Ticker

6/recent/ticker-posts

Kome Ba Da Saninta Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Mijina ya yi mini saki ɗaya, bayan watanni biyu sai ya kira waliyyina wai ya mayar da ni, amma ba a faɗa mini ba. Sai a bayan na gama idda har bazawarai sun fara zuwa, shi ne ya kira ni wai ya mayar da ni tun tuni. Yanzu auren ya komu ko zan iya yin wani?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Abin da malamai suka ce shi ne: Daga wannan ayar

فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمْسِكُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ أَوْ فَارِقُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ

To idan suka kai lokacin cikar iddarsu sai ku riƙe su da kyautatawa ko kuma ku sallame su da kyautatawa. (Surah At-Talaaq: 2).

Ma’anar riƙe su da kyautatawa shi ne yin kome in ji malamai irin su Ibn Hazm (Rahimahul Laah), kuma ya ce

وَلَا تَكُونُ - بِنَصِّ كَلَامِ اللَّهِ تَعَالَى إلَّا بِمَعْرُوفٍ، وَالْمَعْرُوفُ - هُوَ إعْلَامُهَا، وَإِعْلَامُ أَهْلِهَا، إنْ كَانَتْ صَغِيرَةً أَوْ مَجْنُونَةً - فَإِنْ لَمْ يُعْلِمْهَا لَمْ يُمْسِكْ بِمَعْرُوفٍ، وَلَكِنْ بِمُنْكَرٍ

Kuma hakan ba ya kasantuwa - da nassin maganar Allaah Ta’aala - sai da kyautatawa. Kyautatawar kuma ita ce: Ya sanar da ita ko ya sanar da iyayenta idan ita ƙaramar yarinya ce ko kuma mahaukaciya ce. Idan kuwa bai sanar da ita ba, to bai riƙe ta da kyautatawa ba, sai dai da munanawa kawai. (Al-Muhallaa: 10/21).

Haka kuma daga wannan ayar

وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَلِكَ إِنْ أَرَادُوا إِصْلاحًا وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ

Kuma mazajen aurensu su suka fi cancantar su mayar da su a cikin hakan idan dai sulhu suka yi nufi. (Surah Al-Baqarah: 228).

Malamin ya ce

وَمَنْ كَتَمَهَا الرَّدَّ، أَوْ رَدَّ بِحَيْثُ لَا يَبْلُغُهَا، فَلَمْ يُرِدْ إصْلَاحًا بِلَا شَكٍّ، بَلْ أَرَادَ الْفَسَادَ، فَلَيْسَ رَدًّا وَلَا رَجْعَةً أَصْلًا.

Wanda ya ɓoye mata komen, ko kuma ya yi komen ta yadda labarin bai kai mata ba, to ko shakka babu bai yi nufin gyara ba. Ɓarna kawai ya yi nufi. A ƙarƙasihin hakan babu kome, babu dawowa a asali. (Al-Muhallaa: 10/21).

Sai kuma ya kawo riwayoyi daga magabata domin tabbatar da hakan, kamar wannan daga Al-Hakam Bn Uyainah

 أَنَّ عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ قَالَ فِي امْرَأَةٍ طَلَّقَهَا زَوْجُهَا، فَأَعْلَمَهَا، ثُمَّ رَاجَعَهَا وَلَمْ يُعْلِمْهَا حَتَّى تَنْقَضِيَ عِدَّتُهَا: فَقَدْ بَانَتْ مِنْهُ.

Umar Bn Al-Khattaab ya faɗa dangane da macen da mijinta ya sake ta kuma ya sanar da ita hakan, sannan ya mayar da ita amma bai sanar da ita ba har sai da iddarta ta cika: Ya ce: Ta yanke daga gare shi (ba shi da daban yin kome). (Al-Muhallaa: 10/21).

Haka Al-Imaam Al-Qurtubiy shi ma ya kawo a ƙarƙashin ayar Suratut-Talaaq

وَأَشْهِدُوا ذَوَيْ عَدْلٍ مِنْكُم

Kuma ku sanya adalai guda biyu daga cikinku sheda. (Surah At-Talaaq: 2).

A ƙarƙashinta ya ambaci cewa akwai masaloli guda shida Har zuwa inda ya ce

الرَّابِعَةُ- مَنِ ادَّعَى بَعْدَ انْقِضَاءِ الْعِدَّةِ أنَّهُ رَاجَعَ امْرَأَتَهُ فِي الْعِدَّةِ، فَإِنْ صَدَّقَتْهُ جَازَ ، وَإنْ أنْكَرَتْ حُلِّفَتْ، فَإنْ أَقَامَ بَيِّنَةً أنَّهُ ارْتَجَعَهَا فِي الْعِدَّةِ وَلَمْ تَعْلَمْ بِذَلِكَ لَمْ يَضُرَّهُ جَهْلُهَا بِذَلِكَ

 Matsala ta-huɗu: Wanda ya yi da’awa a bayan cikar idda cewa shi yayi wa matarsa kome a cikin iddar, to idan ta gaskata shi to ya halatta. Idan kuma ba ta yarda ba sai a rantsar da ita. Idan kuma ya kawo sheda cewa shi ya mayar da ita a cikin idda ita ce dai ba ta san hakan ba, wannan rashin sanin na ta ba zai cutar da shi ba, tana nan a matsayin matarsa. (Tafseer Al-Qurtubiy: 18/158).

Baiwar Allaah! Daga waɗannan nassoshin na malamai muna iya fahimtar amsar tambayarki

1. Tun da mijin ya riga ya sanar da waliyyinki hakan to magana ta kare, sai kawai ki koma ki cigaba da zama da shi.

2. Idan kuma ba ki yarda da maganar komen ba to kina iya kai maganar gaban alƙali wanda kuma zai rantsar da ke a kan hakan!

3. Rashin sanar da ke da ba a yi ba laifi ne, kuma bai kamata ba. Alƙali yana iya horar da wanda ya ɓoye hakan daga gare ki, idan dai ba yana da wata hujja gamsasshiya ba.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments