Kwatancen Fasaha Tsakanin Wakar Fara Dindiba Da Ta Farar Dango

    Citation: Bunza, D.B. (2024). Kwatancen Fasaha Tsakanin Waƙar Fara Dindiɓa Da Ta Farar Ɗango. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 372-380. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.043.

    Kwatancen Fasaha Tsakanin Wa Æ™ ar Fara Dindi É“ a Da Ta Farar ÆŠ ango

     

    Daga

    Dano Balarabe Bunza (PhD)
    Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
    Jami’ar Usmanu ÆŠ anfodiyo, Sakkwato.
    Email: danobunza@gmail.com
    Phone: 07035141980

    Tsakure

    An gina wannan ma Æ™ala ta yin la’akari da wasu wa Æ™ o Æ™ i biyu na marubuta biyu a kan wasu fari da suka addabi al’umma a cikin Æ™ auyuka da birane ta hanyar cin hatsin da aka noma tare da nakasa shi tun yana tsaye. An lura da wasu abubuwa da marubutan suka yi canjaras da juna a cikin wa Æ™ o Æ™ insu, duk da yake babu wanda ya tuntu É“ i wani kafin ya rubuta ko lokacin da yake rubuta wa Æ™ arsa. Abubuwan da aka yi kwatance tsakanin wa Æ™ o Æ™ in biyu sun ha É— a da mabu É— in wa Æ™ o Æ™ in da marufinsu da sa Æ™ on wa Æ™ o Æ™ in kasancewarsu iri É— aya, na tarihi. Bayan haka an kwatanta wa Æ™ o Æ™ in ta fuskar ambaton sanadiyyar zuwan farin da kuma ayyukan da suka yi na cutar da al’umma. Haka kuma marubutan sun ambaci farin dukkansu da rashin jin kora bayan sun sauka bisa hatsi. Ba wannan ka É— ai ba, marubutan sun ambaci farin sun yi zagayen garuruwa da yawa, wanda ke nuna ba wuri É— aya suka tsaya da ayyukansu ba. Kwatanta wa Æ™ o Æ™ in biyu da aka yi, marubutan sun fa É— i lokacin zuwan farin babu bambanci, wato duk a lokaci É— aya suka zo ko cikin shekara É— aya. Dangane da yawan layukan da suka zuba a matsayin baiti duk tangam (iri É— aya) ne. Kowannensu ya samar da baitin wa Æ™ arsa ta hanyar shirya shi da layuka biyu kacal (‘yar tagwai ce). Tare da haka, duk abubuwan da aka ambata na kwatance tsakanin wa Æ™ o Æ™ in marubutan biyu an raka su da misalan da mai karatu zai fahimci inda ma Æ™ alar ta dosa. Haka na tabbatar wa mai karatu cewa, kwatancen da aka yi da misalan da aka kawo na tabbatar da wa Æ™ o Æ™ in sun mallaki wasu siffofi iri É— aya da ake samu a cikin kowaccensu.

    Gabatarwa

    Allah ka É— ai ya san abin da ke tsakaninsa da bayinsa dangane da ayyukan da suke aikatawa a dare da rana, domin shi ne masanin fi li da É“ oye. Tare da haka, an sanar da bayi cewa duk wanda ya aikata alheri ko akasinsa zai ga sakamakonsa , faman ya’amal mis Æ™ ala zarratin khairan yara, waman ya’amal mis Æ™ ala zarratin sharran yarah ( Qur’an, 99:7-8). Haka kuma , Allah na jarraba imanin bayi gwargwadon ayyukan da suke aikatawa Walanablu wannakum bi shai’in minal khaufi wal ju’i… .” ( Qur’an, 2:155-156 ). Abubuwa da dama na jarrabawa sun faru ga bayi domin gano masu yi da gaskiya da wa É— anda ba su ba. An jarrabi Annabawa da salihan bayi da abubuwa masu yawa domin fitar da masu gaskiyar imani daga wa É— anda ba su ba. Bayan jarraba bayi domin a gano gaskiyar imaninsu, akan hukunta su dangane da ayyukan da suka aikata ya zama horo da jan kunne ga abubuwan da suka aikata a rayuwarsu ta yau da kullum. A kan haka ne aka samar da wannan takarda don tabbatar da Allah na kama bayi a kan laifukan da suke aikatawa. Wannan ne ya sanya aka kawo wasu wa Æ™ o Æ™ i biyu domin a ji tarihin abin da ya faru ga wasu mutane sanadiyyar wasu ayyukan da suka aikata marasa kyau. Allah ya jarrabi al’ummar Æ™ asar Sakkwato da Kano da wasu fari sanadiyyar wasu ayyukan da suka aikata marasa kyau domin jan hankali gare su da na baya gare su. Wa Æ™ o Æ™ in biyu su ne ‘Wa Æ™ ar Fara Dindi É“ a” a Sakkwato wadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya rubuta da ta ‘Farar É— ango’ a Kano ta Sheikh Atiku Sanka. An yi haka domin bibiyar tarihi tare da yin hannunka mai sanda ga sauran jama’a cewa abin da ya faru ga wasu al’ummu na jarrabawa na iya faruwa ga kowa a sanadiyyar ayyukan sa É“ o, duk da yake ana sane da cewa wani/wasu na janyo wa wasu matsala sanadiyyar aikinsa ko ayyukansa marasa kyau. Ba wannan ka É— ai ba, domin ya kasance yankan hanzari ga mai Æ™ udurin aikata abin da yake sa É“ a wa Allah ne.

     Dalilin Bincike

    Dalilin da ya sa aka gudanar da wannan bincike shi ne domin a fito da kamannun da ke tsakanin wa Æ™ o Æ™ in biyu tare da kawo misalan da suka tabbatar da gaskiyar kwatancen da aka ambata. Wani dalili shi ne domin Æ™ ara wa juna ilmi kan abubuwan da za a tattauna. Haka kuma wani dalilin gudanar da wannan bincike shi ne, rashin samun takarda irin wannan a iya binciken da aka gudanar.

    Dabarun Bincike

    Daga cikin dabarun da aka yi amfani da su domin gudanar da wannan bincike sun ha É— a da farauto wa Æ™ o Æ™ in biyu, wato wa Æ™ ar fara dindi É“ a ta Maharazu Barmu Kwasare da ta farar É— ango ta Atiku Sanka Kano tare da nazarin su domin fito da wuraren da suka yi kama da juna. Haka kuma an yi amfani da littattafan masana da suka yi magana a kan rubutattun wa Æ™ o Æ™ in Hausa musamman na Abdul Æ™ adir ÆŠ angambo da Abdullahi Bayero Yahya da sauran wa É— anda suka yi rubutu kan rubutacciyar wa Æ™ a. Haka kuma an Le Æ™ a É— akunan karatu domin ganin ayyukan da aka yi a kan wa Æ™ o Æ™ in da suka shafi fagen da ake wannan bincike a kai. An yi hira da mutane masana wannan fanni domin gudanar da binciken da aka sanya a gaba na É— aya daga cikin dabarun gudanar da wannan bincike.

    Ta Æ™ aitaccen Tarihin Malam Maharazu Barmu Kwasare DA Na Sheikh Atiku Sanka Kano

    Malam Maharazu fitaccen marub u ci wa Æ™ a ne kuma sananne a zamaninsa. A lokacin da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya (1988) ya rubuta littafinsa mai suna ‘Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa’ ya kawo sunan Maharazu cikin marubuta wa Æ™ o Æ™ in jihar Sakkwato, kuma shi ne na goma sha biyu a ciki.

    Ba wannan ka É— ai ba, Malam Maharazu ya fa É— i ko shi wane ne a cikin wasu baitoci n wa Æ™ o Æ™ insa. Ga abin da ya ce a cikin wa Æ™ arsa ta masallaci:

    Tammat da É— a Bar m u ya cika wanga littafi,

    Sunansa Maharazu halshenai da Hausanci.

    Garinsu Kwasare nasbatai guda biyu ta,

    Abbun Fulatiyyi Ummu ha Æ™ i Æ™ a Gobarci.

    Idan aka dubi baitocin da ke sama na cikin “W a Æ™ ar M asallaci , za a fahimci sunan marubucin da kuma harshen da yake amfani da shi. A baiti na biyu kuma, ya kawo sunan garinsa da fa É— ar cewa yana da asali iri biyu, inda ya ce mahaifinsa Bafulatani ne, ita kuma mahaifiyar Bagobira ce. Duk inda aka sami mutum ya fa É— i sunansa da na garinsu kuma bai tsaya nan ba ya ha É— a da asalinsa, to ana iya cewa ya bayyana kansa da yadda ake iya gane ko shi wane ne.

    Bayan wannan kuma Malam Maharazu ya Æ™ ara wa mai karatun wa Æ™ o Æ™ insa haske game da shi kansa a cikin “W a Æ™ ar T a’azi y yar Malam B abi . Ga abin da ya ce:

    Tammat da É— a wa Æ™ a ta cika,

    Daga Barmu Maharazu sha’iri.

    Birnin Kwasare nan yaf fita,

    Wani mai yawo almajiri.

    Allah sarki! Dubi yadda Malam Maharazu ke ba da bayanin yadda ake gane shi a cikin wa Æ™ a kamar yana kallo ana kallon sa. A baiti na sama ya fa É— i sunansa tare da bayanin cewa shi fa marubuci wa Æ™ a ne. Bayan wannan ya Æ™ ara bayanin cewa Kwasare ne garinsa na haihuwa, kuma yawon karatu yake yi da na kasuwanci, kuma sana’ar koli ce sana’arsa. B ugu da Æ™ ari kuma almajiri ne mai neman ilmin addinin Musulunci da kuma karantar da shi . Ta hanyar wannan bayani za a tabbatar da akwai bayani cikakke ga duk mai neman sanin sa.

    Shi kuma Shehin Malami Atiku Sanka ba a sami ha É— a tarihinsa ba nan take, sai dai za a Æ™ o Æ™ arta nemo shi idan aka samu a sanya a cikin takardar. Abin da ake iya cewa game da shi kawai shi ne, babban malami ne a garin Kano. Haka kuma babba ne a cikin É— ari Æ™ ar Tijjaniyya, kuma sha’iri ne domin ganin wa Æ™ ar da ya rubuta ta farar É— ango da wasu da dama.

    Kwatance Tsakanin Wa Æ™ o Æ™ in Biyu

    Wa Æ™ o Æ™ in da takardar za ta yi magana a kansu sun ha É— a da ‘Wa Æ™ ar Fara Dindi É“ a’ ta Malam Maharazu Barmu Kwasare da ta ‘Farar É— ango’ ta Sheikh Atiku Sanka Kano. Fara Dindi É“ a ta bayyana a Æ™ asar Sakkwato, ita kuma Farar É— ango a Æ™ asar Kano lokaci mai tsawo da ya wuce. An Æ™ uduri gwama wa Æ™ o Æ™ in a wuri É— aya domin a fito da wuraren da suka yi kama da juna duk da yake marubutansu ba a wuri É— aya suke ba. Akwai abubuwa da dama da aka hango kuma masu kama da juna a cikin wa Æ™ o Æ™ in biyu da za a duba tare da cewa wa Æ™ o Æ™ in na É— auke da kamannu tsakaninsu kamar yadda za a gani nan gaba ka É— an. Daga cikin kamannun da ke akwai tsakanin wa Æ™ ar fara dindi É“ a da farar É— ango sun ha É— a da wa É— annan abubuwa da ke tafe:

    Jigon Tarihi

    Masana da manazarta sun yi Æ™ o Æ™ ari Æ™ warai ta fuskar bayyana ma’anar kalmar tarihi a cikin rubuce-rubucensu na yau da kullum. Ba za a kawo ma’anonin duka ba sai dai za a kawo É— aya ko biyu domin Hausawa sun ce “Daga na gaba ake gane zurfin ruwa”. Ga É— aya daga cikin ma’anonin da aka samu daga gare su:

    A wani wuri an sami ma’anar tarihi da cewa shi ne labarin abubuwan da suka wuce ( Æ™ amusun Hausa:429). Har yanzu an Æ™ ara da cewa, tarihi na nufin fannin ilmi na al’amurran da suka faru a zamanin da ya wuce. Idan aka lura akwai ala Æ™ ar aiki da masu aikata shi a cikin ma’anonin da aka kawo a sama. A wannan ma’ana an fahimci cewa tarihi shi ne labarin abubuwan da suka wanzu a lokaci mai tsawo da ya wuce.

    Wa Æ™ ar ‘Fara Dindi É“ a’ da ta ‘Farar É— ango’jigonsu iri É— aya ne. Duk suna É— auke da babban sa Æ™ o ko muhimmin sa Æ™ o na tarihin wanzuwar wasu fari da suka zo a Æ™ asar Sakkwato da Kano suka yi É“ arnar da ta kai mutane suka shiga halin Æ™ a Æ™ a-nika-yi. Aikin farin shi ne cinye hatsin da jama’a suka shuka, kuma sai hatsin da aka shuka ya kusa isa girbi sannan farin su zo su lalata shi. wanda a Æ™ arshe ya sanya al’ummomi suka fa É— a cikin matsalar rashin abincin da ya yi sanadiyyar matsananciyar yunwa a lokacin. Domin tabbatar da jigon wa Æ™ o Æ™ in iri É— aya ne, ga abin da Maharazu ya fa É— a a cikin wa Æ™ arsa:

    3. Can dauri yunwa ta wuce murna mukai,

    Kuma ga mu mun katce da munka ga dindi É“ a.

     

    5. Ita ba haki taka ci ba mi taka yi da shi?

         Sai dai hatci suwa a’ abincin dindi É“ a.

     

    6. In ta ga gero ba ta cin dawa ita,

         Farag ga ha’ iko takai muna dindi É“ a.

     

    11. Farin Æ™ warai ta bi su duk ta nakkasa,

         Duk ta gwada musu zamba fara dindi É“ a.

     

    18. Ta gayyato fari iri da iri duka,

         Sun taimake ta tana ta sharri dindi É“ a.

     

    25. Ta murmure geron mutan wajjen Maru,

         Mafara mafarin tasu yunwa dindi É“ a.

    Idan aka lura da abubuwan da ke cikin baitocin da ke sama, ba shakka za a fahimci akwai tarihi a cikinsu. An yi wannan wa Æ™ a tun shekarar1942, kuma sha’irin ya raja’a ga ba jama’a labarin abubuwan da suka faru sanadiyyar zuwan fara dindi É“ a a Æ™ asar Sakkwato. Idan aka bi wa Æ™ ar baki É— ayanta za a tabbatar da babban sa Æ™ on da take É— auke da shi tarihi ne. Marubucin ya fa É— a cewa farar ba ta cin haki sai hatsi kawai. Haka kuma idan ta sami gero ba ta damu da dawa ba. A nan marubucin ya bayyana cewa farar har za É“ e take yi idan ta tarar da gero da dawa. Haka kuma ya nuna cewa zuwan fara dindi É“ a ya yi sanadiyyar lalacewar sauran fari baki É— aya, domin a da ba su cutar al’umma, yanzu kuma suna yi saboda ha É— uwarsu da fara dindi É“ a. A ta Æ™ aice, ta koya musu zambatar jama’a ta inda suka koma cin hatsi wanda a da ba hakanan suke ba. Jin haka na nuna wa mai karatu cewa, akwai abubuwan da suka gabata da ake bu Æ™ atar sanar da shi, wato tarihin zuwan fara a Æ™ asar Sakkwato a wani lokaci mai nisa da ya gabata.

    A É“ angare É— aya kuma marubuci wa Æ™ ar ‘Farar É— ango’ ya tabbatar da jigon wa Æ™ arsa shi ne tarihi a inda ya ce:

     17. Idan ta sauka shuka duk ta cinye,

         Ta bar fili a banza aljaradu.

     

    18. Zuwan farko da rana ta zo garin nan,

         Muna kallon ta har la’asar jaradu.

     

    19. Zuwan na biyu ko ku san ta kewaye mu,

         Ta can bayan gari ta shigo jaradu.

     

    25. Wajen Badun a can fara ta somo,

         Ta zo nan munka gan ta fa aljaradu.

     

    26. Ta sam masara da dawa duk ta cinye,

         Fa har gero ta cinye aljaradu.

     

    29. Fa har Sarkin Kano ma ya yi ro Æ™ o,

         Ta’ala ai ya kore aljaradu.

     

    30. Æ™ asar Zazzau fa su ma sun yi ro Æ™ o,

         Ta’ala ai shi yaye aljaradu.

     

    Marubucin wa Æ™ ar Farar É— ango ya fito da jigon wa Æ™ arsa na tarihi a cikin baitocin da ke sama inda ya ba da labarin cewa farar cinye shuka take yi baki É— aya ta bar filin banza. Bayan haka kuma, ya ba da labarin cewa sau biyu farar na zuwa Æ™ asar Kano. Zuwanta na farko da rana ne, na biyu kuwa ta kewaye garin Kano domin ta bayan gari ta shigo amma bai fa É— i a wane lokaci ta zo ba. Haka kuma ya bayar da labari cewa farar ta faro wajen garin Ibadan (Badun) kafin ta kawo Kano. Ya fa É— i cewa idan ta sami masara da dawa da gero ba ta barin ko É— aya cinyewa take yi. A Æ™ arshe sai da aka koma ro Æ™ on Allah ya magance wannan matsala, ya ku É“ utar da su daga sharrin wannan fara. Daga cikin wa É— anda suka yi ro Æ™ on akwai Sarkin Kano na wancan lokaci, wato shekarar 1942 domin farar ta zo a wannan shekara ne.

     Mabu É— in Wa Æ™ a

    An bayyana ma’anar mabu É— i da cewa yana nufin abin da ake amfani da shi don bu É— e kwa É— o ko wani abu. Mabu É— in da takardar ke magana a nan shi ne na bu É— e wani abu, kuma abin shi ne wa Æ™ a. A harshen ingilishi ana kiran mabu É— in wa Æ™ a opening dexology. An lura da marubutan sun yi amfani da mabu É— i iri É— aya a wajen fara wa Æ™ o Æ™ insu. Kowannensu ya fara da ambaton sunan Allah a matsayin abin da ya fara wa Æ™ arsa da shi. A wa Æ™ ar ‘Fara Dindi É“ a’ ga abin da fasihin ya fara da shi:

    1. Na ro Æ™ i Allah Jalla don shi ya’ iya,

         Shi yi min fasaha za ni wa Æ™ at dindi É“ a.

     

    2. Sarki Karimun Wahidun mai É— aukaka,

    Ya É— auke yunwa ya azo muna dindi É“ a.

    Marubuci wannan wa Æ™ a ya fara da ro Æ™ on Allah ganin irin matsalar da suka sami kansu a ciki. Muhallis shahid a nan shi ne ambaton sunan Allah a wurin fara wa Æ™ a. Ya yi anfani da sunayen ubangiji guda hu É— u a cikin mabu É— in wa Æ™ arsa da suka ha É— a da Allah da Jalla da Karimun da kuma Wahidun kuma babu mutum É— aya mai suna irinsu. Wannan girmama Allah ne tare da sanin shi ya dace a kira a duk cikin halin da ake, na yalwa ko tsanani.

    Haka shi ma marubucin wa Æ™ ar ‘Farar É— ango’ ya bu É— e tasa wa Æ™ a da ambaton Allah tare da ro Æ™ on ya da É— a tsira ga Annabi Muhammadu (S.A.W.) da alayensa da kuma sahabbansa. Ga yadda mabu É— in wa Æ™ arsa yake:

    1.   A ya Allahu salli alan Nabiyyi,

    Rasulullahi Annabi aljawadu.

     

    2.   Wa salli wa sallama ya Rabbi farda

    Ala ashabihi addal jaradu.

     

    3.   Ilahiy khali Æ™ i ad’uka fa Æ™ bal,

    Du’a’iy wabtahaliy ya Jawadu.

    Shi ma wannan marubucin ya bu É— e wa Æ™ arsa da sunan Allah ta fuskar ro Æ™ o kamar yadda marubucin wa Æ™ ar ‘Fara Dindi É“ a’ ya yi. Ya ambaci sunayen ubangiji guda hu É— u da suka ha É— a da Allah da Rabbi farda da Khali Æ™ i da kuma Jawad.

    Ha Æ™ i Æ™ a marubutan sun bu É— e wa Æ™ o Æ™ insu da mabu É— in da ya dace, wato farawa da sunan Allah tare da neman agaji daga gare shi dangane da matsalar da ake fuskanta a wannan lokaci. Wannan ya Æ™ ara nuna cewa marubutan malaman addinin Musulunci ne. A kan haka ana iya cewa wa Æ™ o Æ™ in na da mabu É— i iri É— aya ta fuskar abin da aka hango a cikinsu na farawa da ambaton Allah da yin salati ga fiyayyen halittu, Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

    5.3 Addu’a

    Ita ma kalmar addu’a ta sami masana da manazarta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anarta. Wasu sun ce addu’a na nufin ro Æ™ on Ubangiji ( Ƙ amusuna Hausa, 2006:3). Har yanzu an sami wasu sun ba da ma’anar addu’a inda suka ce: Bergery (1934:5), ya ce kalmar addu’a na nufin ro Æ™ on da ake yi bayan wanda ake yi a lokacin salloli biyar na wuni. Sai dai an ba da ma’anar ne a Turanci. A cikin Æ™ amusun Nicholas Awde (1996:2) cewa aka yi, Addu’a na nufin prayer, prayer kuma na nufin addu’a. A cikin littafin Hausa Metalanguage cewa aka yi, addu’a na nufin doxology (1990:56).

    An lura da dukkan marubuta wa Æ™ o Æ™ in sun yi amfani da kalamin addu’a a cikin wa Æ™ o Æ™ insu. Marubuci wa Æ™ ar ‘Fara Dindi É“ a’ ga wuraren da ya yi nasa addu’o’i kamar haka:

    1.   Na ro Æ™ i Allah Jalla don shi ya’ iya,

    Shi yi min fasaha za ni wa Æ™ at dindi É“ a.

     

    64. Ya Allah na ro Æ™ e ka kai muna gafara,

         Na san hukunci na tafowar dindi É“ a.

     

    67. Allah shi gafarce mu domin Annabi,

         Ba ni ka É— ai ba dukkan musulmi bakke É“ a.

    Maharazu ya ro Æ™ i Allah ya ba shi fasahar yin wa Æ™ ar fara dindi É“ a domin shi ne gwani wanda yake gagara misali wanda ya fi misali. Haka kuma ya ro Æ™ i Allah ya yafe musu laifukan da suka aikata har aka jarrabe su da fara wadda ta zama sanadiyyar shiga matsalar rashin abinci har yunwa ta zo. Ya Æ™ ara da ro Æ™ on Allah ya gafarce su domin darajar Annabi (S.A.W.) inda ya nuna ba shi ka É— ai ba, dukkan musulmin duniya baki É— aya.

    A cikin tasa wa Æ™ a, Sheikh Atiku Sanka ya yi addu’o’i da dama domin samun mafita ga sharrin farar É— ango. Ga É— an misali domin wuraren da ya yi addu’o’in na da yawa:

    6. Ilahiy wahidun, samadun, Æ™ adirun,

         Ƙ ina ya rabbana É“ arnar jaradu.

     

    7. Ilahiy kulluna narju najatan,

         Ƙ ina ya rabbana fitinar jaradu.

     

    8. Muna ro Æ™ o cikin birni da Æ™ auye,

         Ya Æ™ inallahu min sharril jaradu.

    Ba a nan ka É— ai ya tsaya da addu’o’insa ba, idan aka duba a baiti na 65 zuwa na 85 duk addu’o’i ne na neman Allah ya É— auke musu fitinar farar da aka aiko musu saboda laifukan da suke aikatawa dare da rana. Ya ro Æ™ i Allah da abubuwan da suka dace a ro Æ™ e shi da su, kasancewarsa malamin addini, irin siffofinsa ma É— aukaka da sunayensa masu tsarki da darajar Annabi Muhammadu da sahabban Annabi baki É— ayansu. Ya yi wannan domin Allah ya yaye musu fitinar da aka jarrabe su da ita, ta fara. Akan yi addu’a don gudun faruwar, to ina ga ta faru?

    Dalilin Zuwan Farin

    Marubuta wa Æ™ o Æ™ in sun fa É— i dalilin da ya haddasa zuwan wannan fara a wuraren da suka kai hari. Malam Maharazu Kwasare ya kawo dalilin wanzuwar farar kamar haka:

    64. Ya Allah na ro Æ™ e ka kai muna gafara,

         Na san hukunci na tafowar dindi É“ a.

     

    65. Wa Æ™ atin da sa É“ on namu yay yi yawa Æ™ warai,

         Sababin abin nan sai a sa muna dindi É“ a.

    Malam Maharazu Barmu ya kawo dalilin da ya sanya fara ta zo musu a cikin baitoci biyu da ke sama. Sanin sun yi wa Allah ba daidai ba ya sanya shi farawa da ro Æ™ on gafarar Allah da sauran mutane baki É— aya, tare da bayyana cewa zuwan wannan fara hukuncin Allah ne sakamakon ayyukan da suka aikata marasa kyau. A baiti na 65 marubucin ya fa É— i gaskiyar cewa yawan aikata ayyukan sa É“ o ne dalilin da ya sanya aka aiko musu fara domin ta gyara musu zama, mai hankali ya shiga taitayinsa. Cikin hukuncin Allah aka samu marubucin ya gano dalilin da ya sanya aka aiko musu fara a matsayin jarrabawa. Wannan maganar ta yi daidai da ayar da Allah ya ce “Ba za mu musanya ni’imar da muka yi wa mutane ba face sai sun sauya ta da hannunsu”.

    A É“ angare É— aya ma irin wannan dalili ne Sheikh Atiku Sanka na Kano ya kawo inda yake cewa:

    42. Ku san sababin zuwanta shina gare mu,

         Fa in kun so ku daina kisan jaradu.

     

    43. Ta’ala (layugayyiru ma bi Æ™ aumin),

         Fa É— ar Allah Ta’ala mai jaradu.

     

    44. Ta’ala ya hana mu ga aika sa É“ o,

         Fa mu ko mun Æ™ iya, ya aiko jaradu.

     

    45. Muna aikin da ba shi da kyau jiharan,

         Ta Æ™ a Æ™ a za mu kasa ganin jaradu?

     

    46. Mu samu haram mu ci shi muna ta murna,

         Ta Æ™ a Æ™ a za a kasa sako jaradu?

    Shehin Malami Atiku Sanka ya kawo dalilan da suka haddasa zuwan fara a Æ™ asar Kano ta inda ya ce sababin zuwanta yana gare su. Ya ce , Allah ba ya sauya ni’imar da ya yi wa mutane har sai sun sauya ta da hannunsu, wato ta hanyar aikata ayyukan da aka hane su. Ya Æ™ ara da cewa yawan aikata ayyukan sa É“ o barkatai ke janyo irin wa É— annan musibu ga al’umma. Hasali ma ana aikata ayyukan da ba su da kyau a bayyane ba tare da jin kunyar Allah ba balle mutane. Æ™ are da Æ™ arau ma Allah ya yi hani daga aikata ayyukan sa É“ o, amma mutane sun Æ™ i hanuwa sai abin da rayukansu ke so suke aikatawa. Ya kawo misalin cin haramun da jama’a ke yi tare da murnar an sami banza da dai sauran laifuka barkatai da ake aikatawa. Ba wa É— annan ka É— ai ba, malamin ya kawo abubuwa da dama da ke haddasa Allah ya jarrabi al’umma sanadiyyar ayyukan sa É“ on da suke aikatawa. Idan aka lura malaman sun kawo dalili iri É— aya da ya sabbaba zuwan fara a Æ™ asar Sakkwato da Kano.

    Ayyukan Farin

    Dangane da ayyukan farin har yanzu akwai kama da juna tsakaninsu abin da marubutan suka fa É— a. Marubutan sun zayyano ayyukan farin da fuska É— aya. Za a ga haka idan aka shiga cikin wa Æ™ o Æ™ insu kamar haka:

    Malam Maharazu Barmu Kwasare ya fa É— i ayyukan fara dindi É“ a a cikin wa Æ™ arsa kamar haka:

    4.   Ita ba haki taka ci ba mi taka yi da shi?

         Sai dai hatci suwa a’ abincin dindi É“ a.

     

    6. In ta ga gero ba ta cin dawa ita,

         Farar ga ha’ iko takai muna dindi É“ a.

     

    18. Ta gayyato fari iri da iri duka,

         Sun taimake ta tana ta sharri dindi É“ a.

    A baitocin da ke sama Maharazu ya kawo ayyukan fara dindi É“ a inda ya ce hatsi take ci ba hakin banza ba. Haka ma idan ta ga gero ba ta cin dawa. Ba wannan ka É— ai ba, gayyato sauran fari da ba su yin É“ arna a da domin su taya ta yi wa mutane É“ arna na daga cikin ayyukanta. Maharazu ya fa É— i garuruwan da farar ta bi ta yi É“ arna sosai a cikin wa Æ™ arsa, wanda yin É“ arnar shi ne aikin farar. Misali, daga baiti na 19 zuwa 42 marubucin ya kawo garuruwan da farar ta biya kuma ta yi musu É“ arnar hatsi babu kyau. Ga É— an misali kamar haka:

    22. Ta yo ma Gobir gobara ga hatsutsuwa,

         Da isarta Isa kamar jihadi dindi É“ a.

     

    23. Ta more Moriki ba su more mata ita,

         Hakanan Maradun biyan bu Æ™ atar dindi É“ a.

    Duk wannan babu abin da yake nunawa sai zagayen da farar ta yi a garuruwan Æ™ asar Sakkwato tana É“ arna ga hatsin jama’a. Haka kuma, babu garin da suka yi murnar zuwanta saboda cutar da take yi musu. A ta Æ™ aice, ayyukan farar shi ne cutar jama’a ta fuskar cinye musu cimakar damana a gonakinsu.

    Shi ma marubucin wa Æ™ ar farar É— ango ya fa É— i ayyukan farar É— ango a cikin wa Æ™ arsa kamar haka:

    17. Idan ta sauka shuka duk ta cinye,

         Ta bar fili a banza aljaradu.

    A cikin baitocin da Malam Maharazu ya bayyana ayyukan fara dindi É“ a shi ma Shehin Malami Atiku Sanka haka ya yi a cikin baitin da aka kawo. Don haka farar É— ango da fara dindi É“ a aikin da suke yi wa jama’a na cuta ta fuskar cinye musu shuka/hatsi iri É— aya ce. A nan za a fahimci ayyukan farin iri É— aya ne domin cinye hatsin jama’a da suke yi su bar filin banza. Cinye shukar da jama’a suka yi a lokacin damina a bar ko’ina tamkar fa Æ™ o na sabbaba yunwa kamar yadda sha’iran suka ambata a cikin wa Æ™ o Æ™ insu. Masu karatu da sauraro sun san cewa Æ™ arshen alewa Æ™ asa, domin duk wurin da shuka ta sami matsala babu zancen samun hatsi. Wannan na nuni ga dukkan alamu yunwa za ta maye baya a sanadiyyar rashin samun hatsi lokacin damina. A cikin wannan akwai musharaka tsakanin abubuwan da marubutan biyu suka fa É— a dangane da ayyukan farin da suka wa Æ™ e. Haka kuma wannan ya nuna ayyukan farin illa ne ga al’ummar lokacin da suka zo ko kuma a ce bala’i.

    Rashin Jin Kora

    Abin da aka sani ga al’ada idan aka kori dabba ko tsuntsu ko mutum, ya bar wurin da aka kore shi ya koma wani. Abin mamaki ga wa É— annan fari shi ne ba su jin korar da ake yi musu. Rashin jin korar kuma na nuna aiko su aka yi, ba haka kurum suka zo ba. Wannan na Æ™ ara bayyana wa jama’a cewa farin runduna ce daga Allah. Marubutan sun fa É— i cewa farin ba su jin korar da ake yi musu domin su tashi su bar wurin da suke. Dangane da rashin jin kora ga abin da Maharazu ya ce:

    8. Lalaciya idan ta tafo tcinka akai,

         A fito a kore ba a tcinkan dindi É“ a.

     

    9. Lalaciya in an tsawata to tashi takai,

         Ko ka yi tsawa ba ta tashi dindi É“ a.

    A cikin baitoci biyu da aka kawo Malam Maharazu ya bayyana cewa akan ga sauran fari lokacin da suka zo ga gari, amma ya ce ko an fito a kore ba a tcinkan fara dindi É“ a. A nan farar ta zama tamkar mai duhu/ba-duhu. Muhallis shahid na abin da ake magana shi ne rashun jin kora wanda marubucin ya kawo a baitinsa na tara. Ya ce farar da ake kira lalaciya na tashi idan an yi mata tsawa, amma fara dindi É“ a ba ta tashi ko an yi mata tsawa. A nan ne aka la É“ e aka ce farar ba ta jin kora kuma, haka ne domin marubucin ya fa É— a da bakinsa. Kalmar tsawa da ke cikin baitin na nufin kora domin ba a yin tsawa ba tare da wata manufa ko bu Æ™ ata ba. Manufar da ke sa a yi wa farar tsawa ita ce domin ta tashi ta bar wurin da take. Haka kuma yin tsawar na nuna farar ta bar abin da take yi na cin hatsin jama’a.

    Marubuci wa Æ™ ar farar É— ango ma ya kawo zancen rashin jin kora gare ta kamar yadda mai wa Æ™ ar fara dindi É“ a ya kawo. Ga wurin da ya fa É— i ba ta jin kora:

    10. Tana yawo cikin birni da Æ™ auye,

         Ana korar ta ba ta ji jaradu.

     

    15. Da fara ko ta zo yara da manya,

         Fita gona ake tashin jaradu.

    Idan aka yi la’akari da baiti na goma da ke sama akwai kamannu sosai tsakanin maganar Maharazu da Shehin Malami Atiku Sanka dangane da rashin jin kora ga farin da suka yi wa wa Æ™ a. A cikin wa Æ™ ar farar É— ango kalmar jaradu da marubucin ya yi amfani da ita na nufin fara a harshen Larabci. Kalmar tsahin jaradu na nufin koran fara.

    Yawan Layuka a Baitin Wa Æ™ a

    Baiti na nufin layukan wa Æ™ a gwauruwa ko ‘yar tagwai ko Æ™ war uku ko’yar hu É— u ko ‘yar biyar ( Ƙ amusun Hausa, 2006:29). A ta Æ™ aice baiti na nufin layi ko layukan da marubuci ya rubuta wa Æ™ arsa da su da yake ambaton yawansu a wasu lokuta a cikin wa Æ™ arsa, kuma ana gane su layi É— aya ne ko biyu ko uku ko hu É— u ko kuma biyar a matsayin baiti. Wani lokaci akan sami Æ™ arin da wasu ke yi wa wa Æ™ o Æ™ in wasu marubuta ‘yan uwansu, amma Æ™ arin ko ya yi tsawo ba ya zarce layi biyar a matsayin baiti. Akan sami mai layi biyu a mayar uku ko hu É— u ko biyar ko mai uku a mayar hu É— u ko biyar, kuma Æ™ arin da sama ake sanya shi. Tare da haka sai a kiyaye da cewa, ba kowane marubuci wa Æ™ a ke iya yin tahmisi ga wa Æ™ a ba. Wata baiwa ce ta daban a fannin rubutacciyar wa Æ™ a. A tunanina tahmisi ya samo asali daga wa Æ™ ar baka wanda ‘yan amshi na Æ™ ari fiye da wanda marubuta ke yi. Idan aka É— auki wa Æ™ o Æ™ in maka É— a Musa ÆŠ an Æ™ wairo Maradun da Yaro na Hore za ga haka (Bayanin marubuci).

    Bisa wannan an sami kwatancen daidaito tsakanin yawan layukan da Maharazu da Atiku Sanka suka gina baitocin wa Æ™ o Æ™ insu da su. Wannan ba ya bu Æ™ atar dogon bayani sai dai a yi na kare da aka ce ana buki a gidansu, sai ya ce ya gani a Æ™ asa. Don haka kawo baitocin kowane marubuci daga cikinsu zai warware matsalar. Ga misalin baitoci biyu na farko na Maharazu:

    1.   Na ro Æ™ i Allah Jalla don shi ya’ iya,

    Shi yi min fasaha za ni wa Æ™ at dindi É“ a.

     

    2.   Sarki Karimun, Wahidun mai É— aukaka,

    Ya É— auke yunwa ya azo muna dindi É“ a.

    A É“ angare É— aya ma an sami haka a cikin wa Æ™ ar Malam Atiku Sanka inda ya ha É— a baitinsa ta yin amfani da layi biyu kamar yadda Malam Maharazu Kwasare ya yi. Ga baiti biyu na farko a cikin wa Æ™ arsa:

    1.   A ya Allahu salli alan Nabiyyi,

    Rasulullahi Ahmadu aljawadu.

     

    2.   Wa salli wa sallama ya rabbi fardha,

    Ala ashabihi addal jaradu.

    Yadda aka kawo a cikin misali, haka dukkan baitocinsu suka tafi da tsarin layi biyu. Wannan ya nuna akwai ala Æ™ a iri É— aya a haujin ginin baitocin wa Æ™ o Æ™ insu.

    Zagayen Garuruwa

    Zagaye a nan na nufin halarta/zuwan da fari suka yi a birane da Æ™ auyuka lokacin da suka zo (Bayanin marubuci takarda). An sami marubutan dukkansu sun labarta cewa farar daga wani wuri ta fito kuma ba ta tsaya wuri É— aya ba. Abin da take yi shi ne ta tafi can, ta koma can, ba wuri É— aya ta tsaya ba. Marubutan sun nuna haka a cikin wa Æ™ o Æ™ insu kamar haka:

    Malam Maharazu Barmu Kwasare ya kawo wuraren da farar ta fara yada zango bayan baro inda ta fito kamar haka:

    19. Ta yo cida ga hatcinmu ta bi ta Acida,

         Ba murna, kowa ba shi murnar dindi É“ a.

     

    20. Wurno wurin nomansu duk ta lullu É“ e,

         Guda, ba wata guda nata sharri dindi É“ a.

     

    21. Ta sa farinta Gwaranyo ta rinyo musu,

         Akadas kadas taw wa Kadassaka dindi É“ a.

     

    A ta Æ™ aice, da Maharazu ya fara lissafo garuruwan da farar ta je bayan ta fara daga garinsu sai wurno da Gwaranyo da garin Kadassaka da Gobir da Moriki da Zurmi da Kaura Namoda da Tcafe/Tsafe, daga nan sai Gusau da Kwatarkwashi da Bungu É— u da É— ansadau da Maru har ta zagayo ta komo Sakkwato. Wannan zagaye ne da ya ha É— a jihar Sakkwato ta da baki É— aya da Zamfara ta yau. Daga baiti na 19 har zuwa na 42 maganar zagayen farar ne kawai Maharazu ya yi, ta fuskar ta je nan, ta je can.

    Malam Atiku Sanka ma bai Æ™ yale ambaton wurin da farar ta fito ba da inda ta kai a cikin wa Æ™ arsa face sai da ya ambace shi. Ga abin da ya kawo a cikin wa Æ™ arsa kamar haka:

    31. Fa tun daga Ikko labari muke ji,

         Fa har ta zo Kano ai aljaradu.

     

    32.Fa tun daga Ikko sai da ta je ta Yerwa,

         Ta je ta ba Æ™ i Æ™ irin ai aljaradu.

    Marubucin ya fa É— i wurin da farar ta faro da wuraren da ta biyo kafin ta iso Kano. Bayan zuwanta Kano ma ta É— an zagayi wasu garuruwan Æ™ asar Kano da dama kamar Rano da awaki da Kura da Gaya da sauransu. Ga misalin zagayen da farar ta yi a Æ™ asar Kano kamar haka:

    20. Sarakin Æ™ auyuka da sunka aiko,

         Suna cewa da Sarki ga jaradu.

     

    21. Su Sarkin Bai, Ciroma sunka aiko,

         Mutan Rano sunka aiko ga jaradu.

     

    22. Dawaki da Kura su ma sunka aiko,

         Mutan Gaya sunka aiko ga jaradu.

     

    23. Ƙ asar birnin Kano duk sunka aiko,

         Suna cewa da Sarki ga jaradu.

     

    24. Ƙ asar Zazzau a can ma ta yawaita,

         Ƙ asa ba a ganin ta fa sai jaradu.

    A cikin wa Æ™ ar Sanka ma an sami gewayen garuruwa da farar É— ango ta yi kamar yadda dindi É“ a ta yi. Wannan na nuna akwai ala Æ™ a ta Æ™ ut-da- Æ™ ut tsakanin wa Æ™ ar fara dindi É“ a da ta farar É— ango ta fuskar zagayen garuruwan da suka yi. Marubucin ya nuna farar ta fito daga Ikko, ta biyo ta Yerwa kafin ta iso Kano. Isowarta Kano ke da wuya sai ta kama zagayen garuruwan Æ™ asar Kano kamar yadda aka gani a cikin baitocin da aka kawo. Wannan na tabbatar da zagayen da aka yi magana a kai.

    Sakamakon Bincike

    Daga cikin abubuwan da binciken ya gano akwai munin ayyukan sa É“ o da mutane ke yi a ban Æ™ asa. Duk abin da Allah ya hana barin aikata shi shi ne alheri. Haka kuma aikata sa É“ o na janyo wa masu aikin matsala kamar yadda ya faru ga al’ummar Æ™ asar Sakkwato da Kano idan aka yi la’akari da abubuwan da marubutan suka bayyana a cikin wa Æ™ o Æ™ insu. Wannan ya sa binciken ya Æ™ ara gano cewa sa É“ on Allah na sa a jarrabi al’umma da wata cutar da ba su sani ba, kuma su kasa gano an kama su da cutar ne sakamakon ayyukan da suka aikata na sa É“ on Allah. Haka kuma binciken ya gano wani na janyo wa wani musibar Allah ba tare da ya ji ko ya gani ba. A kan haka kuma, binciken ya Æ™ ara gano cewa malaman addini mutane ne masu ilmi da hangen nesa inda suke gano sanadin faruwar abu domin sun karanta sun gani. Bayan wannan kuma, binciken ya gano Allah na jarraba mutane da duk abin da yake so ba sai fara ka É— ai ba, domin an jarrabi na gaba da soro da sauran rashin lafiyoyi, wasu ba a ma san kansu ba. Allah ya tsare mu, ya tsare muna don darajar Al Æ™ ur’aninsa.

    Kammalawa

    An rubuta ma Æ™ alar da farawa da gabatarwa inda aka yi tsokaci kan abin da ma Æ™ alar ta Æ™ unsa. An kawo dalili da dabarun bincike inda aka yi bayani gwargwado a kansu. Bayan haka an kawo ta Æ™ aitaccen tarihin marubuta wa Æ™ o Æ™ in da aka yi kwatance tsaknin wa Æ™ o Æ™ insu. Biye da shi kuma, an kawo kwatancen fasahar da aka Æ™ uduri yi tsakanin wa Æ™ o Æ™ in biyu inda aka dubi abubuwan da suka ha É— a da jigo wanda na tarihi ne, wato muhimmin sa Æ™ on da wa Æ™ o Æ™ in ke É— auke da shi da mabu É— in wa Æ™ a da addu’a da dalilin zuwan farin da ayyukansu da rashin jin kora idan an yi korar. Haka kuma an kawo yawan layukan da ke a cikin baitocin wa Æ™ o Æ™ in da zagayen garuruwa da farin suka yi da sakamakon bincike a Æ™ arshe.

    Manazarta

    Al Æ™ ur’ani Mai Tsarki (Fassarar Abubakar Mahmud Gummi)

    Awde, N. (1996). Æ™ amusun Hausa da Turanci da Turanci da Hausa. Hippocrene Books, INC 17 Madson Avenue New York, NY10061

    Bunza, D. B. (2012), Nazarin Diwanin Malam Maharazu Barmu Kwasare, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato. Jami’ar Usmanu É— anfodiyo.

    CNHN, (2006). Æ™ amusun Hausa. Zariya: Ahmadu Bello University Press.

    ÆŠ angambo A (2007). É— aurayar Gadon Fe É— e Wa Æ™ a. Zaria : Amana Publishers Ltd.

    Yahaya, I. Y. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria NNPC.

    Yahya, A.B. (1982) Jigon Nazarin Wa Æ™ a, Fisbas Media Service, Kaduna.

    Yahya, A.B. (2001) “Salo Asirin Wa Æ™ a” . Fisbas Media Service, Kaduna.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.