Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Son Wata Yarinya Idona Rufe

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Ina tsananin son wata yarinya, idona duk ya rufe akanta, amma ita kuma ba ta sona, na rasa yadda zan yi saboda zankwaɗeɗiya ce, son kowa ƙin wanda ya rasa, bana iya bacci saboda tunaninta, a bani shawara.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. To, ɗan uwa ka nemi zaɓin Allah a duka lamuranka. "Allah yana cewa:

...وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

Akwai fãtar cwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhri a gare ku, kuma akwai fãtar cwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba. (Suratul Baƙara, aya ta 216).

Wannan aya ta ƙunshi sirrika da yawa, saboda duk lokacin da bawa ya san cewa, abu mai kyau yana iya zuwa da mara kyau, sannan mara kyau yana iya zuwa da mai kyau, wannan zai sa ba zai aminta daga cewa musiba za ta iya samunsa ta hanyar farin ciki ko akasin haka ba, saboda ba shi da ilimin ƙarshen lamura. Allah kuma ya san abin da bawa bai sani ba, wannan zai wajabtawa bawa abubuwa kamar haka

1. Babu abin da yafi ga bawa fiye da ya aikata abin da Ubangijinsa ya umarce shi, ko da kuwa da wahala, saboda ƙarshen lamarinsa zai zama farin ciki da annashuwa.

2. Ya wajaba ya bar aikata saɓo, saboda ƙarshensa musifu ne masu yawa, ko da kuwa farkonsa akwai annashuwa.

3. Yana da kyau bawa ya miƙa lamuransa zuwa wanda ya san makomar al'amura wato Allah, ya kuma yarda da abin da ya zaɓar masa.

4. Kar ya roƙi ubangijinsa abin da ba shi da ilimi akai, zai yiwu ya hallaka ko ya cutu, idan aka ba shi wannan abin, kamata yayi ya roƙi Ubangijinsa ya zaɓa masa.

5. Duk lokacin da bawa ya nemi zaɓin Allah, hakan zai hutar da shi daga yawan tunanin abin da zai aikata.

Duba Al-Fawa'id, shafi na (246).

Allah ne mafi sani.

𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments