Ticker

6/recent/ticker-posts

Kayan Sarauta Na Al'ada, Kayan Sawa Da Kayan Rikewa Na Mulki Da Dawaki Da Ake Amfani Da Su A Masarautar Zazzau

1. RAWANI BAKI (DAN KURA): Ana yin sa da yadi na akoko ko alawayyo ko saka asala sannan a rina shi a garin Kura, kasar Kano. Kuma ana yinsa a Zariya a Marina

2. RAWANI HAKORIN FARA: Wannan Rawani yana zuwa ne a sakakkensa kuma yana da ratsin kala a gefensa na dama da na hagu. Ana yin sa a Unguwar Masaka Zariya

3.RAWANI SAKAKKE: Shi ne ake kira farin saka asali kuma ana saka shi a Kano da zariya

4. RAWANI AGANDI: Ana zuwa da shi daga kasar Maroko da Masar

5. RIGA TOKARE: Riga Tokare ana yinta da yadi amma dinkin hannu mai manyan asake guda biyu kuma ana dinka ta tare da datsi-datsi ana dinka ta a zariya

6. RIGA BULLAN: Rigar Bullan, Riga ce ta Saki da ake saka ta da zaren kadi kuma ana yi mata aiki a jikinta. A na dinka ta a Kano da Yola da Katsina

7. RIGA 'YAR MADAKA: Ana mata aiki mai yawa a jikinta da zare tun daga farkonta har karshe, a na dinka ta a Unguwar Madaka, zariya

8. RIGA KWAKWATAN SAKI BAKA: Duk kusan Rigar kwakwata yanayin dinkinta daya ne, kuma tsarin rigar shi ma yanayi daya ne sai dai kowace kasa akwai tasu kuma da irin kalanta. Akwai kwakwatar yadi wadda ake dinkawa a zariya, akwai kwakwatar Saki baka wadda ake dinkawa a ilori, 'yan 'ise sai Kwakwatar Saki Ja, ita ma a na yin ta a Zariya da sakkwato

9. RIGA KWAKWATAR YADI: A na dinka ta da yadi aikin hannu ko na keken dinki

10. RIGA AGANIYA: Ana dinka ta da yadi dinkin Tela

11. RIGA KWAKWATAR TSAMIYA: Ana dinka ta da Saki ai mata aiki

12. RIGA 'YAR ISE: Ana dinka ta da bakin Saki ai mata farin aiki

13. RIGUNA GIRKEN SAKI: Wadannan riguna dinkinsu da tsarinsu iri daya ne sai dai kowacce da irin yadda sakarta take. Ita girken saki, ana samunta a baka, watau sakar bakin saki ita kuma girken tsamiya ana mata saka ne da zaren tsamiya wato kalar tsamiya kuma dukkansu ana masu dinki ne da zare fari. Wadannan riguna ana dinka su a kasar Bidda da Zariya

15. RIGAR BARAGE: Rigar Barage , rigar Sarki ce wadda ake mata layi-layi ko ratsi-ratsi da wata kalar Ja, a jikinta ko kuma Ja da ratsin baki, sannan ana yi mata aiki a jikintane zare, ana dinka ta a zariya

16. RIGAR SHUNI: Wannan riga ce ta yadi ko saki amma ana rina ta ne da rinin shuni baki duka gaba dayanta. Ana yin ta a Sakkwato da Maiduguri da Zariya da Kano

17. RIGA GABAN HANKAKA: Wannan riga ana dinka ta da yadi fari ko shadda ko wagambari, sai a rina ta baki daya kalar sudi. Daga baya sai a yi ma gabar rigar kala baki mai turuwa sosai. Ana yin wannan riga a zariya da katsina da Kano da Sakkwato da Maiduguri

18. RIGA ALLURA BIYU: Riga Allura biyu da aska biyu duka riga iri guda, ana musu dinkin hannu da ake cewa dinkin aska biyu. Abin da ya bambanta tsakanin aska biyu da allura biyu shi ne, allura biyu wajen dinkinta ana yinta da zaren dinki kala biyu kamar misali a hada jan zare da fari ko shudi da kore fari da baki ko ja da mai ruwan goro

Haƙƙin Mallaka: Shafin Ƙasar Zazzau Jiya Da Yau

Fadar Zazzau

Post a Comment

0 Comments