𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam ina da
matsala tsakanina da mijina, baya son haihuwa ko saduwa muka yi saidai ya zubar
da maniyinsa a waje, Ga shi kuma yarinyar mu ɗaya,
ita ma bai damu da ita ba, ina da laifi In na hana shi kaina ??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam To 'yar'uwa
yana da kyau ki Sani cewa ya Halatta a samu tazara a tsakanin iyali, abin da
musulunci ya hana shi ne kin haihuwa kwata-kwata, saboda babbar manufar aure
shi ne hayayyafa, don a samu wadanda za su bautawa Allah.
Zubar da maniyyi a wajan
Farji ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna
yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake
sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911.
Hadisin da ya gabata yana nuna
cewa: Bai halatta mace ta hana mijinta kanta ba saboda hujjar yana AZALO, tun
da Alqur'ani bai haramta ba.
Saduwa rukuni ne babba a aure,
Wannan yasa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: (Mace ta amsa kiran
mijinta ko da tana kan kaskon tuya ya kira ta, sannan la'ana ta tabbata ga
wacce mijinta ya yi fushi da ita, saboda ya neme ta ba ta ba shi hadin-kai ba.
Kula da abin da mutum ya haifa
wajibi ne, ciyar da su kuma sadaka ne, Wannan yasa za ki dinga yiwa mijinki
nasiha cikin ladabi don ya fahimci gaskiya .
Allah ne mafi sa ni
Amsawa✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.