Maganin Mijin Dare

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Tambayata itace inada aure amma  na yi wata uku dayin auren to watan farko mijina baya gida watana biyu yadawo bayan nagama jinin haila sai yasadu dani sai na yi mafarkin wani daban yana saduwa dani Sai da ya sake tafiya bayan na sake yin wani jini sai ya sadu dani saina sake yin mafarkin wani na saduwa dani, Dana fadama mijina sai yace narinqa yin addu'a kuma ina yi amma duk da haka ina mafarki mai ban storo.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wannan ba shakka yana daga sharrin jinul ashiq (Aljanin soyayya). 

    Amma ki samu man zaitun alhawaj ki haɗa da  kisdil Hindi da man habbatus-sauda seki soya Man Jan miski ki haɗa Su duk seki tofa ayoyin ruqya aciki duk Lokacinda zaki kwanta ki shafa shi daga cibiya zuwa qasa.

    Sannan ki samu ganyen magarya guda bakwai ki dandaqesu kisa akwano ki zuba ruwa aciki seki tofa ayoyin ruqya aciki seki sha Kuma ki shafa dukkan jikinki dashi kullum haka har tsawon Kwana 7.

    Sannan ki tafasa yayan habbatus-sauda shi kaɗai kinasha kaman shayi.

    Ki samu Garin habbatus-sauda kina haqayi dashi da sassafe dakuma inkinzo kwanciya da dare.

    Sanan ki cigaba da addu'ar da kike da azkar na safiya da maraice , kwanciya da alwala, in sha Allahu zaki  rabu da mafarkin..

    Allah ta'ala yasa mudace

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.