Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Darussan La’akari a Zababbun Matanonin Adabin Baka Na Hausa

Cite this article: Bunza, U.A., Yusuf, J., Aliyu, A. & Mujaheed, A. (2023). Wasu Darussan La’akari a Zaɓaɓɓun Matanonin Adabin Baka Na Hausa. Zamfara International Journal of Humanities, (2)3, 39-49. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2023.v02i03.005.

Wasu Darussan La’akari a Zaɓaɓɓun Matanonin Adabin Baka Na Hausa

Na

Dr. Umar Aliyu Bunza
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Email: aliyu.bunza@udusok.edu.ng
Phone No: +2347063532532

Da

Jibril Yusuf
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna
Jami’ar Jihar Kaduna
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone No: +2347030399995

Da

Abdulrahman Aliyu
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Email: ksarauta@gmail.com
Phone No: +2348036954354

Abstract

This paper focused on the study of Hausa Orature as a tool for emparting knowledge to contemporary society. Hausa Orature as component of Hausa literature constitutes an indepth knowledge which can serve as reference points in building a better society yet, researchers in this century gives little considerations in analysing such angle. The medology used in the analysis includes consultation of books and online sources, and citing examples from the folktales, epics, stories and other related literature with oral sources. The study shows how How Hausa Orature constitutes knowledge for the betterment of the society today and in the future generation.

Tsakure

Manufar wannan takarda ita ce nazarin labarun bakan Hausawa a matsayin taskar ilimi ga al’ummar yau. Nazarin yana da muhimmanci ne ganin labaran baka kamar sauran nau’o’in adabin bakan Bahaushe, ɗamfare suke da ilimin da zai iya zama madogara ga al’umma, amma duk da haka manazarta ba su faye ba su muhimmanci ba a wannan ƙarnin. Hanyyoyin da aka yi amfani da su wajen gudanar da binciken sun haɗa: karance-karance a littattafai da kuma yanar gizo tare da zaƙulo labaran da kuma yin nazarinsu. A ƙarshe, takardar ta gano cewa, labarun bakan Bahaushe suna da matuƙar muhimmanci, musamman wajen bayyana tunani da dabarun rayuwar al’ummar da ta gabata domin kasancewa madubi ga al’ummar yau.

Fitilun Kalmomi: Darussa, La’akari, Zaɓaɓɓu, Matanoni, Adabin Baka

1.0    Gabatarwa

Labarun baka nau’i ne na adabin baka na Hausawa. Labaru ne da ake ƙirƙirar su a ka, a wanzar da su da fatar baki, kuma a adana su a ka. Da yake adabi tamkar madubi ne da ke nuna yadda rayuwa ke gudana, mai taimaka wa mutum ya ƙaru da ilmin jiya domin gyaran yau tare da daidaita makomar gobe. A wannan takarda an mayar da hankali kan labaran baka, domin rarabe aya da tsakuwa a kan abin da ya shafi muhimmancin labaran na baka wajen taskace ilimi ga al’ummar yau. Nazarin, ya shafi tsokaci ne kan yadda labarun baka suka kasance a matsayin taskar ilimi ga al’ummar yau. An yi nazarin ne ta hanyar fito da batutuwan da suka shafi tarihi da sana’o’i da fasaha da kimiyya a cikin labarun. Sannan aka fayyace yadda labaran za su iya kasancewa hanyar gina rayuwar gobe, musamman ta fuskokin sadaukar da kai da taimakon juna da aikin gayya da makamantansu. Daga ƙarshe an kawo jawabin kammalawa da manazarta.

2.0 Ma’anar Labaran Baka

Masana irin su Ɗangambo, (2008) da Yahaya, da wasu, (1992); da sauransu, sun nuna cewa labaran baka , su ne labaran da Hausawa suka gada daga kaka da kakanni. Wato sun kalli labaran baka a matsayin nau’in adabi wanda ke ɗauke da zantuttuka gajeru ko dogaye na hikima waɗanda ke koyar da wasu darrusa. Ke nan, labaran baka, zance ne na hikima da ake shiryawa cikin azanci da yake zuwa kara zube, kuma yake wanzuwa ta hanyar magana; zance ne mai ɗan tsawo wanda kuma yake ɗauke da dabarun zaman duniya ta hanyoyi da matakai daban-daban. Babbar hanyar isar da su ita ce kunne-ya-girmi-kaka.

Haka kuma, labaran baka sun kasance ayyuka ne na fasaha da suka shafi sarrafa harshe da kaifafa tunani daga cikin rayuwar al'umma ta yau da kullum. Labaru ne da aka fara samar da su tun zamanin gargajiya, wato zamanin da Bahaushe ba shi da wata takamammiyar hanyar rubutu. Ke nan, a ka, ake adana su. Kuma da fatar baki ake bayar da su.

2.1   Ire-iren Labaran Baka

Labaran baka zance ne na hikima da ake shiryawa cikin azanci da yake zuwa a kara zube, kuma mai ɗan tsawo, mai kuma ban sha`awa da koyar da dabarun zaman duniya ta hanyoyi da matakai daban-daban. Labarun baka sun haɗa da tatsuniya da almara da ƙissa da hikaya da tarihi da tarihihi. Haka kuma akwai guntattakin maganganu na hikima kamar kirari, da karin magana, da kacici-kacici, da zaurance, da salon magana da dai sauransu. Bari mu kawo bayanin wasu daga cikinsu:

2.1.1        Tatsuniya

Masana da dama sun daɗe suna kallon tatsuniya ta fuskoki daban-daban, (Gusau, 2006) cewa ya yi “tatsunniya wani tsararren labari ne wanda magabata (musamman tsofaffin mata) suke shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da raha ga rayuwa da kuma cinye dare”.

Tatsuniya makaranta ce ta Hausawa wadda ta nan ne suke ilimantar da `ya`yansu tare da koya masu dabarun zaman duniya tun kafin su sadu da baƙin al’umma. Ta amfani da tatsuniya, Hausawa kan kaifafa tunanin `ya`yansu. Har ila yau, tsofaffi ne kan shirya tatsuniya, domin ilmantarwa ga yara. Ana buɗe tatsuniya ne da ‘Ga ta nan ga ta nan ku’ a rufe kuma da ‘Ƙurungus’. Galibi an fi yin tatsuniya da dare, in kuwa za a yi da rana to sai an ɗaure gizo.

2.1.2        Almara

Almara ita ce hanyar gabatar da wasu matsaloli kara-zube ko kuma ta hanyar labari, sannan a buƙaci mai sauraro ya bayar da amsa ko kuma ya zaɓa tsakanin abubuwan da aka ambata. Gusau, (1995), yana ganin almara wani shiryayyen labari ne na jawo hankali da ake bayarwa don kaifafa tunanin masu sauraro ko nishaɗi. Saboda haka almara ba ta fiye tsawo sosai ba, sai dai takan ƙunshi wani abu na ban dariya ko ƙalubalen da za a nemi mai sauraro ya warware. A taƙaice, almara labari ne ƙirƙirarre wanda ba lalle ne ya auku ba.

Tun kafin Hausawa su haɗu da Larabawa suna da ire-iren waɗannan labaru na ban dariya da sa nishaɗi. Misalin almara ta kaifafa tunani ko wasa ƙwaƙwalwa ko auna fahimta, wato mai buƙatar sai an yi tunani kafin a bayar da amsa, ita ce;

Wasu adadin tsuntsaye ne a sama, da kuma wasu a ƙasa. Sai na sama suka ce wa na ƙasa da ɗaya daga cikinku zai hawo sama da adadinmu ya zama daidai. Su kuma na ƙasa suka ce wa na sama da ɗaya daga cikinku zai sauko ya haɗu da mu, da adadinmu ya ninka naku. Shin tsuntsaye nawa ne a sama kuma nawa ne a ƙasa ?

Akwai kuma almara ta dabara mai buƙatar ka amsa tambayar in kai ne yaya za ka yi ? Wato mai ɗauke da ɗaurin gwarmai da ake buƙatar ka kwance. Misali:

Mutum ne yake tafiya tare da akuya da kura da dawa. Sai ya zo tsallake ruwa, kuma kana da damar tsallakawa tare da abu ɗaya ne kawai cikin ukun da kake tafe da su sannan ka dawo ka ɗauki sauran biyun, ɗaya bayan ɗaya ba tare da ka bar wani ya cutar da ɗaya ba. Ga shi kuma kura tana iya cutar da akuya, akuya kuma tana iya cutar da dawa. In kai ne ya za ka yi ka tsallaka da su?

Akwai kuma almara ta barkwanci wadda takan ƙunshi wasannin tsakanin ƙabilu ko garuruwa ko sana’o’i ko dangantaka da sauransu. Ta haka ne ake ƙirƙirar labaru iri-iri da suke nuna rashin wayo ko gidadancin abokin wasan, lamarin ba ya kai wa ga faɗa sai dai raha kawai. Misali, tsakanin Fulani da Barebari ko tsakanin Kanawa da Zazzagawa, da sauransu. Misalin irin wannan almara ta barkwanci ta ƙunshi waɗannan:

i.        Wai Bafulatani ya ga biri ya ƙura masa ido, aka tambaye shi ko me ya sa yake kallon birin, sai ya ce ; Baffa sak !”.

ii.      Bayerabe yana cin sabulu yana yamutsa baki ba daɗi, shi ya ɗauka abin ci ne. Da aka tambaye shi ya aka yi? Sai ya ce; “kudina ina ci.”

2.1.3        Hikaya

Hikaya labari ne da ake bayarwa da ya faru dangane da mala`iku, ko aljannu ko mutane ko rauhanai ko dabbobi ko tsuntsaye ko kuma ƙwari. Wani lokaci kuma takan ɗauki yanayin ƙago wasu labaran don ƙarin bayani kan wani abu ko kwaikwayon sa. Hikaya labari ne na manyan mutane, ba annabawa ba, da abin da ya faru gare su. Misali, hikayar wani halifa ko sahabi ko wani babban sarki. Hikaya kuma, takan ƙunshi wani abin mamaki da ya auku ko kuma dai wani labari mai koya darasi ga zaman duniya (ko ma amfanin lahira). Hikaya kuma tana iya zama ta wani attajiri ko kuma dai wani labari mai koya zaman duniya dangane da yadda mutum zai iya bakinsa, (Ɗangambo, 2008). Misali hikayar kunkuru da gauraki da sauransu.

2.1.4        Ƙissa

Ita dai wannan kalma tana ɗauke da ma’anoni biyu a cikin harshen Larabci. Wato ma’ana ta lugga da kuma ta zahiri. A luggance, ƙissa na nufin bibiya ko ƙididdigewa. Wato mutum ya bi diddigin wani abu har zuwa ƙarshensa (Sabe, 2011:43).

A ma’ana ta zahiri kuwa, kalmar ƙissa na nufin ba da labari dangane da mutanen da suka shuɗe, ko kuma ba da labarai a kan waɗansu abubuwa da suka auku a da. Watau wani labari da yake kara zube wanda ya danganci rayuwar wasu magabata wanda ake cirowa daga cikin Alƙur’ani mai girma. Wato bayanai a kan rayuwar Annabawa da Sahabbai da wasu Waliyyai waɗanda Allah (SWT) ya kawo labarinsu cikin Alƙur’ani. Ana kuma samun ƙissa ta akasin mutane na gari kamar su Fir’ana da Ƙaruna da sauransu. A taƙaice ƙissa wata hanya ce ta cusa wata manufa cikin zukatan masu saurare (Sabe, 2011:43).

A ɓangare ɗaya kuma akwai ƙissar Bahaushe. Ita wannan ita ce ƙissar da aka gina ne bisa tunanin Bahaushe, wato ga yadda labarin yake a zahiri, amma a ƙara masa wani abu ko dai don daɗin labarin ko kuma domin a ƙara ƙayatar da mai sauraro. Bisa ga wannan sai aka raba ƙissar Bahaushe zuwa gida biyu, wato issar cinye dare wadda ta ƙunshi labarai da zantuttukan da mutane suke yi don cinye darensu kawai. Akwai kuma ƙissar addini wadda ta ƙunshi labarai ne da ake tsarawa a kan wani abu da ya auku na addini a lokacin Annabawa da Sahabbai da waliyyai da shaihunnai da sauransu (Sabe, 2011:44).

2.1.5        Tarihi/Tarihihi

Shi dai tarihi dai yana nufin wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma. To, amma shi tarihihi za a iya cewa, wani labari ne na wasu abubuwa da suka taɓa wakana na haƙiƙa a cikin al’umma, sai dai irin wannan labarin yana cakuɗe da wasu abubuwan da ba a tabbatar da faruwarsu ba. Don haka idan aka ce tarihihi, a taƙaice ana nufin gurɓataccen tarihi, wanda aka cakuɗa shi, a tsakanin abin da ya faru na haƙiƙa da wanda bai faru ba (Sabe, 2011:45).

Ana ƙirƙirar tarihihi a matsayin labari a ka, kuma a adana shi a ka, akan sami sauye-sauye saboda tsawon zamani wajen wanzar da shi daga al`umma zuwa ga wata al`ummar. Wannan dalili ne ya sa mutane ke ganin ba abin mamaki ba ne don an sami ƙarya a cikin tarihihi. Tarihihi, ya ƙunshi labarai ne na kunne-ya-girmi-kaka, waɗanda ba a iya tabbatar da haƙiƙanin aukuwarsu ba. Kuma labarai ne da suka ƙunshi abubuwan da suka danganci rayuwar Hausawa, musamman a jiya, akwai tarihihi kala-kala a ƙasar Hausa sai dai waɗanda suka yi tashe sun haɗa da taririhin Bayajidda da tarihihin Sarkin Katsina Korau da tarihihin Wali Ɗanmarina da Wali Ɗan Masani ko wani ɓangare na tarihin Usman Ɗanfodiyo ko Ɗanwaire da makamantan su (Sabe, 2011:45).

Duk wanda ya duba ɗaya daga misalin da aka bayar zai fahimci labarai ne masu ƙunshe da gaskiya da ƙarya duk a cikinsu, wato wani ɓangare na labarin ƙarya ce wani kuma akwai alamun gaskiya.

3.0 Labaran Baka a Matsayin Taskar Ilimi ga Al’ummar Yau

Tabbas! Labarun bakan Bahaushe wata makaranta ce mai zaman kanta, ko kuwa ana iya bayyana su a matsayin taskar ilimi ga al’ummar wannan zamanin musamman idan aka nazarce su don ganin irin ƙunshiyar da suke ɗauke da ita, domin kuwa cike suke da hikima da basira da kuma tunani irin na ɗan’Adam wanda ya ƙirƙira kan wani abu, ya kuma aiwatar da shi ta fatar baki, domin yaɗa wata manufa don koyarwa ko kuma hannunka-mai-sanda ko kuma don samun nishaɗi a tsakanin al’umma musamman ƙananan yara. Haka kuma labaran bakan Bahaushe ba su tsaya kan nishaɗi kaɗai ba, akan yi amfani da su don koyar wa yara da nusar da su ko zaburar da su ko kuma yin amfani da labaran dom kaifafa tunani ga yaran. Wataƙila wannan shi ne dalilin da ya sa labaran suka ƙunshi kusan kowane fanni na rayuwa da zamantakewar al’umma.

Ta la’akari da waɗannan bayanai da aka kawo a sama, an a dubi waɗansu batutuwa don ganin yadda tasirinsu ya fito a cikin labaran bakan Bahaushe. Batutuwan sun haɗa da: kimiyya da fasaha da tarihi da sana’o’in Bahaushe da ma wasu waɗanda a cikin su ne za a kafa hujjojin da za su tabbatar da kasancewar labaran a matsayin taskar ilimi ga Bahaushen jiya, har ma da na yau idan lokaci ya ba da dama. Mu je zuwa!

3.1  Tarihi

Tarihi wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma (Sabe, 2011:45). Ke nan, tarihi taska ce mai ƙunshe da rayuwar da ta gabata, inda ake fasalta yau da kuma hasashen yadda gobe za ta kasance. Wasu daga cikin labarun bakan Bahaushe sun kasance ƙunshe da tarihin al’ummar ƙasar Hausa da wasu maƙwaftansu, ko kuma wasu al’adu nasu waɗanda sun shuɗe. Labarin Gardamar Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina ya baje mana wannan fasali a faifai:

Gardamar Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina

Wata rana gardama ta kaure tsakanin wani mutum da matarsa kan ganin watan Azumi. Mijin ya ce yau ne watan zai tsaya, matar kuma ta ce sai gobe. Suka tashi suka iske Wali Ɗanmasani domin neman fatawa, suka tarar yana zaune tare da sauran almajiran Wali Ɗanmasani.

Wali Ɗanmasani ya ce yau ne wata zai tsaya. Shi kuwa Wali Ɗanmarina wanda yake almajirin Malamin ne, cikin ladabi da girmamawa ya ce gobe wata zai tsaya. Daga nan sai gardama ta koma tsakanin malami da ɗalibinsa.

Da yamma ta yi lokacin duban wata, jama’a suka taru a unguwar malamai domin ganin yadda al’amarin ganin watan zai kaya. Kowa ya ɗaga kai sama yana duban ko wata zai tsaya.

Da aka ɗauki lokaci, sai Wali Ɗanmasani ya shiga gida ya sami sakaina ya feƙe ta daidai tsayuwar wata. Ya jefa ta sama, sai ta manne. Mutane suka ɗauki kuwwa malam ya yi kaye.

Shi kuma Wali Ɗanmarina da ganin haka ya gane sakaina ce, sai ya tashi tsaye, ya miƙa hannunsa ya ce sakaina ta faɗo. Kafin ka ce kwabo, sai ga sakaina a tafin hannunsa. Sai kuwa kuwwa ta sake ɓarkewa.

Wali Ɗanmasani ya ji sabuwar kuwwa, sai ya fito ya ga dalilinta, ya iske sakaina a hannun almajirinsa. Da ganin haka sai ya ce wa almajirin nasa, ‘‘Bayan mutuwarka babu mai sanin ɗaya daga cikin danginka.’’ Shi kuma Wali Ɗanmarina ya ce masa, ‘‘Kai kuma babu mai sanin kabarinka, ko waɗanda suka rufe ka.’’ Haka kuwa lamarin ya kasance, babu wanda ya san ɗaya daga cikin dangin Wali Ɗanmarina bayan mutuwarsa, haka kuma babu wanda ya san inda kabarin Wali Ɗanmasani yake bayan mutuwarsa, (Bunza, 2012:9-10).

Ko ba komai wannan labari ya nuna wani ɓangare na tarihin waɗannan mashahuran malamai da aka yi a ƙasar Katsina. Wannan ya sake jaddada yadda labarin baka ke ɗamfare da tarihin al’umma. Haka kuma labarin Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina sun nuna irin baiwar da Allah Ta’ala ya yi cikin ƙasar Katsina, ya raya wasu bayinsa da tarihinsu bai ɓacewa har abada (Bunza, 2012:13.

3.2   Sana’o’i

Dangane da ma’anar sana’a, a cikin Ƙamusun Hausa na CNHN (2006:186) an bayyana sana’a ko sana’o’i da cewa: Aikin da mutum yake yi don samun abinci, misali manomi sana’arsa noma, wanzami kuwa sana’arsa aski ne. Saboda haka, sana’a hanya ce ta neman abinci ga mutum. Kowace al’umma tana da sana’o’in da take yi don samar da abinci da sauran kayan buƙata (Bunza, 2015:130). Daga cikin labarun bakan Hausawa akwai waɗanda suka fito da irin sana’o’in da Bahaushe yake da su tun can azal, waɗanda suke ƙunshe da bayani kan waɗannan sana’o’in, wanda hakan ke nuna cewa tun can da Bahaushe ba ci-ma-zaune ne ba. Shi ya sa wasu labarun baka suna ƙunshe da bayani kan wasu sana’o’i na wasu al’ummomi da kuma nuna muhimmancin sana’ar ga rayuwa. Misali, a labarin:

Basha Jagora

An nuna cewa akwai wasu mutane da suke zaune a dajin tsakanin Bidda da Kwantagora waɗanda ba su da wata sana’a sai farauta da neman zuma. Ta wannan sana’a tasu ta neman zuma suka waye da tsutsuwa ‘Basha’ wadda take jan su zuwa wurin da ke da zuma. A hankali har ta fara kai su mahallaka. Ta kai mutum ɗaya ga zakanya mai ɗiya ta kashe shi. Ta ja na biyu, ta kai, Allah ya kare shi, ya kashe zakanyar. Daga wannan lokaci mutane suka nemi layar zana, suka kuma riƙa shiga daji da kwari da baka (Bunza, 2015: 130).

Wannan labarin ya nuna yadda wasu mutanen da ke maƙwaftaka da ƙasar Hausa suke gudanar da sana’arsu. A ɗaya ɓangaren kuma an nuna muhimmancin shiri a duk al’amarin da za a sa gaba na fita nema, musamman dabarun kare kai daga hare-haren mugayen halittu.

Bugu da ƙari, idan aka yi la’akari da labarin Bakatsine Mai Kan ƙwarya, ko da yake akwai ɓurɓushin wauta-wauta a cikinsa, amma ya fito da irin zaman mutanen Katsina mazajen tsaye ga riƙon sana’a domin kore wa bakinsu ƙuda da hana wa kansu zama ci-ma-kwance, ‘yan ku-ci-ku-ba-mu. Wannan ya sa ɗan alewa ya jajirce da ɗaukar masakin alewarsa yana yawo gari-gari yana tallatawa (Bunza, 2012:12), har dai ‘tsautsayi’ ko ‘wauta’ ta sa bayan ya sha fura ya kwanta bacci a inuwa garin magagin bacci kansa ya shige ƙwaryar alewa ya maƙale saboda danƙo. Ƙarshe dai sai da aka yi jidali kafin aka cire masa bayan ya farka daga bacci, (Bunza, 2012:4-5).

3.3  Falsafar Bahaushe

Falsafa hanya ce ta tunani da ƙoƙarin samun bayanin dukkan al’amurra da suka shafi duniya da ɗan’Adam da inda suka sa gaba (Dunfawa, 2013). Ke nan, falsafa wani tsarin ilmi ne mai alaƙa da imani, da tataccen tunani mai zurfi a kan al’amarin rayuwa da halita, da duniya, da kuma nazarin halayyar wani. Labarun baka na Bahaushe suna haska mana irin falsafar Bahaushe, wato tunaninsa game da duniya, da yadda yake kallon duniyar da halittun da suke cikinta. Misali, Bahaushe yana alaƙanta wasu tsuntsaye da wayo, musamman tsuntsaye irin su hankaka da makwarwa da yautai da kurciya da tsadda da sauransu. Bari mu ɗauki labarin hankaka mai hikima domin nuna misalin yadda Bahaushe ke tunani game da tsuntsaye musamman hankaka:

Labarin Hankaka Mai Hikima

Wani hankaka ne yana jin ƙishirwa, yana cikin fafutukar neman inda zai sha ruwa, sai ya hangi wani tulu. Ya yi ƙasa-ƙasa ya sauka a bakin tulun, ya leƙa ya ga akwai ruwa a ciki sai dai kash! Yawan ruwan rabin tulu ne, bakinsa ba zai kai yadda zai sha ba. Yana nan bakin tulu, yana tunani. Ga ƙishirwa yana ji , ga ruwa yana gani, amma ba hali ya sha, yaya ke nan? Kawai sai ya je yana tsinto duwatsu yana jefawa cikin tulun, da haka ruwa ya riƙa yiwo sama har ya kai yadda bakin hankaka zai kai, ya sha iyakar yadda ya ishe shi ya tashi (Muhammad, (2014).

Abin lura a wannan labarin shi ne, Bahaushe yana danganta wayo ga hankaka, bisa wannan dalili ne ya sanya hankaka bai fid da tsammani ga shan ruwan tulu ba, duk da bakinsa ba zai kai ba. Don haka sai ya ci moriyar wayonsa ya riƙa ɗebo dutse yana jefawa cikin tulun, ruwa na fallatsowa yana sha, har ya sha ya ishe shi. Ke nan, in da wani tsuntsun ne wanda Bahaushe ba ya kallon sa a matsayin mai wayo, to da sai dai ya haƙura da shan ruwan, tun da bakinsa ba zai kai ba.

3.4   Kimiyyar Gargajiya

A nan, idana aka yi batun kimiyyar Bahaushe a gargajiyance ana nufin hikimar da yakan yi amfani da iya wajen sarrafa wani abu ko samar da wani daga wani. Saboda haka, Bahaushe yana da kimiyyarsa ta gargajiya wadda yake sarrafa duniyarsa da ita domin samun abin masarufi musamman ta sana’o’insa na gargajiya. Shi ya sa wasu labarun bakan Bahaushe kan zo da bayanin irin kimiyyar da Bahaushe ke da ita a gargajiyance. Misali, labarain Bakatsine Mai Kan Ƙwarya ya nuna mana yadda kimiyyar sarrafa alewa take da kuma yadda ake sarrafa wuta a kimiyyance domin narkar da abin da ya daskare.

Bakatsine Mai Kan Ƙwarya

Wani ɗan alewa a ƙasar Katsina ya ɗauki ƙatuwar ƙwaryarsa danƙare da alewa, ya nufi Caranci cin kasuwa. Hantsi na yi, ban ruwan dawaki, ɗan alewa ya isa kasuwa, ya raɓa gindin inuwar wata ‘yar rumfa, ya sauke ƙwaryarsa ta alewa. Ya sa baki ya kira wata mai tallar fura da wata mai nono. Ya sayi furar kwabo biyu, nonon taro, ya yi damun ƙyale moɗa. Da ya gama, ya ɗebe hularsa ya ajiye gefe guda, ya sa ludayi ya yi wa furan nan kaf. Ya sa ruwa ya ɗauraye ƙwaryar. Ya zauna yana hutawa.

Can ta gero ta fara kama shi, sai ya riƙa lumshe ido yana gyangyaɗi. Sai ya yi nan lau, ya buɗe ido, ya sake yin lau, ya buɗe ido.

Jim kaɗan sai ya kishingiɗa gyangyaɗi na ta ɗaukarsa. Can barci ya rufe masa ido, bai san abin da yake yi ba, sai ya jawo ƙwaryarsa ta alewa, ya aza kansa bisa alewar. Ka san takan daskare ne kamar dutse, sai an narka in za a ja a sayar.

Gogan naka, ko da ya samu abin tayar da kai, sai ya duƙa barci, har da saleɓa. Can rana ta take tsaka, inuwar rumfa kuwa ta janye, alewa ta ce me za ta yi ko ba narkewa ba. Ashe sa’ad da alewa ke narkewa, kan gogan naka sai lumewa yake ciki, bai sani ba. Ga shi ko da suma cike da kai.

Can bayan azahar, da rana ta yi sanyi, sai alewa ta sake daskarewa, da kan ɗan alewa nutse ciki. Zuwa can kasuwa ta cika maƙil, sai hayaniyar mutane ta tayar da goganmu. Ya buɗe ido, ya yi miƙa, ya yi hamma, ya yunƙura zai tashi, sai ya ji kansa gingirim. Ya yi, ya yi ya tashi, ya kasa. Sai ya fasa kuka. Nan da nan kasuwa ta yi caa, aka taru wajensa.

Dattijai suka kama ƙwaryar alewa, suna ƙoƙari wai su cire ta. In sun ɗan ja, sai ɗan alewa ya ce, ‘‘Wayyo! Wayyo! Ku tsaya, ku tsaya!’’

Yara suka kewaye suna ta dariya, suna cewa, ‘‘Ihu! Ihu! Ga mai kan ƙwarya!’’

Mutane suka rasa yadda za su yi da shi. Sai wani ɗan alewa kuma ya ba da wata dabara, ya ce, ‘‘A kawo shi nan wajen masu tsire, a narka alewar.’’ Nan da nan aka kinkime shi da ƙwarya riƙe, aka je aka narka alewa. In an dakata wajen wuta, ɗan alewa ya ce, ‘‘Ku juya ni, ku juya ni, zan ƙone!.’’ Haka dai aka yi ta yi sannu sannu, har aka samu aka cire masa ƙwaryan nan daga kansa (Bunza, 2012:5).

A wannan labarin an nuna kimiyyar Hausawa ta hanyar amfani da wuta don sarrafa wasu buƙatun rayuwarsu. Sannan kuma, sana’ar alewa da yadda ake sarrafa ta sun tabbatar da yadda Bahaushe yake da kimiyyarsa a gargajiyance tun kafin ya haɗu da wata baƙuwar alumma. haka kuma dabara da suka yi wajen amfani da wuta domin cire ƙwaryar da ta maƙale a kan ɗan alewa, kimiyya ce ta gargajiya kamar yadda ta fito a cikin labarin. Bugu da ƙari, ko a labarin Ƙunar Baƙinwake mun ga yadda kimiyyar gargajiya take, musamman abin da ya shafi sarrafawa da samar da tukwane da toya su a wuta da makamantansu.

3.5   Fasahar Al’umma

Al’ummar Hausawa suna amfani da adabinsu wajen kimshe fasaharsu. Shi ya sa ta hanyar labarun baka za a iya naƙaltar fasahar al’ummar Hausawa. Misali, a labarin Wani Maciji da Zakara a Zariya, za a ga yadda labarin yake ƙunshe da fasahar al’ummar Hausawa wajen magance matsalar da aka hango tun kafin faruwarta:

Labarin Wani Maciji da Zakara a Zariya

A cikin Birnin Zariya an yi wani shahararren malamin addinin Musulunci, mai suna Malam Shehu na Malam Na'iya. “Wata rana yana cikin bayar da karatu a zawiyya, sai yara suka fito daga cikin gida da mushen zakara a hannunsu. A ɗaya hannun kuma da mushen maciji, sai Malam ya tambaye su ina za ku? Me ya faru? Yara suka ce ai wannan macijin ne ya sari zakara ya kashe shi, sai su kuma suka kashe macijin. Abin mamaki, sai Malam ya ce su ajiye mushen zakaran su tafi su jefar da mushen macijin. Bayan ɗan lokaci ana cikin karatu, sai ga wani maciji yana janye da mushen macijin da aka jefar ya shigo cikin zaure. Nan take, sai malamin nan ya sa aka ɗauko mushen zakara, ya karɓa ya ajiye a gaban macijin. Sai ya ce: “Ga ɓarnar da ya yi mana. Ya kashe zakara ne, mu kuma muka kashe shi.” Sai kawai aka ga macijin nan ya ɗauki mushen macijin nan ya juya ya tafi abinsa (Muhammad, 2014).

A wannan labarin, fasahar Bahaushe ta fito ƙarara inda aka nuna yadda malamin cikin hikima ya kauce wa abin da zai iya faruwa, sakamakon kashe macijin da yara suka yi. A matsayinsa na babba ya san cewa akwai yiwuwar macijin aljani ne (ko kuma aljani ya shiga jikinsa), tun da an san idan maciji ya riƙa, ya gawurta aljani kan shige shi. Saboda haka sai ya ce yaran su ajiye mushen zakaran domin ko da ‘yan’uwansa sun biyo baya, to za su gane wa idonsa ɓarnar da ɗan’uwansu ya yi har aka ɗauki fansa. Wannan ya tabbatar da fasahar al’ummar Hausawa cikin labaransu na baka. Haƙiƙa, za a iya cewa in da za a yi amfani da irin wannan fasahar, to da an yi maganin matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan, domin kuwa za a haƙe tutsiya tun daga tsittsigen.

4.0   Labaran Baka a Matsayin Hanyar Gina Rayuwar Gobe

A wannan gaɓar an zaɓi wasu batutuwa da suka shafi gina rayuwar gobe aka yi bayanin yadda suke fitowa cikin labaran bakan Bahaushe. An kawo misalan labaran da suke nuna sadaukar da kai da aikin gayya da taimakon juna da kuma nuna illar ƙarya da mutunta ɗan’Adam.

4.1 Sadaukar Da Kai Wurin Neman ‘Yanci

Babu wata al’umma da ba ta son ta rayu a matsayin ‘yantacciya. Kasancewa cikin ƙangin bauta yakan sa waɗansu su yi tunanin mafita ko da kuwa za ta zamo ajalinsu, matuƙar dai na baya za su rayu cikin yanci. A wasu lokutan, labaran baka sukan nuna darasi na sadaukar da kai domin ceto al’umma daga wani hali da suka shiga. Ire-iren waɗannan labaran sukan kasance na ƙundumbala da tauraron labarin ya yi domin kuɓutar da al’umma daga cikin wani halin ƙunci da suke ciki, don gobensu ta yi kyau. Irin wannan sadaukarwa ta fito ƙarara a labarin:

Ƙunar Baƙinwake

A zamanin da, an yi wani mutum marini mai ƙarfi wai shi Baƙinwake a Katsina. A daidai wannan lokaci kuwa akwai wani ɗan sarki da ya ƙasaita, ana jin tsoron sa a dukkan faɗin ƙasar, saboda zalunci da rashin tausayinsa. Su kuma mutanen fada a duk lokacin da ya fito sai kirari kawai suke masa, shi kuma sai girman kai, ba ya ko magana da talaka, sai dai ya sa a buge shi a ɗaure.

Shi ɗan sarkin nan yakan fita kilisa lokaci-lokaci. Ranar nan zai fita kilisa sai ɗan sarkin nan ya ce wai shi ya gaji da hawan doki. Nan da nan wani bawansa ya ce a je a kawo raƙumi. Ɗan sarki ya ce ya gaji da hawan raƙumin ma. Daga nan sai wani bawansa ya ce, ‘‘Ranka ya daɗe, yanzu ba abin da ba ka hau ba, sai mutum.’’

Da yake an sosa wa ɗan sarki abin da yake so, sai ya ce, ‘‘Haka ne. A je cikin birni a kamo ƙato guda, a yi mini sirdi bisansa.’’

Daga wannan lokaci sai ɗan sarki ya daina hawan dabba sai dai mutum. Idan zai hau sai a ɗaura masa sirdi a baya, a rataya masa igiya a wuya, ya dafa wani mutum, sa’annan ya hau a yi ta gudu da shi kamar dai ya hau doki. Kullum haka yake yi. Yau a kamo ƙato daga wannan unguwa, gobe wata unguwa.

A kwana a tashi, sai hawa ya kawo kan Baƙinwake. Mai unguwarsu ya zo ya gaya masa gobe shi za a hau, kada ya je koina. Baƙinwake ya yi shiru, ya ce, ‘‘To, ta faru ta ƙare!.’’Bayan da mai unguwarsu ya wuce, sai Baƙinwake ya tafi marinarsu ya sami tarin ciyawa ya sa masa wuta, ya koma gida ya jira wayewar gari. Kafin gobe wuta ta kama ciyawa rigirigi.

Gari ya waye, ɗan sarki ya aiko ga mai unguwa a kai masa ƙaton da zai hau ya je kilisa. Mai unguwa ya kira Baƙinwake ya ce ya hanzarta ya je ɗan sarki na jiran sa. Baƙinwake ya shiga gida ya yi ban kwana da iyalansa. Mutane suka nemi su ji ko lafiya, ya ƙi faɗin aniyarsa.

Da isar Baƙinwake fada aka yi masa sirdi, ɗan sarki ya hau, yana gaba sauran jama’a na biye. Bayan da suka ƙare kilisa, za a dawo gida sai aka bi ta hanyar marina. Suna nan zuwa har suka kai marinar su Baƙinwake, suka iske wuri ya cika da mutanen gidan su Baƙinwake. Idan Baƙinwake ya yi sanyi, sai ɗan sarki ya yi masa ƙaimi ya tsala masa bulala. Da Baƙinwake ya zo daidai ciyawar da ya sa wa wuta jiya, sai ya fara sakin hanya, ɗan sarki na karkata linzami, Baƙinwake na ƙiyawa. Dogarai na ‘‘Hattara dai, zaki! Linzami!’’ Shi kuwa ɗan sarki ya ruɗe sai bulala yake tsala wa Baƙinwake, yana masa ƙaimi. Da mutane suka gane nufin Baƙinwake sai suka fara ‘‘Kai, kai, kai! Shi kuwa ɗan sarki sai ihu yake yi, yana ƙoƙari ya kubce. Kafin dogarawa su cece shi, Baƙinwake ya kai ga wuta, ya yunƙura ya ce; ‘‘Tun nan duniya zan fara jefa ka wuta, daga yau kowa ya huta.’’ Sai ya yi tsalle ya faɗa tsakiyar wuta tare da ɗan sarki (Bunza, 2012:6-8).

An ce tun daga wannan lokaci ba a sake samun wani ɗan sarki a Katsina ko ma a kowane ɓangare na ƙasar Hausa, ya sake hawan mutum ya yi kilisa ba. Ke nan, wannan sadaukar da kai da Baƙinwake ya yi, ya kuɓutar da al’ummar ƙasar Katsina da ma sauran ƙasashe daga wani nauin zalunci daga masu mulkinsu na gargajiya. Tun daga wannan lokaci aka sami karin maganar nan ta Ƙunar Baƙinwake. Wannan yana nuna mana ko a yanzu idan ana buƙatar kawo gyara daga wata matsalar da ta yi wa alumma katutu, sai wasu sun sadaukar da rayukansu don goben wasu ta yi kyau. Domin kuwa labarin Ƙunar Baƙinwake ƙarara ya nuna irin sadaukar da kan mutanen Katsina wajen ceto yan uwansu daga halin ƙunci da baƙin ciki na baƙin zaluncin da wani ke yi masu. Ba tsoro, ba mugun mutuwa. Wannan shi ya sa Baƙinwake ya sadaukar da ransa, ya yi ƙunar mu je mu mutu tare da ɗan sarkin da ya addabi talakawa a nasa lokaci (Bunza, 2012:12).

4.2   Ayyukan Gayya

Aikin gayya wani aiki ne da ake taimaka wa juna ta hanyar haɗuwa a yi aikin taimakon kai da kai, ko kuma idan wani ba shi da lafiya ya kasa gyara gonarsa sai a yi gayyar ‘yan’uwa da abokan arziƙi a tafi a nome masa kyauta (Muhammad, 2014). An lura za a iya amfani da darussan cikin labarun baka domin gina rayuwar gobe, musamman ta laakari da yadda wasu labaran ke ɗamfare da darussan da ke nuna muhimmancin ayyukan gayya a cikin al’umma. Misali, tatsuniyar:

Barewa ta Auri Mutum

A cikin tatsuniyar, an nuna wata barewa ce ta rikiɗa ta zama mace kyakkyawa, ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a kanta, ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye.Ta ce duk wanda ya jefa ‘yar tsakuwa ta buɗe kwatashin shi ne mijinta, sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa, bai buɗe ba.Wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba, sai aka samu wani ya jefa ‘yar tsakuwa sai ya buɗe, sai ta ce ta samu miji shi za ta aura, sai suka tafi garin su yarinyar wurin iyayenta, aka ɗaura mata aure da wannan mutumin, ta zo ta zauna a gidan miji. Kullum ranar girkin ta sai a ce ta je, ta ciro kuɓewa a gonar miji ta yi miya.Da ta je gonar sai ta yar da zaninta, ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa, sai ta yi kiran yanuwanta, ta hanyar waƙa, ta ce:

Cikal-cinkal, cinkali kalaya.

Turmin ‘yankale ya yi fure, ceɗiya.

Tudu na korar tudu marina.

Tudu na korar tudu da ƙaho.

Ban da kwatsakwatsan ban da ƙanƙana.

Nan da nan sai ‘yan uwanta su zo su taro su ciccinye kuɓewa, in sun gama sai su tafi ta gida, ita kuma sai ta yi birgima ta koma mutum ta ɗauki zaninta ta ɗaura, ta koma gida tana cewa ni da gangan aka tura ni ga shi nan ban samo komai ba. To wata rana sai mijinta ya bi ta gonar sai ya gan ta tana birgima, da ta gama birgimar sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa, sai ya ga ta yi kiran ‘yan’uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim, duk suka cinye kuɓewar suna cikin ci sai ya fasa su sai ya ga matarsa ta gan shi, ya koma gida sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi ta tarar da shi a gida. Ya ce wace ce? Ta ce ni ce. Ya ce ina za ki? Ta ce ɗaki za ni. Ya ce a’a koma daji. Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji daga nan ba ta sake dawowa ba (Muhammad, 2014).

Abin lura a nan shi ne, duk da tatsuniyar tana ɗauke da wani saƙo na daban, amma tana ƙarfafa aikin gayya. Idan aka yi la’akari da yadda barewa take yin waƙa yanuwanta su taho su taya ta cinye kuɓewa, wanda in ita kaɗai ce ba za ta iya cinyewa ba. Wannan ya yi daidai da karin maganar da ke cewa hannu da yawa maganin ƙazamar miya, ko kuma hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, da sauransu. Bugu da ƙari, tatsuniyar ta nuna hoton rayuwa irin ta zaman gandu wadda Bahaushe ke yi. A irin wannan zama tamkar ana ayyukan gayya wajen taruwa a riƙe gida da ƙarfafa zumunci da yanuwantaka da zaman tare.

A yau zamani ya banzantar da aikin gayya, komai sai dai kuɗinka ya ba ka, in ba ka da shi sai dai ka haƙura, ashe kuwa da za a koma a rungumi irin waccan rayuwa mai ruhin taimakon juna ta fuskar aikin gayya kamar yadda suka fito a tatsuniyar Barewa ta Auri Mutum, lallai da an gina rayuwar gobe ingantacciya.

4.3   Taimakon Juna

Bahaushe mutum ne mai taimakon juna a tsarin zamantakewarsa. Tun ta hanyar duba da yadda gidansa yake za a tabbatar da haka. Har ila yau, duk inda Bahaushe yake a da, za a same shi ba ya ƙaunar wani abu mara daɗi ya sami ɗan’uwansa, kamar ciwo ko mutuwa, ko wata asara kamar gobara, ko sata da sauransu. In kuma wata ƙaddara ta sami ɗan’uwansa, yana taya shi jaje da alhini. In kuma abin alheri ya samu ɗan’uwansa, misali idan aka yi wa wani haihuwa, ko kuma aure, a nan ma Bahaushe yana taya juna farinciki da murna (Muhammad, 2014). Duk waɗannan suna ƙara ƙulla zumunci da taimakon juna a tsakanin alumma. A wannan fuskar ma za a iya amfani da labaran baka a matsayin hanyar gina kyakkyawar al’umma ta fuskar taimakon juna. Alal misali, idana muka dubi almarar Ɗanfulani da Kaɗo, za ta haska mana wannan fasali.

Almarar Ɗanfulani da Kaɗo.

Wata rana an yi wa Ɗanfulani haihuwa, ranar suna sai ya gayyaci Kaɗo zuwa taron suna. Gari ya waye Kaɗo ya shirya ya nufi ruga, don amsa gayyata. Bayan an yi taro an sanya wa jariri suna, aka yi shagali aka watse. Ɗanfulani bai ba Kaɗo komai ba, sai ya ɗauko ƙahon sa, wanda aka yanka ya ce da Kaɗo ga shi ka yi tururu (ƙahon hura). Kaɗo ya karɓa ya yi godiya, bai nuna ya damu ko ɓacin rai ba. Ashe Kaɗo ya yi alƙawarin sai ya rama.. (Muhammad, 2014).

Idan aka yi la’akari da wannan almarar, za a iske cewa tana nuna muhimmancin taimakon juna da kuma gudummawa da taimakekeniya a tsakanin al’umma, musamman a yanayi na sha’ani ko buki na aure ko haihuwa. Shi ya sa ko da Kaɗo ya zo suna gidan Ɗanfulani, a bisa yadda alada ta tanadar ya kamata ya zo masa da gudummaw, amma bai zo da shi ba, shi kuma Ɗanfulani sai cikin hikima ya nuna masa ya dace ko don nan gaba ya lura da muhimmancin taimakekeniya a muamalarsa da jamaa. Saboda haka ne Ɗanfulanin ya ba Kaɗo kyautar ƙahon sa. Almarar tana nuna mana muhimmancin taimakon juna, don haka za ta iya zama hanya ta gina rayuwar al’umma.

4.4   Illar Ƙarya

Ƙarya mugun guzuri! Ƙarya na nufin maganar da ba ta gaskiya ba ce. (Sa’id, 2006). A ra’ayin Bunza (2009) yana ganin cewa, ƙarya ita ce faɗar maganar da ba a yi ba, ko ba a gani ba, ko ba a tabbatar ba, da kuma yin ƙari ga abin da aka ji ko aka gani, ko yin ragi a gare shi. Idan aka yi laakari da labaran baka za a ga cewa, Bahaushe ba ya son ƙarya, ya ƙyamace ta, wannan ya sa ma yake kiran ta mau gajeren zango. A cikin tatsuniyoyin Hausa za a ga duk tauraron da ya yi ƙarya, komin nasarar da ya samu kafin tatsuniyar ta ƙare, sai an nuna ƙarshensa bai yi masa kyau ba. Ga misali daga tastuniyar Gizo da Dodanniya:

Tatsuniyar Gizo da Dodanniya

Wata rana Gizo ya tafi gidan Dodanniya ya karɓo bashin bajimin sa, da alƙawarin zai biya shekara mai zuwa. Ya zo ya cinye, ya hana kowa. Ko da shekara ta zagayo, sai Dodanniya ta zo bin bashi gidan Gizo. Bayan Dodanniya ta iso gidan sai Ƙoƙi ta ce gizo ya mutu. Har ta kama hanya za ta koma, sai Kurciya ta ce ƙarya ne. Daga nan sai suka koma gidan Gizo, ta fara waƙa tana cewa:

 

 Kurciya: Mabiyan bashin Gizo sun iso,

 Mabiyan bashin Gizo sun iso,

 Zai yi biyan bashi a kushewa.

 

 Gizo: Un uhun wai ya kurciya,

 Ki biyo ta gidan mu ki sha ruwa,

 Ruwanki na nan a kururrumi,

 Bari in fita in taɓa ‘yar rawa,

 Bari in fita in taɓa ‘yar rawa.

Daga nan sai Gizo ya fito, Dodanniya ta kama shi ta tafi da shi gidanta (Muhammad, 2014).

 

Wannan ya nuna mana muhimmancin gaskiya tare da horar da al’umma cewa komi rintsi kada ka yi ƙarya, ka tsaya a kan gaskiyarka. Domin kuwa ko da ka yi ƙaryar, to fa ramin ƙarya ƙurarre ne. Shi ya sa ko da Ƙoƙi ta yi ƙaryar cewa Gizo ba ya nan, har Dodanniya ta juya za ta tafi, sai Kurciya ta tona asiri ta hanyar yin waƙa shi kuma Gizo ya amsa mata. Ke nan, ramin ƙaryar Gizo ya ƙure ne a daidai lokacin da raujin waƙa ya ɗebe shi ya manta an zo kama shi, ya amsa waƙar har Dodanniya ta kama shi.

4.5   Mutunta Ɗanadam

Labaran baka na Bahaushe suna koya mana sanin mutuncin ɗan’adam, ta yadda wasu labaran ke jaddada kada ka raina matsayin mutum don halin da ka tsince shi. A kodayaushe ka mutunta mutum, ko ba komai ba ka san baiwar da Allah ya yi masa ba wadda in aka yi dubi na tsanaki, ƙila yana da wani abin burgewa ko wani abin da kai ba ka da shi. Mu dubi almarar Ɓeran Birni da Ɓeran Daji:

Ɓeran Birni da Ɓeran Daji

Wata rana ɓeran birni ya tafi daji wurin ɓe ran daji. Ko da ya je sai ya ga abincin ɓeran daji daga harawa, sai dankali, sai ciyawa. Nan take sai ɓeran birni ya kushe abincin, sai ya ce ɓeran daji shi ma ya zo birni don ya ga irin daɗin da yake ci. Watarana sai ɓeran daji ya tashi ya tafi birni. Da isarsa sai ɓeran birni ya tarbe shi, sai ga soyayyen nama, ɓeran daji zai ci ke nan sai ɓeran birni ya hana shi ya ce kar ka taɓa tarko ne, suka wuce. Daga nan kuma, sai ga wani abincin har zai taɓa, ɓeran birni ya ce wannan da magani in ka ci za ka mutu. Bayan wannan kuma suna cikin tattaunawa kawai sai ɓeran birni ya ce yi maza ka shiga rami ga mage nan, suka shige rami a guje. Ganin irin wannan rayuwa mai cike da haɗari wadda ɓeran birni ke ciki, sai ɓeran daji ya ce: A gaskiya raka ni in koma daji in cigaba da rayuwata a sake, ba irin wannan ba. Da arziƙi da tashin hankali, ai gwamma tsiya da kwanciyar rai, in ji ɓeran daji (Muhammad, 2014).

Wannan almara ta nuna mana cewa duk halin da kake ciki ka fi wani, wanda kake ganin ya fi ka. Shi ya sa ko da ɓeran birni ya raina abincin ɓeran ƙauye, ya gayyace shi zuwa birni domin ya ga irin abincin da ɓeran birnin ke ci, da ya je kuwa sai ya ga cewa bayan tiya akwai wata cacar, domin kuwa abincin ba ya ciwo cikin kwanciyar hankali. A kodayaushe yana cikin zullumin tarko ko magani ko kuma mage. Haka wannan batun yake a zahiri, saboda haka wannan ya sake jaddada cewa za a iya amfani da labaran baka wajen gina rayuwar gobe, musamman gyara tunanin mutane a kan darajanta ɗan’adam a kowane matsayi ka same shi.

A tunani irin na wannan yanayi, ya sa hukumomi da dama sun sha yin kira a kan mutanen karkara da su rage kwararowa zuwa birane, domin hangen dala ba shiga birni ba ne. Ko ba komai kallon kitsen rogo da ake yi wa rayuwar birni ta fito fili a cikin wannan almarar. Domin kuwa duk da ɓeran birni yana jin cewa shi yana cikin jin daɗi, yana cin abinci mai kyau fiye da na ɓeran ƙauye, amma ya rasa kwanciyar hankali irin na ɓeran ƙauye.

5.0   Sakamakon Bincike

Labaran baka kamar kowane nau’i na adabi sukan kasance hoto ne da ke ɗauke da kwatankwacin rayuwa ta jiya da yau da kintatar gobe. Suna ɗauke da fasalce-fasalcen rayuwar al’umma tare da kuma nuna rayuwa mai kyau da maras kyau. Wannan ne ya sa labaran baka suka kasance su ne ke inganta rayuwar ɗan’Adam, har ya zama mutum. Tun da farko, wannan nazari ya ƙudiri aniyar gano yadda adabin bakan Bahaushe musamman labarai kan kasance tamkar wata taskar adana ilimin rayuwa ga alummar jiya da ma ta yau.

A cikin wannan nazari an fahimci cewa labaran bakan Bahaushe wata makaranta ce wadda ke koya dabarun rayuwa ta hanyar hani da horo cikin nishaɗi. A cikin nazarin an gano cewa akwai abubuwa da dama waɗanda labaran suka ƙunsa waɗanda ke nuna rayuwar Bahaushe ta asali wanda ya shafi tarihinsa da kimiyyarsa da fasaha da zamantakewa wanda ya shafi yanayin taamakon juna ta hanyar aikin gayya da sauransu.

A cikin naazarin an riƙa yi ana kafa hujja da wasu labarai na baka waɗanda daga cikinsu ne aka fito da waɗannan abubuwa ta hanyar bayani da fashin baƙin labaran.

Wani abin da nazarin ya gano kuma shi ne, yadda labaran za su taimaka wurin gyarawa da daidaita rayuwar yau ta la’akari da irin hikimomin rayuwar da aka kawo a cikinsu waɗanda in da al’ummar yau za su ɗabbaƙa su cikin alamuransu na yau da kullum a wannan zamanin da an samu sauƙi a wasu lamura da dama.

6.0   Kammalawa

A wannan aikin, an yi ƙoƙarin fito da muhimmancin labaran baka ne ga Bahaushen yau. Bayan shimfiɗa tare da ma’anar labari da labaran baka, an kawo ire-iren labaran bakan Bahaushe, inda aka ɗauki wasu daga ciki aka yi bayaninsu daidai gwargwado domin fito da su fili a fahimce su. Daga nan sai aka fayyace yadda labaran suka kasance taskar ilimi ta fuskokin tarihi da kimiyya da fasaha da falsafa da sana’o’i. Daga bisani aka bayyana yadda labaran suke kasancewa hanyar gina rayuwar gobe, inda aka riƙa bayani ana kawo misalai daga labaran. A ƙarshe, an kawo sakamakon bincike sannan aka kammala nazarin tare da manazarta.

Manazarta

Babajo, A.K (2018). Orature, Meaning, Nature and Forms. A Study Guide. Kaduna-Nigera: Slimline Communications Ltd.

Bunza, U. A. (2012). “Katsina Ɗakin Kara: Gudummawar Qasar Katsina Ga Samuwar Wasu Labaran Bakan Bahaushe. Takardar da aka gabatar a taron Ranar Katsinawa da Ɗaliban Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato yan asalin Katsina suka shirya a babban Ɗakin ETF3 na mazaunin jamiar na dindindin a ranar Assabar, 24 ga watan Nuwamba, 2012 da ƙarfe goma na safe.

Bunza, U. A. (2013). “Tarbiya a Cikin Adabin Hausa: Tsokaci Daga Karin Magana. Cikin Malumfashi, I.A.M. (ed); Kada: Journal of Liberal Arts, Vol 7 No. 1. Kaduna-Nigeria: Faculty of Arts, Kaduna State University, Kaduna.

Bunza, U.A (2015). “Talife-Talifen Hausa a Zamanin Mulkin Mallaka: Sigoginsu Yanayinsu Da Sigoginsu.” Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Dunfawa, A.A. (2013). “Tunanin Bahaushe Cikin Littafin Ruwan Bagaja”. Cikin Special

 Research in Humanities. Katsina: Umaru Musa Yar’adua University.

Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa. Sabon Tsari. Zaria : Amana Publishers.

Gusau, S.M (1995). Dabarun Nazarin Hausa. Kaduna : Fisbas Media Services.

Gusau, S.M. (2006). Tatsuniya (Gatana):Sigoginta da Hikimominta.Cikin Mujallar Algaita,

Malumfashi, I. (2019) (ed). Labarin Hausa a Rubuce: 1927-2018. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Muhammad, M. S. (2014). “Rowa (Hali, Wayau, ko Ciwo?): Tsokaci a kan Ɗabiar Rowa a Rayuwar Bahaushe Jiya da Yau”. Takardar da Aka Gabatar a Taron Tallafa wa Marayu a Garin Kudan a Zauren Taro (Town Hall) da ke Likoro Road Sabon Garin Kudan. Ranar Asabar 5 ga Yuli 2014, 8 ga Ramadan da Ƙarfe 09:00 na Safe.

Muhammad, M. S. (2014). “Wayon Dabbobi a Ma’aunin Adabin Bahaushe Jiya da Yau”. Being a Mandatory Ph.D Seminar Paper, Presented at the Department of Nigerian Languages. Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto.

Muhammad, M. S. (2014). “Rikiɗa a Falsafar Bahaushe.” Being a Mandatory PhD Seminar Paper, Presented at the Department of Nigerian Languages. Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto.

Sabe, B. A. (2011). “Adabin Kasuwar Kano: Nazari Da Sharhi Game Da Ƙagaggun Labaran Hausa, 1984-2008”. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Sa’id, B. (2006) Ƙamusun Hausa. Zariya: Ahmadu Bello University Press

Yahaya I.Y. da Wasu (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. Ibadan: University Press PLC.

Yahaya I.Y. (1971). Tatsunniyoyi da Wasanni. Ibadan: Oxford University Press.

Download the article:

Post a Comment

0 Comments