TAMBAYA (144)❓
Assalamu alaikum
Gaskiya tsoron Maza. Nake yi. Malam. Ko za asama min me
hankali. Da tausayi❓
AMSA❗
Waalaikumus salam, warahmatullahi, wabarakatuhu
Yar uwa, ina roqon Allah (Subhanahu wata'ala) ya azurta ki
da samun Miji nagari tare da sauran gwagware da tuzuran da suke a wannan gida
mai albarka. Kuma Ina roqon Allah yasa na zamo silar hada aure don a samu
wannan nutsuwar, son da rahamar da Mahaliccinmu ya ambata a cikin Qur'ani mai
girma
Allah Subhanahu wata'ala ya ce:
( وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ
أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ
فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ )
الروم (21) Ar-Room
Kuma akwai daga ayoyinsa, Ya halitta muku matan aure daga
kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku.
Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani.
Idan mai niyyar ba shi da wadata Allah zai azurta shi daga
inda ba ya zato Kamar yanda ya fada:
( وَأَنكِحُوا الْأَيَامَىٰ مِنكُمْ وَالصَّالِحِينَ
مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ ۚ إِن يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِن
فَضْلِهِ ۗ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ )
النور (32) An-Noor
Kuma ku aurar da gwauraye daga gare ku, da salihai daga bayinku,
da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadatar da su daga
falalarSa. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani.
Haka Kuma Allah Azzawajallah yace:
( وَاللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا
وَجَعَلَ لَكُم مِّنْ أَزْوَاجِكُم بَنِينَ وَحَفَدَةً وَرَزَقَكُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ
ۚ أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَتِ اللَّهِ هُمْ يَكْفُرُونَ
)
النحل (72) An-Nahl
Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma Ya
sanya muku daga matan aurenku ɗiya
da jĩkoki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa masu daɗi.
Shin fa, da ƙarya
suke yin ĩmani, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kafirta?
Kuma Mazinaci baya aure face da Mazinaciya Kamar yanda Allah
Azzawajallah yace:
( الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ
مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ ۚ وَحُرِّمَ
ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ )
النور (3) An-Noor
Mazinaci ba ya aure face da mazinaciya ko mushirika, kuma
mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci ko mushiriki. Kuma an haramta wannan
a kan mũminai.
Ibadar Aure lada ce Wanda ko da azumi idan kusanci iyalinka
zaka samu lada ne:
( أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ
إِلَىٰ نِسَائِكُمْ ۚ هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمْ وَأَنتُمْ لِبَاسٌ لَّهُنَّ ۗ
البقرة (187) Al-Baqara
An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga
matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su,
Niyyata ita ce na zama silar da a ranar lahira za'ace wa
Mata da Miji:
( ادْخُلُوا الْجَنَّةَ أَنتُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ
تُحْبَرُونَ )
الزخرف (70) Az-Zukhruf
Ku shiga Aljanna, kũ da matan aurenku, ana girmama ku.
Idan kai gwauro ne Kuma Allah to kayi haquri ka kame kanka
idan Allah ya baka dama sai ka nemi auren. Allah Azzawajallah yace:
( وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا
حَتَّىٰ يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ ۗ
النور (33) An-Noor
Kuma waɗannan
da ba su sami aure ba su kame kansu har Allah Ya wadatar da su daga, falalarsa.
Idan Kuma Allah ya qaddara bazakayi aure ba a duniya to kada
ka damu domin kuwa indai har ka bi Allah da sunnar Manzo Sallallahu alaihi
wasallam to zaka samu Hurul Ayn a Aljannah Kamar yanda Allah Azzawajallah ya
fada:
( وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌ
)
الصافات (48) As-Saaffaat
Kuma a wurinsu, akwai matan aure masu taƙaita
kallonsu, masu manyan
idanu.
Da Kuma ayar:
( وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ أَتْرَابٌ
)
ص (52) Saad
Kuma a wurinsu akwai matan aure masu gajarta ganinsu ga
mazansu, tsarar jũna.
Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) yace: an tambayi Manzon
Allah Sallallahu alaihi wasallam: Ya Rasulullah, wacce mata ce tafi ? Sai yace:
"Itace wadda idan ka kalleta zaka ji farin ciki, wadda take bin umarninka,
kuma bata saba maka akan haqqinka ko kuma dukiyarka akan abinda baka so"
(Sunan Ahmad: 2/251 Haka Kuma Al-Albany ya hassanashi a
cikin Al-Silsilah Al-Sahihah: 1838)
Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: Ana auren mace ne
don dukiyarta, kyawunta, nasabarta ko Kuma addininta. Sannan sai yace: Ina baku
shawara ku auri mai addini
(Bukhari: 5090 da Kuma Muslim: 1466)
Kamar haka yake Kuma ga namiji shima ya zamo mai addini.
Domin kuwa kudi, nasaba da kyau duk suna iya disashewa amman addini da shi za'a
tashi mutum
Imam al-Nawawy (Rahimahullah) yace: Ma'anar wannan hadisin
shine Annabi Sallallahu alaihi wasallam yana magana ne akan mutanen da suke
kallon wadannan abubuwan guda 4, Wanda na karshe shine addininta, don haka yana
qarfafa gwiwarsu akan addininta
(Sharh Muslim: 10/51-52 da Kuma Riyadis Salihin page na 454)
Son mace mai kudi, kyau ko nasaba abune da Allah ya halicci
mutum dashi don haka ba laifi bane idan namiji yace Yana son mace saboda
kyawunta ko dukiyaba saidai abinda aka fi so shine addininta da kyakkyawar
alaqarta da mutane kamar yanda Imam al-Qurtubi ya fada a cikin: Al-Mufhim lima
ashkala min Talkhis Sahih Muslim, 4/215
Muhallish shahid din dai shine a fara duba addininta idan
Kuma an same ta da kyau, dukiya da nasaba to wannan falala ce daga Falalar
Allah Azzawajallah
_Don Haka kamar Yanda Shari'ah ta sauqaqa cewar mutum zai
iya buqatar ganin wadda zai aura babu hijabi don ganin abinda zai kwantar masa
da hankali daga gareta_
Kamar Yanda Maaiki Sallallahu alaihi wasallam yabawa Sahabi
Al-Mugheerah ibn Shu’bah (Radiyallahu anhu) shawara a lokacin da ya nemi aure:
Annabi Sallallahu alaihi ya tambayesa shin ka ganta yace: A'a. Sai yace masa
kaje ka ganta, hakan zaisa so da qauna su shiga tsakanin ku
(Al-Daaraqutni, 3/252 (31, 32); Ibn Maajah, 1/574)
Haka Kuma zai iya ganin hotunanta idan hakan bazai haddasa
fitina ba
Sannan Kuma don ya tambayeta nasaba ko sana'arta shima ba
laifi bane ba
Kuma ba laifi bane idan mace ta nuna tana son namiji sabanin
yanda muka maidashi al'ada wai dole saidai namiji ne zai nemi auren mace. Ko
kun manta da cewar Nana Khadija (Radiyallahu anha) itace ta nuna buqatar auren
fiyayyen halitta Sallallahu alaihi wasallam
Ibn Munayyir (Rahimahullah) yace: Imam al-Bukhari ya fitarda
hukuncin halascin mace ta nemi auren namiji Wanda ta yarda da addininsa
Duba littafin Ibn Hajar al-Asqalani:
(Fath al-Bari: Vol. 9, page na 175)
A karshe: duk wadda take fatan samun Mijin Aure musamman a
cikin wannan group mai albarka na "TAMBAYA DA AMSA" kamar yanda
mutane dayawa sukemin maganar ta private to da akwai dokoki da qa'idoji don
tabbatuwar hakan
1️⃣A samu Saurayi da Budurwa (Ko
Kuma Zaurawa) wadanda zasuyi auren saboda Allah
2️⃣Iya karanta addu'ar Istikhara
don neman zabin Allah sannan Kuma su sanarda iyayensu/wakilansu
3️⃣Nesantar dukkan wasu abubuwa da
suka shafi Bidi'ah kamar irinsu Dauko Dj, yin Party da sauransu
4️⃣Yin walima bayan auren kamar
yanda addininmu ya tsara
5️⃣Hotunan Namiji/Mace guda 3. Sai
cikakken suna, Address da kuma Sana'a
A KULA:
Iya admins kadai za'a turawa bayanan
Muna roqon Allah ya duba manufarmu ya shiga al'amarin.
Sannan Nima a matsayina na wanda lokacin sa bai zo ba, a tayani da adduar samun
mace tagari: MAR'ATUS SALIHA wadda zamu Sha ZANJABEEL daga tafkin SALSABEEL da
yake a cikin ALJANNAH
( وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا
زَنجَبِيلًا )
الإنسان (17) Al-Insaan
Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin
gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
( عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلْسَبِيلًا
)
الإنسان (18) Al-Insaan
Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la ilaha illa
anta astaghfiruka wa'a'tubu ilayka
Amsawa:
Usman Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.