𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Na kasance mai azumi sai na yi
barci a masallaci, dana tashi sai na samu cewa na yi mafarki, Shin mafarkin
yana da tasiri ga azumina? Tare da cewa banyi wanka ba sai kawai na yi sallah
ba tare da nayi wankan ba.
Wata rana kuma dutse ya rotse min
kai sai jini ya kwarara, Shin azumina ya lalace saboda fitan jini?
Dangane da amai kuma shin yana ɓata azumi ko a'a? Ina
fatan a amfanar da ni?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Lallai mafarki baya lalata azumi,
kuma baya yi masa tasiri; saboda kasancewarsa yana fita ne ba a cikin zabin
mutum ba, Sai dai kuma wajibi ne akansa ya yi wankan janaba idan har maniyyi ya
fita daga gare shi, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم)
yayin da aka tambaye shi kan haka, sai ya amsa da cewa mai mafarki zai yi wanka
ne; idan har ya ga ruwa (maniyyi).
Sallar da ka aikata ta kuma ba
tare da ka yi wanka ba wannan jahilci ne daga gare ka, abun kyama, kuma dole ne
akanka ka sake sallah bayan ka yi wanka, kana mai tuba zuwa ga Allah (سبحانه وتعالى).
Shi kuma dutsen da ya rotse kanka
har ya kwararar da jinni babu komai akan haka.
Shi kuma amai da ya fita maka ba
tare da zaɓinka ba,
to ba zai ɓata maka
azuminka ba; saboda faɗin
Annabi (صلى الله عليه وسلم)
«مَنْ ذَرَعَهُ الْقَيْءُ فَلَا قَضَاءَ عَلَيْهِ،
وَمَنِ اسْتَقَاءَ فَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ».
MA'ANA: "Wanda amai ya
rinjaye shi to babu ramukon azumi akansa, duk kuma wanda ya janyo amai to
wajibi ne akansa ya yi ramuko", Ahmad da ma'abota littafan
"sunan" suka rawaito shi da isnadi ingantacce.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.