Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Azumi Ya Wajaba A Kan Dan Shekara Sha-Biyar (15)?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam barka, malam dan Allah ina son in san actual shekarun da namiji azumi ya wajaba a gare shi, muna da yaro yana cikin shekara ta 15 Amma muryar shi ta yi nauyi kuma gashin hamata ya fito masa amma abun da ba mu sani ba ko ya yi mafarki, to shi ne bai son yin azumi ni kuma ina ganin kamar azumi ya wajaba a gare shi amma babansa yana yi masa daukar karamin yaro.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, Duk yaron da waɗannan abubuwa guda uku suka tabbata a tare da shi, to babu shakka ya kai haddin balaga

1. Tsurowar gashin mara, ko na Hammata.

2. Kai wa shekara goma sha biyar (15).

3. Yin mafarki.

Matuqar ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa uku ya sami yaro namiji, to ya balaga, kuma azumi da sauran ibadoji kamar sallah da sauransu, sun hau kansa.

Idan kuma mace ce sai a qara mata da

4. Al'ada ko Haila.

Dazarar ɗaya daga cikin huɗun nan ya tabbata ga ƴa mace, to ita ma azumi da sauran ibadoji sun wajaba a kanta. Saboda haka, kuskure ne a bar yaron da ya kai shekara goma sha biyar (15), ko ya taɓa yin mafarkin saduwa, ko gashin mara da hamata suka fito masa ya qi yin azumi.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖��𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments