gode Allah nai salati da sallama,

      Bisa Annabinmu da tarsashin allai nasa.

     Tammat bihamdillahi wa husni aunihi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.