Ticker

6/recent/ticker-posts

Rusuno Wurin Gaisuwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Menene gaskiyar maganar da ake cewa wai Sayyiduna Umar da sauran Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) sun rusuna a kan gwiwoyinsu wurin gai da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A ƙaida wanda ya yi wannan daawar shi zai kawo dalilinsa har a duba a gani ko ya cancanta ya zama dalili a sharia ko bai cancanta ba.

Amma daga cikin abin da muke iya tunawa a kan wannan matsalar waɗansu hadisai ne kamar waɗannan

(1) Hadisin Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) wanda a cikinsa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tsaya a kan mimbari ya yi musu wa’azi a kan Sa’ar Ƙiyama da waɗansu abubuwa manya, kuma a ƙarshe da suka yawaita yi masa tambayoyi har kuma Umar (Radiyal Laahu Anhu) ya ga kamar ya fusata sai ya rusuna a kan gwiwoyinsa ya ce

رَضِينَا بِاللَّهِ رَبًّا ، وَبِالإِسْلاَمِ دِينًا ، وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا

Mun yarda da Allaah ne Ubangiji, da musulunci shi ne addini, kuma da Muhammad shi ne Annabi. (Sahih Al-Bukhaariy: 540, 7294).

A zahiri wannan ba rusuno ne domin gaisuwa ba. Ya fi kama da rusuno domin ya ƙara tsawo har Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya gan shi kuma ya ji shi. Wallahu Aalam.

(2) Hadisin Abud-Dardaa’i (Radiyal Laahu Anhu) inda ya riwaito bayanin matsalar da ta shiga tsakanin Abubakar da Umar (Radiyal Laahu Anhumaa). Da ya nemi yafiyarsa amma bai yarda ba shi ne ya je wurin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Shi kuma ya ce: Zauna kawai a bin ka Abubakar! Allaah ya gafarta maka! Daga baya da Umar (Radiyal Laahu Anhu) ya zo, kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fara yi masa faɗa a kan yadda ya mu’amalanci Abubakar (Radiyal Laahu Anhu) sai shi Abubakar ɗin ya ji tsoron kar wani abu ya auku. Don haka sai ya rusuna a kan gwiwoyinsa, yana cewa

يَا رَسُولَ اللَّهِ ، وَاللَّهِ أَنَا كُنْتُ أَظْلَمَ مَرَّتَيْنِ

Ya Manzon Allaah! Wallahi ni ne fa mai laifin! Har sau biyu. (Sahih Al-Bukhaariy: 3661).

Wannan ma a fili yake cewa: Ba rusuno irin na gaisuwa ba ne.

(3) Hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) a kan dalilin saukar ayar: Amanar Rasuul, ya ce: Lokacin da aka saukar da aya ta 284 a cikin Surah Al-Baqarah

لِلَّهِ مَا فِى السَّمَوَاتِ وَمَا فِى الأَرْضِ وَإِنْ تُبْدُوا مَا فِى أَنْفُسِكُمْ أَوْ تُخْفُوهُ يُحَاسِبْكُمْ بِهِ اللَّهُ فَيَغْفِرُ لِمَنْ يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Na Allaah ne duk abin da ke cikin sammai da ƙasa, idan kuma bayyana abin da ke cikin zukatanku ko kuka ɓoye shi, Allaah zai yi muku hisabi a kansa. Sai kuma ya yi gafara ga wanda ya ga dama, kuma ya azabtar da wanda ya ga dama. Kuma Allaah Mai cikakken iko ne a kan dukkan komai. (Surah Al-Baqarah: 284).

Sai abin ya yi wa Sahabban Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) tsanani, don haka sai suka zo wurinsa suka rusuna a kan gwiwoyinsu a gaban Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) suka ce: Manzon Allaah, an ɗora mana nauyin ayyukan da muke iyawa sallah da azumi da jihadi da zakkah, amma a yau ga shi an saukar da wannan ayar da ba za mu iya ɗaukar ta ba… har dai zuwa ƙarshe. (Sahih Muslim: 344).

Wannan ma a zahiri lokacin da suka zo Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a zaune ya ke. Shiyasa su ma suka zazzauna a kan gwiwoyinsu. Ba wai sun yi rusuno ne irin na mai gaisuwa kamar yadda waɗansu daga cikin mutanenmu suke yi wa manyansu ba.

Kuma ko da ma ya tabbata cewa, wannan rusunon na gaisuwa ne ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), to wanene daga cikin manyan shehunai da malamai ya cancanci shi ma a yi masa irin wannan? Wanene yake da matsayi irin na Ma’aiki (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)?

Sannan a kan siffar gaisuwa a lokacin haɗuwa dai abin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya koyar da al’ummarsa shi ne

(4) Hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) cewa

إِذَا لَقِىَ أَحَدُكُمْ أَخَاهُ فَلْيُسَلِّمْ عَلَيْهِ فَإِنْ حَالَتْ بَيْنَهُمَا شَجَرَةٌ أَوْ جِدَارٌ أَوْ حَجَرٌ ثُمَّ لَقِيَهُ فَلْيُسَلِّمْ عَلَيْهِ أَيْضًا. قَالَ مُعَاوِيَةُ وَحَدَّثَنِى عَبْدُ الْوَهَّابِ بْنُ بُخْتٍ عَنْ أَبِى الزِّنَادِ عَنِ الأَعْرَجِ عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- مِثْلَهُ سَوَاءً.

Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan’uwansa sai ya yi masa sallama. Idan kuma bishiya ko gini ko dutse ya shiga tsakaninsu ya sake haɗuwa da shi, sai ya sake yi masa sallama. (Sunan Abi-Daawud: 5202, kuma sahihi ne daga Abu-Hurairah, kuma daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)).

(5) Hadisin  Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) ya ce

قَالَ رَجُلٌ يَا رَسُولَ اللَّهِ الرَّجُلُ مِنَّا يَلْقَى أَخَاهُ أَوْ صَدِيقَهُ أَيَنْحَنِى لَهُ قَالَ « لاَ ». قَالَ أَفَيَلْتَزِمُهُ وَيُقَبِّلُهُ قَالَ « لاَ ». قَالَ أَفَيَأْخُذُ بِيَدِهِ وَيُصَافِحُهُ قَالَ « نَعَمْ ».

Wani mutum ya ce: Ya Manzon Allaah, idan wani daga cikinmu ya haɗu da ɗan’uwansa ko abokinsa shin dukawa zai yi masa? Ya ce: A’a. Ya ce: Zai rungume shi ne ya sumbance shi? Ya ce: A’a. Ya ce: To zai kama hannunsa ne ya yi musafaha da shi? Ya ce: E, haka zai yi. (Sunan At-Tirmiziy: 2947, kuma yace: Hadisi ne hasan kyakkyawa).

Ma’anar ɗan’uwa da ya zo a cikin hadisin ba ɗan’uwa na jini ake nufi ba, balle wani ya fitar da iyaye da malamai ko shehunai daga ciki ma’anar hadisin. Ɗanuwa na Addinin Musulunci a ke nufi, kamar yadda ya zo a cikin Tuhfatul Ahwaziy: 7/426.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments