𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Hadisin da ya ce: Wanda duk ke da hali yin layya sai kuma ya ki yi, to kar ya kusanci masallacinmu. Shin wannan hadisin ya inganta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya ce:
مَنْ وَجَدَ سَعَةٌ فَلَمْ يُضَحِّ ، فَلَا
يَقْرَبَنَّ مُصَلَّانَا
Duk wanda ya samu yalwa kuma sai bai yi layya ba, to kar ya
yi ko kusa da wurin sallar idinmu.
Al-Imaam Ahmad (a cikin Al-Musnad: 8256) da Al-Imaam Ibn
Maajah (a cikin As-Sunan: 3242) da Al-Haakim (a cikin Al-Mustadrak: 7576) suka
riwaito shi ta hanyar Abdullaah Bn Ayyaash, daga Abdurrahman Al-A’raj, daga
Abu-Hurairah, daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
Sai dai kuma shi Ibn Ayyaash ɗin
malamai sun ce: Yana da ɗan
rauni, shiyasa Muslim ya riwaito riwayarsa a cikin littafinsa a matsayin shaida
ga wata, kamar yadda Al-Haafiz Al-Asqalaaniy ya faɗa a cikin At-Taqreeb.
Amma kuma wannan hadisin yana da wata riwayar da ta ƙarfafe
shi. Ita ce riwayar Ubaidullaah Bn Ja’afar
da ya riwaito daga Al-A’raj,
daga Abu-Hurairah, mauqufiyah gare shi. Haka Ad-Daaraqutniy ya kawo a cikin
(Al-Ilal: 2023).
Amma kuma duk da haka, tana da hukuncin riwaya ce
marfu’iyyah. Domin ba zai yiwu Abu-Hurairah ya faɗi
wannan kawai da ra’ayi ko ina-gani fahimta daga tunaninsa ba.
Wani daga cikin malaman hadisi ya faɗi cewa wai maruwaicin hadisin, watau: Ibn
Ayyaash ya yi idtiraab a cikin riwayar. Sai dai kuma wannan ba idtiraabi ne mai
cutarwa ba, domin babu cin-karo ko saɓani
da juna a cikin ma’anarsa a tsakanin dukkan riwayoyin, kamar haka
1. ‘Wanda ya samu yalwa sai kuma bai yi yanka ba…’
2. ‘Wanda ya kasance yana da yalwa kuma sai bai yi layya
ba…’
3. ‘Wanda a wurinsa akwai yalwa…’
4. ‘Wanda ya kasance yana da dukiya…’
5. ‘Wanda ya samu yalwar da zai iya yin layya, sai kuma bai
yi ba, to kar ya halarci wurin sallarmu.’
A taƙaice dai, manyan malaman hadisi irin su: Al-Haakim da
Az-Zahabiy duk sun sahhaha shi, sannan kuma a cikin Sahih Ibn Maajah: (3123)
Shaikhul Islaamil Albaaniy ya hassana shi.
Wannan hadisin ɗaya
ne daga cikin hadisan da waɗansu
malaman suka kafa hujja da su wurin cewa, layyar wajiba ce a kan mai hali.
Domin tun da aka hana shi kusantar wurin sallar idi wannan ya nuna cewa abin da
ya bari wajibi ne, kamar dai cewa ake yi: Babu wata fa’ida gare shi ga kusantar
masallaci tare da barin wannan wajibin!
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.