Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Sanar Da Mijina Cewa Na Yi Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mace ce take zina amma kuma tana da aure sai ta zo taji tsoron Allah ta tuba kuma tana tsoron sanar da mijinta kuma tana so ya yafe mata, yaya ya kamata tayi? Ko kuma duk da ta tuba ya zama mata dole ta mika kanta a jefe ta kamar yadda addini ya tanadar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh farko dai ya kamata ki gane cewa a ƙasar nan ba Shara'ar musulinci ake yi ba. Toh gurin wa zata miƙa kanta a jefe ta ɗin? Sannan kuma in ma shara'ar musulinci ɗin ake yi toh ai bai kamata ba shi kuma me lefi a shara'a in har ya tuba ba tare da an kamashi ba toh ba dole bane se ya miƙa kansa, Kawai inya inganta tubar tasa shikenan babu komai akansa.

Batun mijin ta kuma wannan tunda be sani ba to ka da ta gaya masa kawai ta nemi gafarar Allah kuma ta inganta tubar ta. Amma idan taso tana iya samun mijin nata a natse sai tace babansu wance ina roƙon ka dan Allah ka yafe min duka lefukan da nayi maka babba da ƙarami wanda nayi da gangan da wanda nayi cikin kuskure. Ko kuma kice baban wance nayi maka lefi amma kai baka san nayi ba, sedai ni nasan ban kyauta ba kuma in kai baka sani ba nasan Allah ya sani to kayi haƙuri ka yafe min insha Allahu ba zan ƙara ba. Kawai se kiyi abun a haka base kin fito kin bayyana abunda Allah ya rufa miki asiri ba, baya kamata ki tona ma kan ki asiri Allah baya so idan ya rufa ma bawa asiri se shi kuma bawan ya tona ma kansa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments