Nason Wasu Al’adun Hausawa a Littafin Malam Inkuntum

    Bayanin takarda: Haruna Umar Maikwari da Muhammad Chibaɗo Aminu, (2021). Nason Wasu Al’adun Hausawa A Littafin Malam Inkuntum. Maƙala da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani da jami’ar jihar Kaduna ta shirya a kan wasan kwaikwayo da finafinai a ƙarƙashin gudanarwar sashen nazarin harsunan Nijeriya. A ranar 3 zuwa 5 ga Disamba, 2021.

    Nason Wasu Al’adun Hausawa a Littafin Malam Inkuntum

    Daga

    Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

     Tsakure

    Wasan kwaikwayo mai taken “Malam Inkuntum” an shirya shi ne domin raha. Wannan wasa ta fito da wasu al’adun Hausa na malanta. Duk da cewa an saka raha da yawa a ciki, wannan ba ya nuna cewa duk abin da aka zo da shi ciki yana aukuwa a zahiri. Maƙalar tana da manufar fito da wasu al’adun Hausawa da suka bayyana a cikin wannan wasa. Haka kuma a bayyana irin muhimmancin da ke tattare da waɗannan al’adu. Hanyoyin da aka bi wajen gina wannan maƙala kuma sun haɗa da; Karance karancen bugaggun littattafai da kundaye da mujallu na ilimi daga wasu jami’o’i. Sakamakon da wannan maƙalar ta fito da shi kuma shi ne an gano akwai wasu al’adun Hausawa da suka bayyana cikin wannan wasar kamar dai Aure, ɗaurin aure, auren sadaka, yi wa mace toshi, yi wa mace huɗuba da jan kunne, Imani da ƙwanƙwamai, sarauta, sarautar shantali, gaisuwar sarauta sauke baƙo da sauransu.

    1.0 Gabatarwa

     Al’ada aba ce da ta shafi dukkan ɓangarorin rayuwar al’umma. Wannan ne ya sa kalmar ‘al’ada’ ta daɗe tana jan ra’ayin masana da manazarta da dama. Asalin kalmar al’ada ba Bahaushiya ba ce aro ta aka yi. Kuma an are ta daga harshen Larabci. Tana nufin abin da aka saba yi a Larabce. Duk da cewa akwai kininta a harshen Hausa.[1] Akwai rubuce-rubucen ilimi da bincike-bincike da aka gudanar a matakan ilimi daban-daban game da al’adun Hausawa. Masana da manazarta sun yi ƙoƙarin ba da ma’anar wannan kalma. A cewar Ibrahim (1982: iii) “al’ada” tana nufin: “abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya”. ɗangambo, (1987:5) cewa ya yi: “Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” Bunza, (2006:7) na da irin wannan ra’ayi inda yake cewa: “Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa.” Idan aka duba waɗannan ma’anoni da ma wasu da dama makamantansu, za a tarar da cewa, al’ada dai na nufin hanyar rayuwar al’umma ta gaba ɗaya. Wannan kuwa ya haɗa da zamantakewa da tattalin arziki da kiyon lafiya da dukkannin abin da ya shafi rayuwar al’umma.

    Dangane da ma’anar kalmar wasan kwaikwayo kuwa, za a iya cewa manazarta irinsu Ogunbiyi (1981) da ‘Yar’adua (2008) da Yahaya da ɗangambo(2004) duk sun kawo ma’anar wasan kwaikwayo a siga daban-daban. Wasan kwaikwayo yana nufin nau’ine na wasa da yake ɗauke da koyi,ko tsarin zamantakewar mutane ta yin amfani da ‘yan wasa da lokaci na musamman (Ogunbiyi,1981:3).

     Muhimman Kalmomi: Naso, Al’ada, Wasan Kwaikwayo,

    1.1 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

     An zaɓi hanyoyi biyu don gudanar da wannan maƙala Hanyoyin da aka bi wajen tattara muhimman bayanai domin aiwatar da wannan maƙala sun haɗa da tattaunawa da ma’abuta ilimi da kuma karatun littattafai domin samun nasarar aiwatar da wanna maƙala. An samu karanta littafin nan na wasan kwaikwayo mai suna “Malam Inkumtum”. Karanta wannan littafin shi zai ba da damar ganin abin dan da ake son a fito da shi daga cikinsa. Da yake manufar wannan muƙala shi ne a fito da wasu al’adu da aka ci karo da su a cikin littafin na “Malam Inkuntum”.

    1.2 Al’adun Hausawa

     Rayuwar al’umma a kammale ita ake kira da al’ada, wato dai ɗungurungum na abin da ya shafi rayuwa da mu’amalarsu ta yau da kullum. Saboda haka, al’adar Hausawa ta shafi duk wani abu da ake gani (Tufa ko abinci da makamantansu) ko wanda ba a gani (kunya, tarbiyya da makamantansu) wanda za a iya danganta su da Hausawa. Kenan dai, al’ada aba ce da akan san wata al’umma da ita. Akan gane wannan al’umma da irin al’adarta.

    Masana al’ada da zamantakewar al’umma (Anthropologist) sun bayyana cewa, an samu ma’anar al’ada tun a ƙarni na sha tara (Ƙ19). Misali a littafin Edward Burnett Tylor (1871) Primitive Culture(Al’adun Jahiliyya) a sakin layin farko yana cewa: “Al’ada ita ce duk wani abu da ya ƙunshi ilmi, da addini, da sana’o’i, da ɗabi’u, da dokoki, tsarin rayuwa da duk wata halayya da mutum ya koya a matsayinsa na ɗan wata al’umma. Haka kuma Tylor (1881) ya ƙara da cewa al’ada ta shafi ɗan Adam ne kawai saɓanin dabbobi”.

    Wasu masanan zamantakewar al’umma (Anthropologist) wato Kroeber da Clyde Kluckhohn, (1952) sun ciro ma’anonin al’ada kimanin (164) kuma ma’anonin akasarin su sun tafi a kan cewa, al’ada koyar ta ake yi ba halitta ba ce.[2]

    Masana da manazarta da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dagane da al’ada. Misali. Bargery, (1934: 16) ya ba da ma’anar kalmar kamar haka: “Tada ko ɗabi’a ko hanya ko haila wato fashin salla ko jini ko bin wata ko wanki.” Abraham, (1962: 17) ya bayyana al’ada da “ aure, da buki da haila (al’adar mata) da magana da ciwon kai wanda aka saba da yi, ya kuma ce an al’adantai. Peil, (1977) ta bayyana cewa, “Al’ada ta ƙunshi abinda mutum ya tashi da shi na rayuwa, kuma ita al’ada koyonta ake yi ba halitta ce ba. Ta ƙara da cewa, al’ada ba ta canzawa a cikin ƙanƙanin lokaci, amma koma idan daɗe takan sauya ko ma ta mutu.”

    Shi kuwa Ibrahim, (1982: iii) ya ce al’ada na nufin: “Abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Ta haka al’ada ta shafi yanayin rayuwar al’umma da harkokin da take gudanarwa na yau da kullum.” Shi kuwa ɗangambo, (1987:5) cewa ya yi: “Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” A cewar Bunza, (2006:7) ‘’Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan’Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. CNHN (2006:9) an bayyana al’ada da: “(i) hanyar rayuwar al’umma (ii) jinin haila (iii) wani hali na daban na mutum (iv) magani ko tsafi”. A Sa’id, da wasu (2006: 9) an bayyana ma’anar al’ada da: “Hanyar rayuwar al’umma ko jinin haila ko magani ko tsafi ko wani irin hali daban na mutum.” Shi ma Gusau, (2010: 2) ya yi nuni da cewa, al’ada ta ƙunshi dukkan ɓangarorin rayuwar ɗan Adam. Ya ce:

    “Al’ada ta ƙunshi tafarki wanda wata al’umma take rayuwa a cikinsa dangane da yanayin abinci da tufafi da muhalli da rayuwar aure da haihuwa da mutuwa da wasu hulɗoɗin rayuwa kamar maƙwabtaka da sana’o’i da kasuwanci da shugabanci da bukukuwa da sauran abubuwa waɗanda suke da alaƙa da haka.” Gusau, (2010: 2)

    A gudummuwa irin wannan za a iya cewa, al’ada wata hanya ce ta tafiyar da rayuwar dukkan halittu da suke a doron ƙasa, kuma wannan hanyar ta kasance ana tu’ammali da ita lokaci zuwa lokaci na rayuwar wannan halitta.

    Na zaɓi halitta ne domin na lura ba mutane kaɗai ne suke da al’adu ba, hatta ma dabbobi da ƙwari kowa da irin tasa hanyar gudanar da rayuwa kuma da yadda yake aiwatar da tsarin rayuwarsa, kama daga kuka, da nema, da cin abinci da tanadi ga masu yin tanadi da sadarwa tsakanin su da wasu da dai makamantan su.

    1.3 Littafin Malam Inkuntum

     Littafin wasan kwaikwayo mai suna “Malam Inkuntum”, littafi ne da yake da shafuka 41. An tsara wannan littafi a bisa ga tsari na rabo-rabo. Wato rabo na farko zuwa rabo bakwai. Kowane rabo yana da kanun batu da aka yi. Littafin an rubuta shi ne bisa jigon malanta a ƙasar Hausa.

    1.4 Nason Al’adun Hausawa a Littafin Malam Inkuntum

     Al’adun Hausawa sun kasance abin tinƙaho gare su. Hausawa na son su musamman ma sun zame masu wasu hanyoyi da suke amfani da su domin koyar da halaye na gari. Wannan ya sa a cikin dukkan sha’anoninsu na rayuwa ba su barin al’adun sai sun bijiro da su. Marubucin littafin “Malam Inkuntum” ya kasance mai amfani da tsohon salon rubutu, kuma a yunƙurinsa na isar da saƙon da ke tattare da wannan wasa ya bijiro da al’adu waɗanda sun keɓanta ga Hausawa. Akwai al’adun aure da kuma gaisuwa da sarautu da imani da iskoki da kuma kyautata wa baƙo.

    1.4.1 Auren Sadaka

     Wannan auren an fi yinsa a ƙauye kuma a wancan zamani na dauri. Ana ɗaura wa yarinya aure a kai ta gidan miji ba tare da ya sani ba ko ya nemi warin zamanta.

     Irin wannan aure wanda yake da ɗiya kuma yake da ƙudurin yin sadaka da ita, sai ya zauna da iyayenta da duk wani mai haƙƙi ya gaya masu cewa zai yi sadaka da wance, cewa da ɗiyarsa za su amsa masa, sai ya yi shawarar wanda zai ba. Yana iya barin abin a zuciyarsa kuma yana iya kallon hankalin yariyar da kuma kiyon hankalinta tare da duba hankalin wanda yake neman ya haɗa su da shi.

     A wancan lokaci idan za a yi sadaka da mace, akan duba a gani cikin masu hulɗa ta nema da ita wa ta fi so? Ko a nemi wani almajiri wato mai neman ilimi wanda aka san cewa, zai iya zama da mata cikin koyarwa ta shari’a tare da bin dokokin al’adun Hausawa, sai a ɗaura aure uban yarinya ya biya sadaki ya yi komai ya kaita gidan mijin da zai ba sadaka ba tare da wanda za a ba matar ya san cewa shi za a kai ma ba.

     A littafin wasan kwaikwayo mai suna “Malam Inkintum” wannan al’adar ta auren sadaka ta bayyana a shafi na 6 zuwa 7. Misali.

    BAMAGUJE: Towo! Ai ka san ban san Larabci ba, yi mini Hausa. Kai ni tafowa na yi da ɗiyata “Yarkudunu in gwada ma ita don a ba yaron nan ɗan babban malamin nan da ya mutu ita aure. Sadaka ko na ba shi.

    LIMAN: (yana murmushi, ya ga yarinya daƙwalwa guda kyakkyawa). To, to madalla abu ya yi, watau ka riga ka faɗa masa, ko tukuna?

    BAMAGUJE: Ban faɗa masa ba, amma dai si na yi niyya.

    LIMAN: To Allah ya amsa.

    BAMAGUJE: Allah ya amshi me? So ka ke ta mutu halama?

    LIMAN: A’aha wai sadakar da ka yi na ce Allah shi sanar maka.

    BAMAGUJE: Kai ni ban iya salalan nan naku ba. Ladan dai ya karɓa.

     Wannan ya nuna cewa an zo da al’adar auren sadaka a ciki duk kuwa da cewa Bamaguje ne ya zo zai bayar da aure. Wannan ya nuna cewa ba addini kaɗai ba hatta ma al’adar Hausawa ta aminta da yin auren sadaka.

     1.4.1.1 Haɗuwa da Mace Kafin Aure

     Ga al’ada ana haɗu tsakanin namiji da mace a wurare daban-daban. Wannan ya danganta da inda aka haɗu. Ana iya haɗuwa a kasuwa ko gidan buki ko asibiti ko dandali, ko wani muhalli na daban. A wasan “Malam Inkuntum” an nuna inda Malam Inkuntum ya haɗu da Asabe har ma suka daidaita maganar aure. Ga dai yadda abin ya gudana a shafi na 11. Misali.

    HALIMA: “Yar na ki je ki sayo muna taba a kasuwa mana.

    ASABE: Kai ni na gaji da tafiye-tafiyen nan tun dai ba zuwa kasuwa ba.

    HALIMA: Saunar wofi – irin lalacin da ya hana ki bazawari kenan – im ba ki fita ana ganinki ba, wa zai san da ke ma a garin nan.

    ASABE: To iya ba ni in tafi – amma dai uhm- (kuka ke nan).

    HALIMA: Af – to mene ne na kuka kuma?

    MAISHELA: to, ga Asabe can ta ci ado ta nufi kasuwa ta sayo ma Halima taba. Ga Ladan can ya hange ta har ta tafi wujenta.

    LADAN: Aham, aham, (Asabe ta waigo)

    LADAN: Ina son mu gana da ke.

    ASABE: sabon yaushe?

    LADAN: Ai ɗai rana ake sabo. Ina dai son mu gana da ke. Ga gidana can

    1.4.1.2 Yi wa Mace Toshi (Yin Kyauta ga Wadda Ake Nema)

     Al’adar Hausawa ta yadda da wanda ke neman mace ya yi mata kyauta. Babu shakka wannan kyauta na ƙara danƙon soyayya tsakanin masoya. Yi ma mace toshi ba sabon al’amari ba ne. kuma yin kyautar shi ke nuna akwai ƙauna tsakanin namiji da mace. Wannan yana daga al’adar Hausawa. A littafin wasan kwaikwaton “Malam Inkuntum” an bijiro da irin wannan al’ada a shafi na 13. Misali.

    LIMAN: (ya zabura ya shiga gida ya fito da goro da kuɗI da turare) Ga ɗan goro kya ci hure. (Asabe ta karɓa a haɓar zane ta tashi) sai na aiko ɗaurin aure – amma sai an gama na yaran nan tukuna, kin ji?

    ASABE: Ji kai, sai an jima (Ta zunɗI Liman ta tafi abinta)

    1.4.1.3 ɗaurin Aure

    Aure alaƙa ce ta halaccin zama tsakanin miji da mata. An yin sa ne domin shi aure sunna ce ta Annabi Muhammadu Rasulullahi (S.A.W.) domin tsarkake zuri’a. Aure muhimmin abu ne ga al’umma saboda haka akwai hanyoyi da matakai na tabbatar da shi. Mataki na farko shi ne neman aure. Aure wata yarjejniya ce a tsakanin namiji da mace da kuma bin wasu ƙaidoji da dokoki da wannan alumma ta tanada domin samun zuria ta gari (Magaji, 1999).

     A Musulunci kuwa aure na nufin wani ƙuduri tsakanin namiji da waliyyansa da sadaki da kuma shaida. Amma a cewar wani masani mai suna Habib Alhassan da wasu Aure yana nufin wata yarjejeniya ta zama tare tsakanin namiji da mace bisa ga wani tsari na addinin ko alada.

     Shi kuwa ɗaurin aure, ana tara al’umma ne su shaida cewa an aurar da wance ga wane bisa wasu sharuɗɗa. Addini da al’ada duk sun yadda da aure. Haka kuma akwai wasu abubuwa da suke tattare ga ɗaurin aure kuma sai waɗannan abubuwan sun kammala sannan za a yi auren. Wasan kwaikwayon nan mai suna “Malam Inkuntum” an zo da ɗaurin aure a shafi na 15. Misali.

    MAISHELA: Sai kuma aka yi ta dariya ana kallonsu aka watse daga wasa. Ga liman can ya shirya goro da kuɗI don a ɗauro masa aure da Asabe. Ga mutane nan masu zuwa ɗaurin aure, amma Ladan shi ne uban tafiya.

    LIMAN: To ku sanya ɗana Ladan gaba – shi ne uban tafiya. Kai ko Ladan ko me ka yi na yarda. Misalin sadaki ba.

    LADAN: To jama’a kada ku yi mamaki. Ni za a ɗaura wa aure da Asabe, ba da Liman ba.

    MALAM SULE: Me za a yi?

    LADAN: Ni za a ɗaura wa aure ba Liman ba. Amma a tambayo ta wanda ta yarda a ɗaura da shi.s

    1.4.2 Huɗuba da Jan Kunnen Amarya

     Al’adar Hausa ta yi tanadin duk lokacin da aka kai amarya a gidan mijinta, to a yi mata huɗuba wato a gaya mata halayyar zaman aure da kuma abubuwan da ya dace ta yi. Galibi a wancan lokaci kafin a kai mace a ɗakin aurenta akan koya mata dukkan al’adun zaman aure. Idan kuma an kai ta za a ƙara jaddada mata. A littafin wasan kwaikwayon “Malam Inkuntum” an zo da wannan al’adar a shafi na 7. Misali.

    TSOHUWA: Salamu alaikum ɗan Malam.

    LADAN: Maraba, abin ko Ladan ba a cewa?

    TSOHUWA: To ga abin da Bamaguje ya ce a kawoma, mata ce ka riƙa da amana.

    LADAN: (Ladan baki buɗe yana dariya) Madalla, madalla, na gode, Allah Ya gode.

    TSOHUWA: To, a yi zaman girma da arziki ‘Yarkudunu. Hura mai kyau, tuwo mai kyau, ki ci sai kin yi kat.

    1.4.3 Imani da Ƙwanƙwamai (Iskoki)

     Bahaushe ya yi imani da iskoki. An yi lokacin da yake bautawa iskoki. Wannan kuma ko shakka babu al’ada ce tsintsa. Tsafi ya samu ne ga al’ummar Hausawa sanadiyyar buƙatun rayuwa na kariya da magani da biyan wasu buƙatoci na rayuwa. Wannan buƙata ita ta haifar da tsafi da magani da kuma ma su magani. Waɗannan buƙatoci suna nan har yanzu a cikin zukatan mutane. Misali: mutane na buƙatar kariya ga gidajensu da gonakinsu shi ya sa suke da tsafi na kafi a gida ko gona ta yarda wani mugu ko ɓata gari ba zai sami damar shiga ya yi masu ɓarna ba ko ya cutar da su. Haka ma ta fuskar biyan buƙatoci na rayuwa, Hausawa kan yi amfani da magani domin neman farin jini ko kwarjini a wajen neman aure ko a sana’ar da suke gudanarwa don su sami karɓuwa a cikin al’umma. Wasan kwaikwayon “Malam Inkuntum” an samu wanna al’ada a shafi na 9. Misali.

    LIMAN: Bari dai ai wata rana kuwatawa zai yi, don zan sakam masa ƙwanƙwamai in same ki daga ni sai iska. (sai ya yi kwance)

    1.4.4 Sarauta a Littafin Malam Inkuntum

    Sarauta wani tsari ne shugabanci da ake gudanarwa a tsakanin jama’a da manufar kyautata rayuwarsu. Sarauta wani yunƙuri ne na yin sulhu tsakanin jama’a domin kyautata zamantakewarsu da kula da haƙƙoƙinsu. Wato sarauta dai wani tsari ne na shugabanci da al’ada ta shimfiɗa wanda aka gada kakanni da iyaye.

     Wasu kuma suna ganin cewa sarauta wani salon jagoranci ne wanda akan nuna kwarjini da dabaru ko hikimomi daban-daban domin mulkin jama’a da nufin samar da zaman lafiya tsakaninsu. Sarki kuwa wani mutum ne da akan naɗa domin ya jagoranci wani rukuni na al’umma.

    1.4.4.1 Sarautar Shantali

     A gargajiyance akwai sarautar shantali. Wannan sarauta dai wani ake naɗawa kuma babban aikinsa shi ne riƙa wa sarki shantali. Shi kuma shantali wani makayin ruwa ne da aka yi shi da laka kuma aka yi shi daidai da riƙon mutum. Babban aikin wannan makayin shi ne a zuba ruwa a cikinsa don amfani kamar dai tsalki (ɗahara) da alwala da wasu ayyukan ibada da za a iya yi da ruwa kwatankwacin wanda wannan shantali ke ɗauka. Wanda aka naɗa sarautar shantalin kuma babban aikinsa shi ne riƙe wannan shantalin don amfanin sarki. A wasan “Malam Inkuntum” an nuna akwai wannan sarautar a shafi na 22. Misali.

    LADAN: Shantali - ɗauki shantalina ka riƙa in na ratse in taɓa ruwa.

    SHANTALI: (Ya ɗauko shantali). Ga shi.

    LADAN: Wuce mu tafi zagi – kai kuwa Shantali komo nan daura da ni ka taya ni riƙon tasbaha.

    1.4.4.2 Gaisuwar Sarauta

     A al’adun Hausawa komai yana da bagirensa, kuma komai yana da tsari. Sarauta tana da irin nata tsari kuma ta bambanta da tsarin talakawa. Don haka duk abin da aka ce na sarauta ne, yana da bambanci da wanda ba na sarauta ba. Gaisuwa dai wani sashe ne na al’ada daga cikin sassan al’adu. A wasan Malam Inkuntum, an samu irin wannan al’ada a shafi na 26. Misali.

    GATARI: Ran sarki ya daɗI, ai da gani babu tambaya.

    MALAM INKUNTUM: Lafiya ran sarki ya daɗe

    1.4.5 Sauke Baƙo

     Kalmar “baƙo” takan ɗauki ma’anoni daban daban ga yadda Bahaushe ke kallonta da sarrafa ta. Fitacciyar ma’anarta ita ce, “wani mutun da ya fito daga wata nahiya, ko ƙasa, ko jiha, ko gunduma, ko gari, ko unguwa, ko gida zuwa wani wuri wanda ba nasa ba, da niyar zama ko yada zango, ko wata lalura ta daban.” (Bunza 1991:2)

     Akwai bayani a kan baƙunci kuma wanta za mu iya cewa kusan duk abu ɗaya ne, saboda kalmar “baƙunci” ta samu ne daga kalmar “baƙo” bayan da aka yi mata gyaran goshi kamar dai yadda masana ilmin harsuna suka fayyace, (Bunza:1991:2) a cikin (Rufa’i, 1982). Wanda duk Bahaushe ke kira “baƙo” a kan ma’anar farko da aka bayar, to halin da yake ciki a wurin da ya sauka to shi ne baƙunci.

     Hausawa na da al’adar sauke baƙo da karrama shi da kuma tsare mutuncinsa. A wasan Malam Inkuntum wannan al’adar ta bayyana a shafi na 27,32,34 da 39 kamar dai yadda za a gani.

    SARKI: A faɗa wa sarkin gida a kai masa shimfiɗa da abinci da kome da kome wanda ya kamata. Shafi na 27

    SARKI: To Jakada a tafi a saukad da malam inda aka saba, yadda aka saba.

    Shafi na 32.

    Wannan yana nuna irin halin sauke baƙo da Hausawa kan yi.

    1.4.5.1 Karrama Baƙo

     Hausawa na karrama baƙo, ta hanyar ba shi abinci da abin sha da guzuri in zai koma. Haka kuma dukkan tsawo zamansa a muhallin Hausawa ba su bari ya tozarta, ko wani ya tozarta shi. Irin wannan lamari ya bayyana cikin litafin wasan kwaikwayo na “Malam Inkuntum” a shafi na 27. Misali.

    SARKI: A faɗa wa Sarkin gida a kai masa shimfiɗa da abinci da komai da komai wanda ya kamata.

    SARKIN GIDA: Gafara Malam, ga abin da Sarki ya ce a kawo maka sauka.

    MALAM INKUNTUM: Madalla! Madalla! In jin tuwon shinkafa ne?

    SARKIN GIDA: Ai nan acca muke ci, sai shanana da mai.

     A wancan lokaci idan Bahaushe ya yi baƙo yakan sa a yi masa abinci na musamman. To a al’adar Hausawa gidan sarki koyaushe ba a rasa abinci na marmari. Baƙon sarki wato malam Inkuntum, a nasa tunani tuwon shinkafa. A zamanin daka rubuta wannan wasan tuwon shinkafa babban abin marmari ne. Sai sarkin gida ya gaya masa ce ai tuwon ma da yake tsammani wanda aka kawo masa ya fi shi.

     Baya ga tarbon baƙo da karrama shi akwai tsare mutuncin baƙo wanda al’ada ta tanadi a tsare masa mutuncinsa. Don haka wannan wasa na “Malam Inkuntum” ya zo da irin wannan al’ada a shafi na 34. Misali:

    MAGAJI: Ai sai a sa dogarai a tsare kowace hanya mai fita garin nan. Can masaukinsa a sa dogarai su tare don in an ga zai gudu a kamo shi.

    SARKI: Kamu! Haba Magaji! Yaya mutum zai ci amanar baƙonsa? Na yarda a sa a tsare, amma indai har ya fita da niyyar gudu, kada su taɓa shi, kada kuma su ce masa komai. Su dai ga inda ya nufa, su zo su ba mu labari.

    FADAWA: Haka nan ne. Haka shi ne daidai ranka da daɗe.

    1.5 Kammalawa.

     Wannan wasa ta fito da wasu al’adun Hausawa na gargajiya. Tun asali Hausawa suna da tsarin rayuwa wanda shi ne al’adunsu. Wannan kuma ba za a yi mamaki ba don al’adun al’umma sun bayyana a adabinsu. Dama dai al’ada ita ce dukkan rayuwwar ɗan Adam. Wasan kwaikwayo na “Malam Inkuntum” yana isara da saƙon raha ne koma an zaɓi jigon malanta a ƙasar Hausa aka isar da shi a cikin raha. Wani abu da aka zo da shi a ciki na raha wanda wani ke ganin in haka al’adar malanta take a ƙasar Hausa to akwai gyara, ba haka abin yake ba. Tabbas akwai malanta a ƙasar Hausa tun bayan samuwar addinin musulunci. Wani abu da ya zo don bayar da dariya wannan daban ne. Maƙalar ta gano wasu al’adu kamar dai abin da ya shafi aure kama daga ganin matar aure, toshi, ɗaurin aure, huɗuba wa amarya, kai ta ɗakin miji da sauransu. Haka kuma akwai sarauta da tsarin sarautu kamar Sarki, Sarki gida, Sarkin fada, shantali da gaisuwar sarauta sa sauransu. Akwai al’adar baƙunta da kuma yadda ake karrama baƙo da tsare masa mutuncinsa duk a wannan wasa.

    MANAZARTA

    Adamu, A. (2009). Rupert Moultrie East: Gudunmuwarsa Ga Adabin Hausa Da Kuma Sharhi Kan Ayyukansa. Kundin Digiri Na Uku. Kano: Jami’ar Bayero.

    Abbas, H. (2009). “Gudunmuwar Hukumar Wallafa Littattafai ta Arewacin Nijeriya Wajen Havaka Adabin Hausa. 1966-2006”. Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.

    Aliyu, S. I. (2007). Raha A Wasanin Ƙasimu Yaro: Tarken Wasannin Karanbana.

      Kundin Digiri Na Biyu. Zaria: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afrika. Jami’ar Ahmadu Bello.

    Abraham, R.C. (1977). Dictionary of the Hausa Language: London Sidney Auckland Toron: Hodder and Stoughton.

    Ahmad, U. (1985). Taxonomy of Hausa Drama. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    Auta, A.C. (2008). “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa a Ƙarni na Ashirin kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe Kano: Jami’ar Bayero.

    Auta, L.A. (2017). Faɗakarwa A Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Bayero University Press.

    Balbasatu, I. (2009). Gudunmuwar Mata Ga Haɓakar Rubutaccen Adabin Hausa. Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.

    Bargery, G.P. (1993). An English-Hausa Dictionary an English-Hausa Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    Bello, B.N. (2000). “Jirwaye Mai Kamar Wanka, Tura Ta Kai Bango a Sigar Wasan Kwaikwayo” Kundin Digiri na Farko, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Bugaje, H. (2005). Kishi a Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa. Kundin Digiri Na Farko, Zaria: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afrika. Jami’ar Ahmadu Bello.

    Bunza, M. S.(2009). Gudummuwar Shehu Jibrin Golovo Ga Bunqasar Wasan Kwaikwayon Raha A Hausa. Kundin Digiri Na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya. Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo.

    Bunza, U.A. (2014). Waiwaye Adon Tafiya: Faɗakarwa a cikin Ƙagaggun Labaran Hausa. In Harsunan Nijeriya Journal of Nigerian Languages and Folklore Vol. XXIV Bayero University Kano. ISSN: 1116-0691. Page 47-65.

    Bunza, U.A. (2015). Talife-Talifen Hausa a Zamanin Mulkin Mallaka: Yanayinsu da Sigoginsu. Kundin Digiri na Uku, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.

    Bunza, U.A. (2017). Ci Gaban Mai Ginar Rijiya: Nazarin Salailan Warwarar Cikin Litattafan Zuben Hausa. Takardar da aka Gabatar a Babban Xakin Taro na Tsangayar Fasaha Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Aduwa, ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba, 2017.

    Chorko, M. (1994). Yadda Wasan Kwaikwayon Hausa Ya Yi Tasiri a kan na Qabilar Marghi” Kundin Digiri na Farko, Maiduguri: Jami’ar Maiduguri.

    Dabai, L.M. (1991). “Kwatanta Tskanin Duniya Budurwar Wawa da Kulva Na Varna “kundin Digirin Farko, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya jami’ar Bayero.

    Diaomeng, S. (2004). “Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa A Rukunan Adabin Hausa: Havakarsa da Muhimmancinsa” Kundin Digiri na Biyu Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

    ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Kano: K.D.G. Publishers.

    Garba, R. (2009). Mace A Rutaccen Wasan Kwaikwayo. Misali Daga Umar Gulma Da Kulva Na Varna Harshe Journal of African Languages Department of Nigerian and African Languages Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria. ISSN 978-125-100.

    Haspelmath, M. (2008). Framework-Free Grammatical Theory. To appear in Heine (eds). the Oxford Handbook of Grammatical Analysis. Oxford: University Press.

    Ibrahim, F. (2010). ‘Nazarin Gina Halaye Nagari A Rubutattun Ƙagaggun Labarai na Gasar 1933 da ta 1980’ Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Jibril, A.S. (2010). “The Status of Women In Hausa Literature: A Focus on Hausa Plays”. Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Afrika. Jami’ar Ahmadu Bello.

    Khalis, M.I. (1995). Kwatancin Wasan Jatau Na Ƙyallu da Halayen Matan Hausawa”. Kundin Digiri na Farko, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Malumfashi, A.I.(1987). A Madadin Wasan Kwaikwayo. Takardar da aka Gabatar a taron qarawa juna ilimi na huxu a kan Harshe da Adabi da Al’adu. Kano:Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Malumfashi, A.I. (1990). Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa daga 1930-1990: Sharhi kan Matsayinsa”. Takardar da aka Gabatar a Bikin Cika Shekara 60 da Fara Rubuta Wasan Kwaikwayon Hausa Daga 1930-1990 a cikin Dandalin Harshe da Al’ada. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.

    Malumfashi,A.I.(2011). Yusuf Ladan; Jigon Wasan Kwaikwayon Hausa Na Rediyo, Harshe Journal of African Languages and Cultures Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria. ISSN 978-125-100.

    Malumfashi, A.I(2002).Sharhin Sharri A Kan Wasan Kwaikwayo.Takardar da aka Gabatar. Azare: Kwalejin Ilimi.

    Ogunbiyi, Y. (1981). Drama and Theatre in Nigeria. Lagos: Pitman press

    Shehu, I. (2005). Tasirin Harshe A Wasan Kwaikwayon Jami’ar Jatau Na-Albarkawa. ”. Kundin Digiri na Biyu, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello

    Sambo, A. (1990). “Sake Leƙa Rabe-Raben Wasannin Kwaikwayon Hausa”. Takardar da aka Gabatar a taron qara wa juna sani na Neman Babban Digiri Zaria. Sashen Harsunan Nijeriya da na Afirka. Jami’ar Ahmadu Bello.

    Xiomeng, S. (2013). Rubutaccen Wasan Kwaikwayo a Rukunin Adabin Hausa; Havakarsa da Muhimmancinsa. Kano: Gidan Dabino Publishers.

     ‘Yar-Aduwa, T.M. (2007). Wasan Kwaikwayo Na Hausa: Nau’o’insa Da Sigoginsa. Kano: Usman Al-amin Publishing Company.

    ‘Yar’adua, T.M. (2008). Nazarin Rubutattun Wasan Kwaikwayo: Jagoran Nazarin Wasu  Littattafan Wasan Kwaikwayo. Kano: Gidan



    [1] A duba Bunza (2006) Gadon Feɗe Al’ada. A shafi na XXV

    [2] A duba Encycolopedia na Britannica Macropedia mai lamba 16, a shafi na 874.                         

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.