Cite this book as: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Wasannin Kwaikwayo na Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-59094-0-1.
WASANNIN
KWAIKWAYO NA HAUSAWA
Sadaukarwa
Wannan aiki sadaukarwa ne ga
masu tunani nagari da karɓar shawarwari nagari da kuma
aikata aiki nagari. Babban goron da marubutan ke buƙata shi ne addu’ar alhairi, suna raye da
bayan ransu.
Godiya
Da sunan Allah Mai Rahama
Mai Jin ƙai. Tsira da amincinSa su ƙara tabbata ga mafificin halittu Manzon
tsira Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Samun ƙwarin guiwa da jajircewar kammala wannan
ɗan ƙwarya-ƙwaryar
Littafi na nuni ga ikon Allah da taimakonSa dangane da aikin. Muna ƙara maSa godiya dangane da lafiya da
juriya da Ya ba mu har Littafin ya zama abin da yake a yau.
Ba za mu taɓa
mantawa da taimakon Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Dr. Musa Fadama Gummi da
Dr. Alamuna Nuhu da Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad da Malam Almustapha Sambo Wali
da Malam Ibrahim Ɗalha
ba. Sun sadaukar da lokacinsu domin sanya albarka ga littafin. Da fatan Allah
Ya saka musu da mafificin alkairi. Bayan haka, muna miƙa godiya ga dukkanin waɗanda
suka taimaka da addu’o’i da kuma Allah san barka har dai aikin wannan littafi
ya kammala.
Mun gode.
Prof. Yakubu Aliyu GOBIR
Abu-Ubaida SANI
02-01-2023
Muƙaddima
Da sunan Allah Mai Rahma Mai
jin ƙai. Tsira da aminci su tabbata ga
Annabin Rahama Muhammadu ɗan Abdullahi da iyalan
gidansa da sahabbansa da waɗanda suka yi koyi da su da
kyautatawa ya zuwa ranar sakamako.
Na daɗe
ina tunanin yadda za a samu wani gawurtaccen aiki da zai harari wasannin
yaranmu maza da mata da idon basira ta yadda duniyar ilmi za ta amfana da shi.
Cikin ikon Allah, sai ga wasu masana da ban taɓa
tattaunawa da su ba kan haka, sun yi canjaras da tunanina sai na ji an yi mini
susa gurbin ƙaiƙai. Da na karanta wannan littafi na
gamsu da cewa, ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba. Babu wai, ƙasar
Hausa zuriya ɗaya ce, nisantar wurin zama ya haifar da
bambance-bambancen al’adu da karin harshe. Prof. Yakubu Aliyu Gobir, ko ba a faɗa ba
mutumin Gobir ne, Abu-Ubaida Sani daga Bauchin Yakubu sai ga shi sun kalli
wasannin yara na ƙasar
Hausa da tunani ɗaya, ka ce gari ɗaya
ake wasannin. Wannan wata manuniya ce ga buƙatar
irin wannan aiki a duniyar karatun Hausa. Wannan giɓin
da manazartan suka cike ya cancanci ya shiga hannun ɗalibai
da malamai da manazarta Hausa domin su amfana da shi. Haƙiƙa
aikin ya aikatu, ba a yi kasala ba, ba a zure ba, ba a yi azarɓaɓi
ba, an shimfiɗa rubutun bisa ga ladabi da biyayyar karɓar
ilmi da bayar da shi. A tunaninmu na ɗaliban
al’ada da adabi wannan aiki ya cancanci babban yabo domin ba ya jin kunyar ido
huɗu da
ɗaliban
fanninsa da masu sha’awar karatunsa. Fatana shi ne, Allah Ya sa albarka, Allah
Ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya, Gusau.
Tsokaci
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Tsira da
aminci su daɗa tabbata ga fiyayyen halitta, manzon
rahama, Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa, da dukkan masu koyi da
shi har ya zuwa ranar sakamako. A
matsayina na ɗalibi mai bincike da nazarin al’adun
Hausawa, na duba wannan muhimmin littafi mai suna Wasannin Kwaikwayon Hausawa
wanda Prof. Yakubu Aliyu Gobir da malam Abu-Ubaida Sani suka wallafa. Haƙiƙa
wannan wani gagarumin aiki ne mai ɗimbin
fa’ida, musamman idan aka yi la’akari da cewa littattafan da aka wallafa waɗanda
suka gabaci wannan aiki ba su yi
bakandamen tattara wasanni na maza da na mata, na yara da na manya ba a
wuri ɗaya.
Haƙiƙa
littafin bai bar wata kafa ta susar akaifa ba domin ya tattaro kusan duk
wasanni na da da kuma na yanzu.
Fatar da nake yi ita ce Allah ya albarkaci wannan gagarumin
aiki nasu, ya kuma saka masu da mafificin alheri. Amin!
Dr. Musa Fadama Gummi
Department of Languages and
Cultures
Federal University Gusau
Ta’aliƙi
Littafin Wasannin Kwaikwayon
Hausawa ƙari ne cikin jerin littattafan da
malamai da manazarta suka samar domin taskace wani ɓangare
na rayuwar Hausawa jiya da yau. Bisa dukkan alamu, an gudanar da ƙwaƙƙwaran
bincike musamman ziyarar gani da ido domin neman waɗannan
wasannin kwaikwayo na gargajiya game da yadda suke da yadda ake aiwatar da su.
Wani abin ban sha’awa da littafin shi ne, an fasalta wasannin kwaikwayon ƙasar Hausa bakin gwargwado ta fuskar
jinsi da shekaru da yanayin aiwatarwa da lokaci da yanayin wasannin. Hakan ya
sa aka sami bambanci tsakaninsu da sauran takwarorinsu littattafan wasannin
Hausawa da suka gabaci wannan. Babu shakka littafin zai taimaki malamai da masu
nazarin wasannin Hausawa da matani a kammale na nau’o’in wasanni waɗanda
suke daga ɓangarori daban-daban na ƙasar Hausa.
Hausawa suna cewa: “Wasa ba
faɗa
ba”. Tabbasa, marubutan wannan littafi sun yi ƙoƙari wurin samar da aiki wanda zai ƙara bunƙasa
bincike a fannonin nazarin harshen Hausa, musamman a wannan zamani da wasannin
gargajiya na Hausawa suke ɗaukar fasali irin na
wasannin zamani. A gaishe da Malam Farfesa Yakubu Aliyu Gobir da Malam
Abu-Ubaida Sani da ƙoƙari. Allah ya sa littafin ya zama mai
amfani ga masu karatu da nazari, ya kuma zama abin yin madogara a fagen nazarin
ilimi a matakai daban-daban.
Dakta Alamuna Nuhu
Tsangayar Fasaha,
Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami’ar Jihar Kaduna,
Kaduna.
Allah San Barka
Wasannin Kwaikwayon Hausawa,
wani littafi ne kandamin a sha a yi wanka, wanda aka rubuta shi tare da tsara
shi bisa kyakkyawan bincike da nazarce-nazarcen bayanai masu tarin yawa. Ya
shafi wani muhimmin fanni na bayyananniyar al’adar Bahaushe. Dalili kuwa, kusan
ana iya cewa an tattaro wasanni na zamanin da, da kuma na zamanin yanzu tare da
hasko waɗansu
sauye-sauye waɗanda zamanin ya kawo. Babu shakka
littafin ya fito da wasu abubuwa tare da ƙara
haske dangane da abin da ya shafi wasannin Bahaushe. Marubutan sun yi bayanai
da suka shafi wasanni a ƙasar
Hausa ta hanyar rarraba su bisa la’akari
da adadin shekaru ko jinsin waɗanda ke gudanar da wasannin.
Littafin na ɗauke da kammalallen bayanai game da
wasannin. Ya faro tun daga bayyana ma’anar wasanni da amfaninsu har zuwa
bayanin yadda ake gudanar da su dalla-dalla.
Bayan haka, marubutan sun
binciko wasu abubuwa masu nuna alaƙa ko
dangantaka da ke tsakakanin wasanni da rayuwar Bahaushe. Bayyana waɗansu
abubuwan azanci da hikima na Bahaushe da suka shafi wasanninsa sun ƙawata littafin. Babu shakka wannan
Littafi zai taimaka ga fagen ilmi. Zai kuma taimaka wa ɗalibai
na kowane mataki daga sakandare zuwa jami’o’i, malamai da sauran al’umma da ke
sha’awar nazarin al’adun Bahaushe. Na yaba tare da jinjina wa marubutan da
fatan Allah ya ƙara
taimako da ƙarfin guiwa. Amin.
Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad
Department of Nigerian
Languages
Faculty of Humanities
Sule Lamido University Kafin
Hausa
Jigawa State.
Goyon Baya
A lokacin da nake karanta
wannan littafin, abin da ya zo min a rayuwata shi ne irin yadda rayuwarmu ta
kasance a lokacin da muke aiwatar da ire-iren waɗannan
wasannin. A lokacin, rayuwa cike take da nishaɗi da
farin ciki da kuma ƙaruwar
tarbiyya a tsakaninmu, wato lokacin da muke yara. Tabbas, darussa ko jigogin da
wannan littafin ya bayyana ana ta samun raguwarsu a wannan zamanin da muke
ciki. Zamananci ya zo da abubuwa da dama waɗanda
suke dushe waɗannan wasannin da ma darussan da suke
koyarwa. Saboda haka, wannan littafi mai suna Wasannin Kwaikwayon Hausawa ya
taimaka ƙwarai da gaske wajen adana wasu daga
cikin waɗannan
wasannin. Ko da kuwa wasannin sun salwanta, to za su kasance a kattabe har
Madi. Da fatar Allah ya saka wa marubuta wannan littafin da alhairinsa.
Malam Almustapha Sambo Wali
National Institute for
Nigerian Languages
Jinjina
Gaskiyar Hausawa da suka
aminta da cewa: “Sanin wurin bugu shi ne ƙira.” Samar da wannan littafi mai
suna Wasannin Kwaikwayon Hausawa da Prof. Yakubu Aliyu Gobir da Malam
Abu-Ubaida Sani suka yi, bai zo mana da mamaki ba, duba da irin saninsu game da
abubuwan da suka shafi al’adun
Hausawa da kuma irin yadda suka goge wajen
karantar da al’adun
na Hausawa. Nau’o’in wasannin da littafin ya
tattaro, shi ya nuna gagarumin aikin zai
taimaka wa malamai da ɗalibai a matakan ilimi
daban-daban (firamare zuwa jami’a). Don haka, samun wannan littafi a wannan
lokaci abu ne da ya zo daidai lokacin da ake buƙata.
Wato dai, tamkar wani kaya ne da ya tsinke a gindin kaba.
Allah Ya ƙara wa marubuta wannan littafi basira da
juriya. Muna roƙon
Allah Ya sa littafin ya zama mai amfani ga al’umma baki ɗaya;
Ya kuma ci gaba da ɗaukaka Hausawa da karatun
Hausa. Amin.
Malam Ibrahim Ɗalha,
GDSSS, Birnin Kudu,
Ministry of Education
Science & Technology, Dutse,
Jigawa State.
Ƙunshiya
SADAUKARWA iii
GODIYA iv
Muƙaddima v
Tsokaci vi
Ta’aliƙi vii
Allah San Barka viii
Goyon Baya ix
Jinjina x
GABATARWA xvii
Kalmomin Fannu xix
BABI NA ƊAYA
WASANNIN KWAIKWAYO
1.0 Gabatarwa 1
1.1 Ma’anar Wasannin
Kwaikwayo na Hausa 1
1.2 Muhimmancin Wasannin
Kwaikwayo 2
1.2.1 Horo da Gyaran Hali 3
1.2.2 Hannunka-Mai-Sanda 3
1.2.3 Jarumta Da Bajinta 4
1.2.4 Motsa Jiki 4
1.2.5 Hikima Da Dabara 4
1.2.6 Bin Doka Da Ƙa’ida 5
1.2.7 Ilimantarwa Da
Taskance Harshe Da Al’ada 5
1.2.8 Nishaɗi 5
1.2.9 Hana Yawon Banza 5
1.2.10 Ƙarfafa Danƙon
Zumunta 6
1.2.11 Wayewa Da Iya Magana
Cikin Jama’a 6
1.2.12 Bayyana Muradun Zuci 6
1.3 Rabe-Raben Wasannin
Kwaikwayon Gargajiya 7
1.3.1 Iren-Iren Wasanni
Kwaikwayo Ta Fuskar Yanayin Aiwatar Da Su 7
1.3.1.1 Wasan Magana 8
1.3.1.2 Wasan Kurma 8
1.3.2 Rabe-Raben Wasannin
Kwaikwayo Ta Fuskar Masu Gudanarwa 9
1.3.2.1 Wasannin Kwaikwayo
Na Yara 9
1.3.2.1.1 Wasannin Kwaikwayo
Na Yara Maza 9
1.3.2.1.2 Wasannin Kwaikwayo
Na Yara Mata 10
1.3.2.1.3 Wasannin Kwaikwayo
Na Yara Maza Da Mata 10
1.3.2.2 Wasannin Kwaikwayo
Na Manya 11
1.3.2.2.1 Wasannin Kwaikwayo
Na Manyan Maza 11
1.3.2.2.2 Wasannin Kwaikwayo
Na Manyan Mata 11
1.3.2.3 Wasanni Kwaikwayo Na
Gama-gari 12
1.3.3 Rabe-Raben WK ta
Fuskar Lokacin Gudanarwa 12
1.3.3.1 Wasannin Kwaikwayon
Rana 12
1.3.3.2 Wasannin Kwaikwayo
na Dare 13
1.3.3.3 Wasannin Kwaikwayo
Marasa Ƙayyadajjen Lokaci 13
1.3.4 Wasannin Kwaikwayo
Masu Waƙa Da Marasa Waƙa 14
1.3.5 Wasannin Kwaikwayo
Masu Jagora Da Marasa Jagora 14
1.4 Naɗewa 15
BABI NA BIYU
WASANNIN KWAIKWAYON YARA
MAZA
2.0 Shimfiɗa 16
2.1 Taɓaɓɓe 16
2.2 Langa 18
2.3 Ba Mu Kuɗinmu 20
2.4 Ɓelunge 22
2.5 Ɗanduƙunini/Ɗanduƙununu 24
2.6 Yaƙi 25
2.7 Dokin Kara 27
2.8 Bindiga 28
2.9 Sallar Kwaɗi 30
2.10 Motar Kara 32
2.11 Danda Dokin Kara 34
2.12 Alhajin Ƙauye 35
2.13 Mai Ƙiriniya 37
2.14 Tashi Mai Kwaɗayi 39
2.15 Baran Baji 40
2.16 Zule-Zuleyya 42
2.17 Ni Cadi Zan Tafi 44
2.18 Ɗantsoho Mai Cin Bashi 45
2.19 Tsoho Da Gemu 47
2.20 Taya 48
2.21 Na Ci Na Kasa Tashi 50
BABI NA UKU
WASANNIN KWAIKWAYON YARA
MATA
3.0 Shimfiɗa 51
3.1 To Iya 52
3.2 Samodara 53
3.3 Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu 55
3.4 Matar Nakarofi 57
3.5 Maimuna Ta Yi Ciki Ga
Goyo 59
3.6 Hajiyar Ƙauye 60
3.7 Mai Ciki 62
3.8 Kwalba-Kwalba Dire 63
3.9 A Fiffigi Zogale 65
3.10 Ɗanlele 67
3.11 Gamuna 69
3.12 Ragadada 70
3.13 Kallo Da Ido 72
3.14 Dinga-Dinga 75
3.15 A Cikin Wannan Rana 77
3.16 Ke Kika Je Gidansu
Direba 78
3.17 Jar Miya 79
3.18 Ga Mairama Ga Dauda 80
3.19 Rabi Da Audu 82
3.20 Ga KuɗinToshinki
Na Bara 83
BABI NA HUƊU
WASANNIN KWAIKWAYO NA
TARAYYA
4.0 Shimfiɗa 85
4.1 ‘Yartsana 86
4.2 Tuwon Ƙasa 88
4.3 Zuciyar Mai Tsumma 90
4.4 Ɗakin Tsuntsu 91
BABI NA BIYAR
WASANNIN KWAIKWAYON MANYA
5.0 Shimfiɗa 93
5.1 Gwauro 94
5.2 Boka Kake Ko Malami? 97
5.3 Jatau Mai Magani 99
5.4 Wandara A Sha Maganin Ƙaba 102
5.5 Macukule 104
BABI NA SHIDA
TASIRIN ZAMANI A KAN
WASANNIN KWAIKWAYON HAUSAWA NA GARGAJIYA
6.0 Shimfiɗa 107
6.1 Dalilan Dusashewar
Wasannin Kwaikwayon Gargajiya 107
6.2 Sauye-Sauye A Wasannin
Kwaikwayon Hausa Na Gargajiya 112
6.3 Naɗewa 112
Manazarta 113
Gabatarwa
Haƙiƙa,
wasannin kwaikwayo na gargajiya sun kasance wani ɓangare
na rayuwar ɗan’adam. Wannan kuwa bai tsaya a kan
Hausawa ba kawai, ya shafi dukkanin al’ummun duniya da ke ƙasashe daban-daban. Sai dai akan sami
bambance-bambancen salo da siga na waɗannan
wasanni, wanda hakan ya danganta ga al’ada da yanayin wurin zama na masu wannan
wasa.
Wasannin kwaikwayon da
Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni na fuskantar dusashewa, tamkar dai
sauran al’adun Hausawan. Wannan na faruwa ne sakamakon dalilai masu dama waɗanda
za a iya taƙaita su da furucin
tasirin zamani. Lura da wannan ƙoƙarin ɓacewa
da mafi yawan wasannin kwaikwayo na gargajiya ke yi, akwai buƙatar killace su wuri ɗaya
a matsayin wani kundin da zai kasance abin waiwaiya a kodayaushe. Yin hakan zai
sanya ko da wasannin kwaikwayon sun gushe a zamani, za su kasance a killace har
Madi.
Marubutan wannan Littafin
sun tattara wasannin gargajiya na Hausawa guda ɗari
biyu da goma shahuɗu (214) a shekara ta 2021.
Sun wallafa su a cikin littafi mai suna Wasanni a Ƙasar Hausa. Littafin ya ƙunshi dukkannin nau’ukan wasanni – na kwaikwayo da waɗanda
ba na kwaikwayo ba. Daga baya ne suka yi tunanin ware wasannin kwaikwayo daga
cikinsu. An yi nasarar ware wasannin kwaikwayo guda 50.
An raba littafin zuwa babuka
shida (6). Babi na farko yana ɗauke da gabatarwa. A ciki an
kawo bayani game da ma’anar wasan kwaikwayo. An kuma kawo amfanin wasannin
kwaikwayo da rabe-rabensu. Babi na biyu zuwa na biyar kuwa na ƙunshe da bayanai game da wasannin
kwaikwayo na gargajiya daban-daban. Sun haɗa da
na yara maza da yara mata da na tarayya. A gefe guda kuwa, an kawo na manya
maza da mata. Babi na shida wanda shi ne na ƙarshe,
yana ƙunshe da bayani game da tasirin zamani a
kan wasannin kwaikwayon Bahaushe na gargajiya.
Bayan an kawo jerin
manazarta, sai kuma aka biyo baya da ratayen waɗannan
wasannin kwaikwayo na gargajiya cikin tsararren jadawali. An yi hakan ne domin
samar da haske ga mai karatu ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci
a kan kowane wasa kai tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa da suka haɗa
da:
i. Sunan wasa
ii. Masu wasa
iii. Rukunin wasa
iv. Kayan aiki
v. Amfanin wasa
Prof. Yakubu Aliyu GOBIR
Abu-Ubaida SANI
02-01-2023
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.