Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Sadu Da Ni Kafin Na Yi Wankan Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum. Malam mene ne hukuncin mace ta ƙare haila ba ta yi wanka ba mijinta ya sadu da ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Maganar mafi yawan Malamai shine: Ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka fahimta a suratul Baƙara aya ta (222).

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.

Amma Abu-Hanifa yana ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da yankewar jinin haila kawai. Riƙo da mazhabar farko shine ya fi, saboda Allah ya kira haila da ƙazanta. Babu wata kaffara ga wanda ya sadu da matarsa kafin tayi wanka bayan yankewar jinin haila.

Allah ne mafi sani.

𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments