Shin Wanda Ya Bada Sadaki Na Zai Iya Taɓa Jikina

    𝐓𝐀𝐌��𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Malam ashari'ar muslunci namiji zai iya taɓa hannun yarinyar da aka bashi aurenta aka sanya ranar aure har ya biya sadaki, da wanda bai kai da biyan sadakin ba? Malam Allah ya kara nisan kwana da rayuwa mai albarka Malam shin hakan ya halatta ko kuwa bai halatta ba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam Warahmatullah Wabarakatuh.

    Abinda yake halatta wa mutum taɓa jikin mace ko ganin wani sashi na jikinta inbanda fuska, shine in an aura masa ita ko kuma ya mallaketa a matsayin baiwa. Saidai in matan muharramansa ce, wanda babu aure a tsakanin su, ta hanyan dangantaka ko surkuntaka, wannan ba laifi dan ya taɓa jikin ta Amma ba da nufin sha'awah ba.

    Hakanan wanda yake neman auren mace har yakaiga biyan sadaki, har yanzu tana nan a wacce bata halatta gareshiba hassai an aura masa ita.

    Bayada banbanci dashi da wanda bashiba a abinda ya shafi jikinta. Dan haka haramun ne ya taɓa jikin ta.

    WALLAHU A'ALAM.

    Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Waɗannan Links...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.