Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Gama Idda A Watannin Biyu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Bayan miji ya sake matarsa da watanni biyu da wasu ’yan kwanaki sai ya ce ya dawo da ita. Amma sai ta ce ba za ta komo ba, don wai ta yi haila har sau uku daga lokacin da ya aukar da sakin! Shi ne shi kuma yanzu ya ƙyale ta har sai ta sake yin wani auren sannan zai shigar da ita da iyayenta a kotu. Ko hakan ya yi daidai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] Idda da watanni uku yana ga wadda ba ta fara haila ba ce saboda yaranta, ko kuma wadda ta wuce lokacin yin hailar saboda tsufa. Amma wacce take cikin shekarun yin haila, to ita iddarta na kammaluwa ne da yin haila guda uku a zance mafi rinjaye a wurin malamai, saboda ayar cikin Surah Al-Baqarah.

A ƙarƙashin wannan, tsawon lokacin iddar mai yin haila kan iya wuce watanni uku kamar idan tana shayarwa. Haka kuma yakan iya gaza watanni ukun idan ta zama daga cikin masu yin haila da wuri kafin cikan wata.

Abin da ya kamata dai a yanzu shi ne: Idan ana shakka ko kokonto a kan al’amarin wannan matar sai a binciki amintattun masana daga cikin dangi da ’yan’uwanta don tantancewa. Idan kuma hailar ta rikice mata ne saboda shaye-shayen maganin hana ɗaukar ciki da mata ke fama da shi a yau, to sai a koma ga kwanakin hailarta na asali kafin haka, don a gano.

[2] Sannan ita kuma ta san cewa: Bai halatta gare ta ba ta ƙi yarda ta koma gidan mijinta bayan ya komo da ita, matuƙar dai ba saki na-uku, na-ƙarshe ba ne, kuma ba da nufin cutar da ita ba ne. Allah Taaala ya ce

وَالْمُطَلَّقٰتُ يَتَرَ بَّصْنَ بِاَنْفُسِهِنَّ ثَلٰثَةَ قُرُوْۤءٍۗوَلَا يَحِلُّ لَهُنَّ اَنْ يَّكْتُمْنَ مَا خَلَقَ اللّٰهُ فِىْۤ اَرْحَامِهِنَّ اِنْ كُنَّ يُؤْمِنَّ بِاللّٰهِ وَالْيَوْمِ الْاٰخِرِۗوَبُعُوْلَتُهُنَّ اَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِىْ ذٰلِكَ اِنْ اَرَادُوْۤا اِصْلَاحًاۗوَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِىْ عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوْفِۖ وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌۗوَاللّٰهُ عَزِيْزٌ حَكِيْمٌ

Kuma matan da aka sake su sai su  haƙurin zama da kansu har tsawon haila uku. Kuma bai halatta gare su ba su ɓoye abin da Allaah ya halitta a cikin mahaifayyarsu ba, in dai har sun kasance suna yin imani da Allaah da Ranar Lahira. Kuma mazajensu ne suka fi haƙƙin su mayar da su a cikin iddar idan dai sun yi nufin kyautatawa ne. Kuma mata suna da kwatankwacin irin abin da ke kansu na haƙƙoƙi tare da alheri, kuma amma maza suna da ƙarin falala a kansu. Kuma Allaah Mabuwayi ne Mai Hikima. (Surah Al-Baqarah: 228).

[3] Iyaye da sauran wakilai da waliyyai da suka tsaya a wurin ɗaurin aure su riƙa haƙurin zama suna warware matsalolin auratayyansu a gaban limamai ko malaman Sunnah shi ne ya fi. Ba a zuwa kotu sai in abin ya gagara, kuma sai in ya zama dole.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments