Ticker

6/recent/ticker-posts

Taya Kirista Murnar Kirsimeti

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ko zan iya taya kiristoci murnar bikin kirsimati, ko da a rubuce ne kamar ta sanyawa a status da sauran kafafen sada zumunta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Kirsimeti biki ne na addini a wurinsu, ba na al’ada ne kamar na aure ko suna ko na samun ƙarin girma da makamantan hakan ba. Don haka ba daidai ba ne, kuma kuskure ne a haɗa a tsakaninsu a wurin hukunci. Kuma abin da ya halatta a cikin bikin al’ada ba lallai ya halatta a cikin bikin addini ba.

Daga nassin Alqur’ani mun ji cewa, duk kafiran da ba su yaƙe mu a cikin addini ba, ba su fitar da mu daga cikin garuruwanmu ba, kuma ba su taimaka a kan fitar da mu ɗin ba, waɗannan Allaah bai hana mu sadar da alheri da kyautatawa gare su ba, kuma bai hana mu yi musu adalci ba.

لَا يَنْهٰٮكُمُ اللّٰهُ عَنِ الَّذِيْنَ لَمْ يُقَاتِلُوْكُمْ فِى الدِّيْنِ وَلَمْ يُخْرِجُوْكُمْ مِّنْ دِيَارِكُمْ اَنْ تَبَرُّوْهُمْ وَ تُقْسِطُوْۤا اِلَيْهِمْۗ اِنَّ اللّٰهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِيْنَ ٨۝ اِنَّمَا يَنْهٰٮكُمُ اللّٰهُ عَنِ الَّذِيْنَ قَاتَلُوْكُمْ فِى الدِّيْنِ وَاَخْرَجُوْكُمْ مِّنْ دِيَارِكُمْ وَظَاهَرُوْا عَلٰۤى اِخْرَاجِكُمْ اَنْ تَوَلَّوْهُمْۚ وَمَنْ يَّتَوَلَّهُمْ فَاُولٰۤٮِٕكَ هُمُ الظّٰلِمُوْنَ ٩۝

Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle Allah Yanã son mãsu ãdalci. Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai. (Surah: Al-Mumtahana, Ayat: 8-9)

Abu ne a fili kuwa cewa a ƙarƙashin sadar da alheri ga irin waɗannan ɗin akwai taya su murnar samun aure da haihuwa, ko kuma ƙarin girma. Haka kuma taya su baƙin ciki a lokacin asarar dukiya ko ta rayuwa, kamar lokacin mutuwar danginsu kafirai da makamantan hakan, muddin dai hakan bai ci-karo da wata ƙaida daga cikin ƙaidojin addininmu ba.

Amma kuma lallai mu yi taka-tsantsan in ji malamai, a wurin yi musu ta’aziyya tun da shi abu ne da yake da alaƙa da addini. A nan ba a yarda mu roƙa wa mamacinsu gafarar Allaah ko rahamarsa ba. Sai dai kawai mu yi wa rayayyunsu addua, kamar ta neman Allaah ya ƙara musu haƙuri da juriya, da ƙarfin zuciyar ɗaukar nauyin rashin mamacin, da kuma fatar Allaah ya musanya musu abin da suka rasa da wanda ya fi shi alheri.

Kamar haka Kirsimeti - da sauran bukukuwan da suka shafi addininsu - ya ke. Taya su murna ta kowace irin hanya, kamar ta magana ko ta rubutu ta hanyar saƙon waya na kar-ta-kwana, ko ta cikin tashoshin social media ko gidajen rediyo da talbijin, ko ta hanyar kunna wuta da buga abubuwan fashewa da dare, da ziyartarsu a ɗakunan bautarsu da wuraren bukukuwan, da taimaka musu da kyaututtukan furanni ko kayayyaki ko kuɗaɗe da makamantan hakan, waɗannan duk haramtattun abubuwa ne. Saboda ana ɗaukar aikata hakan kamar goya musu baya da amincewa ne da irin abin da ke cikin mummunar addininsu da aƙidarsu ta Allantar da Annabi Isa (Alaihis Salaatu Was Salaam), da kuma cewa Allaah (Tabaaraka Wa Taaala) yana da ɗa. Wannan kuma zagi ne mummuna gare shi (Subhaanahu Wa Ta’aala), kamar yadda hadisai sahihai suka tabbatar. Al-Imaam Al-Bukhaariy (4974) ya riwaito da isnadinsa sahihi har zuwa ga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa, shi ya ce

« قَالَ اللَّهُ: كَذَّبَنِى ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، وَشَتَمَنِى وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّاىَ فَقَوْلُهُ لَنْ يُعِيدَنِى كَمَا بَدَأَنِى ، وَلَيْسَ أَوَّلُ الْخَلْقِ بِأَهْوَنَ عَلَىَّ مِنْ إِعَادَتِهِ ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّاىَ فَقَوْلُهُ اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا ، وَأَنَا الأَحَدُ الصَّمَدُ لَمْ أَلِدْ وَلَمْ أُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لِى كُفْأً أَحَدٌ ».

Allaah ya ce: Ɗanadam yana ƙaryata ni amma hakan bai kamace shi ba. Sanan yana zagi na, kuma hakan ma bai kamace shi ba. Amma ƙaryatawarsa gare ni ita ce maganarsa cewa: Allaah ba zai iya mayar da ni kamar yadda ya fare ni ba. Alhali sauƙin fara halitta a gare ni bai fi na maimaitawa ba. Amma zaginsa gare ni kuwa shi ne maganarsa wai Allaah yana da ɗa.’ Alhali ni ne Makaɗaici, Wanda ake nufi da buƙatu. Ban haifi kowa ba, ba a haife ni ba. Kuma wani ɗaya bai zama tamkar ni ba.

Allaah ya kare mu da zuriyarmu daga dukkan hanyoyin hallaka.

A ƙarƙashin wannan babin ne kuma waɗansu malaman suka sako batun cin abincin na Kirsimeti. Sun nuna rashin halaccin cin sa, domin shi ma kamar goya musu baya da taya su murna ne a kan ɓatarsu da ɓarnarsu.

Sai dai kuma dayake an samu waɗansu riwayoyi masu nuna cewa waɗansu daga cikin magabatan wannan al’ummar mai albarka sun ci, kuma har sun yi umurni da cin irin abin da ba yankakken nama daga arnan zamaninsu ba, shiyasa waɗansu daga cikin malaman musulunci suka yarda cewa za a iya cin na irin waɗannan ɗin su ma.

Akwai ma waɗanda suka zaɓi cewa babu wani bambanci a tsakanin yankarsu da Alqur’ani ya halatta (Surah Al-Maa’idah: 5) da abin da ba shi ba na abincin wannan bikin na su. Suka ce saboda ayoyin da suka halatta cin yankarsu ba su bambance a tsakanin na bikin addini da waɗanda ba su ba.

Amma kuma yana da kyau a riƙa lura da hali ko yanayi na kowane zamani da wuri kafin a ɗabbaka irin waɗancan nassoshin da yadda magabata suka yi aiki da su. Duk mun san cewa nassin da ya halatta cin yankan Ahlul-Kitaab a haɗe ya ke da wanda ya halatta auren matansu

اَلْيَوْمَ اُحِلَّ لَـكُمُ الطَّيِّبٰتُۗ وَطَعَامُ الَّذِيْنَ اُوْتُوْا الْكِتٰبَ حِلٌّ لَّـکُمْۖ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَّهُمْۖ وَالْمُحْصَنٰتُ مِنَ الْمُؤْمِنٰتِ وَالْمُحْصَنٰتُ مِنَ الَّذِيْنَ اُوْتُوا الْـكِتٰبَ مِنْ قَبْلِكُمْ اِذَاۤ اٰتَيْتُمُوْهُنَّ اُجُوْرَهُنَّ مُحْصِنِيْنَ غَيْرَ مُسَافِحِيْنَ وَلَا مُتَّخِذِىْۤ اَخْدَانٍۗ وَمَنْ يَّكْفُرْ بِالْاِيْمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهٗۖ وَهُوَ فِى الْاٰخِرَةِ مِنَ الْخٰسِرِيْنَ

A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra. (Surah: Al-Maaida, Ayat: 5)

Kuma magabatanmu sun yi aiki da su gaba-ɗaya a sadda da yadda suka dace ba tare da matsala ba. Amma me ya sa a yau kuma a cikin al’ummarmu malamai suke ƙyamatar da musulmi daga irin wancan auren na matansu? Ba domin illoli da ɓarnar da suke ganin yana aukuwa a ƙarƙashin hakan ba ne?! Gidajen musulmi nawa ne irin wannan auren ya ruguza ya lalata?! Gidaje nawa ne da ake neman samun zuriya ɗayyaba amma sakamakon irin wannan auren ya koma samar da ’ya’ya kafirai zalla masu aiki da kulawa da coci?! Laa haula walaa quwwata illa bil Laah.

Wannan ya sa na ce: Ni dai a ɗan ƙaramin fahimtata, ba ruwana da duk kiristan da aka san yana daga cikin waɗanda ake haɗa baki da su har kuma ake ta ƙulla mana makirce-makircen da suka haɗa da

(1) Ɗaukar nauyin waɗanda suke cigaba da koyon addininmu domin lalata shi da gurɓata shi, don ƙyamatar da jamaarsu daga kyakkyawar koyarwarsa, kamar su Maitatsine!

(2) Koya wa matasanmu mummunar aƙidar suka ko zagin sahihin addini, da zagin wanda ya zo da addinin, da wanda ma ya aiko da addinin, kuma duk wai da sunan addinin!

(3) Zuga matasanmu ga yin watsi da koyarwar addinin da kyawawan halaye da ɗabi’u, da koya musu shan ƙwayoyi da sauran hanyoyin holewa da morewa a cikin rayuwar duniya kawai!

(4) Kunna wutar fitinar yaƙe-yaƙe da kashe-kashen babu-gaira-babu-dalili a cikin alummominmu na-kusa da na-nesa, domin hallaka jamaarmu da lalata mana dukiyoyi!

(5) Tsare hanyoyi a yankunan da suka fi yawa, ana fitar da masu surar musulmi daga cikin matafiya, ana karkashe su, ana jefa gawarwakinsu da motocinsu a cikin kududdufai…!

(6) Bin mutanenmu a ƙauyuka da rugage ana karkashewa, ana yi wa mata fyaɗe, ana kwashe dukiyoyi da dabbobi, ana yin garkuwa da waɗansu domin neman kuɗin fansa…!

(7) Sace mana jarirai da yara ƙanana ana haurewa da su zuwa yankin kudu, domin a tashe su a cikin wata alada da addinin da ba nasu na asali ba, ko kuma a dasa musu ƙiyayyar addinin musulunci!

(8) Zuwa gidajen marayu na gwamnati ana karɓar yaranmu ƙanana da sunan ɗaukar nauyin marayu da taimakonsu, a ƙarshe kuma a dasa musu ƙyamar addininsu na asali!

(9) Kai ziyara gidajen kurkuku da asibitoci domin bayar da gudunmawa da taimako ga mabuƙata a fili, a ɓoye kuma ko a fakaice ƙoƙarin sauya musu addini!

(10) Ɓuya a ƙarƙashin gina wa almajirai makarantu da ba su taimako domin wai a kyautata rayuwarsu, a fakaice kuma ƙoƙarin amfani da su domin aiwatar da wata agenda a nan gaba!

(11) Lalata mata da matasa ta shigar musu da ƙwayoyi, da yaudararsu da yan kuɗaɗe ko samar musu da aikin yi, ko magani ko kuma samar wa ’ya’yansu makarantu da nufin sauya musu addini!!

(12) Kashe majinyatanmu a cikin asibitoci, ko dai ta hanyar barinsu hakan nan ba tare da kulawa ba, ko kuma ta yi musu allurori ko kuma ba su maganin da zai ƙarasa su, da makamantan hakan.

Duk wanda na fahimci yana da hanu wurin aikata irin wannan ta’addancin ga musulmi, ko yana taimakawa ko kuma yana murna da farin ciki saboda an aikata irin hakan, to kuwa babu yadda zuciyata za ta natsu da shi, har kuma in iya zama in ci abincinsa kowane iri, kuma a kowane wuri da kowace irin ma’ana kuwa.

Ban haramta halal ba. Amma ba ni tsammanin irin waɗannan mugayen arnar ne Alqur’ani ya ce a ci yankansu ko a auri matansu. Kuma ban amince cewa irin su ne magabata suka ci yankansu ko suka auri matansu ba.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments