Ra'ayin Mairubutu: Digirin Girmamawa Ga Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Maradun
Na
Aliyu Ammani
Duk sadda na saurari waƙoƙin marigayi Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo na ji yadda ya baje kolin hikima da baiwar da Allah Ya yi masa, na kan tambayi kaina 'wai shin me yasa jami'o'in mu na Arewa musamman Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato suka gaza wajen bai wa wannan Bawan Allah digirin girmamawa?' Na ambato Jami'ar Usmanu Danfodiyo ne musamman saboda ita ce Ɗanƙwairo ya fito daga 'kaciman eriyarta'.
Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria cikin jihar Kaduna ta bai wa
Alhaji Mamman Shata Katsina, wanda ya fito daga 'imidiyet kaciman eriyarta'
(Katsina dake tsohuwar jihar Kaduna a lokacin) digirin girmamawa tun yana raye.
Jami'ar Jos dake jihar Filato ta bai wa Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos digirin
girmamawa tun yana raye. Amma Alhaji Musa Ɗanƙwairo bai samu ba a lokacin rayuwarsa,
bai kuma samu ba har zuwa yau shekara 33 bayan rayuwarsa!
Shekarun baya na taɓa
yin irin wannan ƙorafin, sai wani uztazu ya ankarar dani cewa bai kamata
jami'ar da aka jingina sunanta da Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo ta girmama
mawaƙi
ɗan bidi'a ba! Amma
tunda kasancewar waƙoƙin baka na Hausa "bidi'a" bai hana sashen nazarin
harsuna na jami'ar nazarin waƙoƙin baka da mawaƙan Hausa suka yi ba (da
bada digirori ga ɗalibai
manazarta), ashe bai kamata ya hana baiwa mawaƙan baka na Hausa (da ake nazarin waƙoƙin
nasu a samu digiri harda digirgir) digirin girmamawa ba!
Na ɗan
yi safiyon nazarce-nazarcen da masana daga jami'o'i suka yi akan waƙoƙin
Marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.
Na ga anyi rubuce-rubucen neman digiri tun daga na farko har
zuwa matakin digirin digirgir kan waƙoƙin Ɗanƙwairo.
An wallafa littatafai da maƙaloli kan waƙoƙin Ɗanƙwairo.
Mutane da dama sun samu digirori harda digirgir kan nazarin waƙoƙin Ɗanƙwairo.
A jami'o'i da dama akwai Dakta-Dakta da Farfesoshi da suka taka likkafar waƙoƙin Ɗanƙwairo
wajen kaiwa ga matsayin da suke kai a yau. Ko a ƴan shekarun nan Jami'ar Bayero dake Kano
ta shirya kwanfarans sukutun-da-guda, inda manazarta suka maida hankali kacokan
kan waƙoƙin Ɗanƙwairo.
Me ya sa jami'o'i masu sashen nazarin harshen Hausa ba za su
yi dubi zuwa ga yiwuwar bada digirin girmamawa ga Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Maradun ba? Wani yace wai in mutum ya wuce shekara 8 da rasuwa bai cancanci a
bashi digirin girmamawa ba. In na fahimci wannan bawan Allah da masu tunani
irin nashi, watau suna nufin duk wanda ya wuce shekara 8 da rasuwa duk wata
gudunmawar da ya bada lokacin rayuwarsa ta tashi a tutar babu kenan?
Maganar da ake yanzu haka, akwai wani na kusa dani dake
bincike da rubutun kundin samun digirin digirgir a kan nazarin waƙoƙin Ɗanƙwairo.
Hasali ma, sauraron rikodin ɗin
tsoffin shirye-shiryen 'Kundin Mawaƙan Hausa' na Rediyon Nijeriya Kaduna
(wanda manazarcin ya tanada ya kuma bani na kwafe 😉)
inda Maigirma Ɗanmadamin Birnin Magaji yayi fashin baƙi kan waƙoƙin
Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Maradun, shi ya zaburar da wannan rubutun. Shima kansa Maigirma Ɗanmadamin
Birnin Magaji yayi irin wannan ƙorafin a cikin shirye-shiryen.
Ina fatan manyan manazarta harshen Hausa a jami'o'in mu na
Arewa, musamman Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato da ta Bayero dake Kano
zasu duba yiwuwar bijiro da batun bai wa wannan bawan Allah, Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Maradun, digirin girmamawa don haƙiƙa ya cancanci hakan.
Aliyu Ammani
14/06/24
Ƙarin Bayani: Hoton dake biye da wannan rubutun na Marigayi
Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Maradun ne, "Ƙwairo mai ƙera waƙa; Ƙwairo mai lasifika".
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.