𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wace magana ce
ta fi a kan: Tsayuwa a bayan malami a lokacin da yake gabatar da wa’azi ko
karatu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Malaman da suka yarda da a riƙa
yin hakan gare su ko ga waɗansu
malaman da ba su ba, me yiwuwa suna da dalilan da suka gamsu da su a kan hakan.
Amma dai abin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
shi ne
« إِنْ كِدْتُمْ آنِفِاً لَتَفْعَلُونَ فِعْلَ فَارِسَ وَالرُّومِ يَقُومُونَ عَلَى مُلُوكِهِمْ وَهُمْ قُعُودٌ فَلاَ تَفْعَلُوا »
Ɗazun nan kun kusa yin irin aikin Farisawa
da Rumawa: Suna tsayuwa a kan sarakunansu a lokacin da su ke zazzaune! Kar ku ƙara
yin irin hakan. (Sahih Muslim: 955).
Ya faɗi wannan ne a cikin hadisin Jaabir Bn
Abdillaah bayan ya ga yadda Jaabir ɗin
tare da waɗansu
Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) sun yi sallah a tsaitsaye a bayansa, alhali kuma
shi a zaune ya yi sallar saboda larurar rashin lafiya da ta same shi a lokacin
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alaa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallam).
A wurin fassara wannan maganar
Al-Imaam An-Nawawiy (Rahimahul Laah) ya ce
فِيهِ النَّهْيُ عَنْ قِيَامِ الْغِلْمَانِ وَالْأَتْبَاعِ عَلَى رَأْسِ مَتْبُوعِهِمْ الْجَالِسِ لِغَيْرِ حَاجَةٍ
Wannan hadisin ya hana masu
hidima da mabiya su miƙe tsaye a kan wanda suke girmamawa alhali shi yana zaune, ba
da wata larura ba. (Sharh An-Nawawiy Alaa Muslim: 4/135).
A fahimtar malamanmu:
(i) Babu wata larura ko buƙata
da za ta sa ɗan
agaji ya tsaya a baya ko a gefe ko kuma a gaban mai wa’azi ko mai karantarwa,
irin yadda ake yi wa waɗansu
malamai a yau.
(ii) Kamar yadda hadisin ya nuna
a fili, wannan koyi ne kawai ake yi da kafirai (Farisawa da Rumawa) a cikin ɗabi’unsu na rayuwarsu.
(iii) Koyi da kafirai a cikin duk
wata keɓantacciyar ɗabi’a da ta shafi
rayuwarsu abin hanawa ne a shari’ar musulunci, sai dai abin da ya zama dole ba
makawa a gare mu.
(iv) A yau dai tsayuwar ɗan agaji a gaba ko baya
ko a gefen malami ba za ta iya kare malamin daga ta’addancin ’yan ta’adda ba
gare shi ko ga sauran masu sauraron wa’azinsa ko karatunsa.
(v) Tsayuwar waɗannan jami’an tsaron a
bakin gate ko ƙofofin shiga inda ake gabatar da darussan, suna binciken masu
shiga da fita ba tare da bambantawa ba shi zai fi amfani, kuma ya fi samar da
natsuwa ta zuciya da gaɓoɓi ga masu sauraro da bin
karatun, in shaa’al Laah.
Allaah ya ƙara mana kariya gaba-ɗaya daga sharrin dukkan
masharranta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp
number: 08021117734
Ga Masu Buqatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi Waɗannan
Links...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.