𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam dafatan kowa lfy Malam Ni ce na sanya
turare mai kamshi asaman kayana tom danaje gidan kanin mamata sai yake min fada
wai hakan bai dace ba infita ina kamshin turare har jama'ar waje suji inason
karin bayani malam Nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu
To ‘yar’uwa ya haramta ga mace Baliga ta sanya turare, ta
fita unguwa, saboda faɗin
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam “Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta
wani majalisi, to ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu dawud ya rawaito.
A wani hadisin kuma yana cewa: “Duk matar da ta sanya
turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu.
Daga Ubaidu Ya ce: "Lallai Abu Hurairata, ya haɗu dawata mata wacce ta
sanya Turare, Sai Yace Mata: Ina kikeson zuwa ne haka Baiwar Allah? Sai matar
tace: Masallaci zanje. Sai Ya ce: Saboda za ki Masallacin ne kika sanya Turare?
Sai matar tace eh, Sai Abu Hurairata Yace Lallai naji Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam Yace "Duk matar da ta sanya turare tafita da nufin zuwa
Masallaci, to Allah mai girma da Ɗaukaka ba zai karbi sallarta ba har saita
dawo ta yi wanka Irin wankanta na Janaba."
{Ibn majah ne ya ruwaito shi acikin KITABUL FITAN babin
Fitnatun Nisa'i (4002)
Malaman Muslunci sun inganta hadisin, Sheik Nasurudden
albany yayi ta'aliqi akan haka, yakara dacewa"Idan har(sanya turare
saboda) zuwa Masallaci yazama Haramun toya (ake tunanin) hukuncinsa zai Kasance
akan wacce ta sanya shi saboda zuwa Kasuwa, titi da kuma hanyoyi? Babu makawa
yin hakan yafi tsananin haramci, Amma ya halatta taci ado maikyau da turare mai
kamshi agidan mijinta da kuma muharranta kamar yanda yazo a Alkur'ani suratul
an-nor (31)
Imam at-taimey yana fada acikin (Az-awajir 36/2) Lallai
fitar mace da za tayi tana mai sanya Turare kuma tana mai kwalliya, yana daga
cikin MANYAN LAIFUFFUKA kuma koda mijinta ne yayi Mata izini, kuma duk Waɗannan Hadisan waɗanda suke nuna haramcin
sanya turare ga mace idan za ta fita waje) baki Ɗayansu sun shafi gaba ɗayan lokuta ne Mukhtasar
Kitabu jalbab Al-mar'atul muslimah (shafi na 44)].
Nassoshin da suka gabata suna haramta sanya turare ga mace
balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin matar aure ba da
budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna gamewarsu ga dukkan mata waɗanda sharia ta hau kansu,
tun da ba’a samu abin da ya keɓance
wasu nau’i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne: saboda yana kaiwa zuwa
tada sha’awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin matar aure da wacce ba
ta yi ba. Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji kamshi, in ta yi
hakan za ta samu lada. Haka ma budurwa, za ta iya sanyawa a tsakanin
‘yan’uwanta mata, ko gaban muharramanta waɗanda
ta san ba za su yi sha’awarta ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.