Ticker

6/recent/ticker-posts

KALUBALE GA IYAYEN ZAMANI (Hausa Haiku 21)

1.

Da me zan fara
wannan kira ne gare
mu iyayen yau?

2.

Musamman mata
way'anda sune tushen
al'uma sahih.

3.

Farkon mace y'a
abar karewa daga
dukkan illoli.

4.
Da haihuwarta
kowa yake shirin yi
mata hidima.

5.
Ta musamman don
kiyaye ta daga hau
da kan doshe ta.

6.
Uwa ta gari
uba yake nemawa
y'arsa tun farko.

7.
In har yana son
ya gina tarbiya mai
kyau da d'orewa.

8.
Ya nema mata
mahaifiya mai ilmi
mai k'aunar Allaah


9.

Ta d'ora damba

don tabbatar da samun

maimai a gaba.


10.

A nuna mata

son kyau ta koyi tsaftar

jiki da hali.


11.

Tunaninta ya

tsarkaka akan neman

da kar6ar halal.


12.

Da jin sunanta

kai ka san babu wargi

a linzaminta.


13.

Mace mutum ce

Daga gidan daraja

tashin sutura.


KALUBALE GA IYAYEN ZAMANI (Hausa Haiku 21)

14.

Fal da karatu

Islamiyya da Boko

Hafizar Qur'an.


15.

'Kawaye sago

kowacce irinta ce

Babu na yarwa.


16.

Lu'ulu'u da

murjanai duk sun fi gwal

wane azurfa.


17.

Ba ballagaza

balle mai ashariya

Duba ka gani.


18.

Sharholiya wai!

Jelar rak'umi ta yi

nesa da k'asa.


19.

'Yar zamani mai

digiri da digirgir

har da PhD


20.

Wasu sun gani

suna so ta ce sai shi

za6a66en bawa.


21.

Uwa da uba

ga jan aiki gabanku

Da mai iyawa?

 Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

Post a Comment

0 Comments