Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Bankwana Ga Kabiru Waya

Bismillahi Rahaminir Rahim

Wak'a ce nake so za ni rera
Mai gajeren zango ya Tabara
Ka ba ni ilhama don in tsara
In yiwa abokina don ya dara
Mutuwa ba za ta sa mu manta da shi ba.

Allah Sarki Mamman Kabiru Waya
Yau dai ka tafi inda ba' biyan haya
Ba jin kira balle har ka d'aga waya
Ba tsumi ba dabara balle kai laya
Tafiya ce za kai ba don za ka dawo ba.

Rayuwa ta yi kyau alkhairi ka shuka
Ga shaidu sun taru kowa na ta kuka
Hankalinmu ya tashi babu mai suka
Da ance K sai ka ji ana ta son barka
Kyautarka sam ba irin ta masu fariya ba.

Gamo da kai gamo ne da alkhairi
Ba ka mugunta balle har kai sharri
Kalamanka a aune harshenka fari
Mai kyauta da k'ari wane alifu d'ari
Sai ka bayar ba don ai ma godiya ba.

Bakwandale hidimtawa marayu
Ka yi sutura har ka basu abayu
Ka ci da su har da kaji soyayyu
Ka sadaukar don al'umarka ta rayu
Ga mai rowar amin bai san Kabir ne ba.

Kiran Waya an san na kowa ne
Ko ba komai ai sada zumunci ne
In ka ji had'a Waya to ai nema ne
Samun alkhair ai wannan dace ne
Sai dai in ba a nema daga Ubangiji ba.

Bawan Allaah fari mai farar aniya
Ka shuka a gonarka dake nan dunya
Koriya shar yabanyarka ba tutiya
Amana ka bar wa wasu a sanadiya
Za ka girba a can ba da tawaya ba.

Cuta ba mutuwa ba kowa da ta shi
Kaima ka kintsa in tazo babu fashi
Dinga adashi don ranar biyan bashi
Ko ka so ko k'i ko da za ka ji haushi
Mai ba ka bashin ba zai manta da kai ba.

Cikar d'ango aka yiwa mai jama'a
Sahu sahu dubbai su kai ma sàllah
Aka rankaya aka kai ka gida jannah
Rok'onmu ke nan ga Maisama Allaah
Yau masoya za su kwan ba da kai ba.

Sunan mawak'in Muhammadu Tajo
Dan Tijjani ne mai suna na Manzo
Zan dakata nan mai gyara ya mik'o
K'olo ne a fagen ya ku masu kallo
Allaah Ka jik'an mu ba don mun gushe ba.

Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments