Ayoyin Waraka (Ayatul-Shifa'i)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mal barka da wannan lokaci. Mal dan Allah AYATUL-SHIFA'I zaka taimaka min dasu wato Ayayoyin waraka. Allah ya saka da mafificin alkairi Ameeen ya rabbbi 🤲

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    An nakalto daga wani babban Malami daga cikin Malaman Musulunci wato Shaikh Abul Qasim Al-Qushairiy (rah) cewa ɗansa yayi rashin lafiya mai tsanani. Ya ce: "Na fidda tsammani daga warkewarsa, Kuma al'amarin yayi tsanani gareni. Sai naga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam acikin Barci. Da na gaya masa abinda ke damun yarona sai yace mun "MAI YASA BAKAYI AMFANI DA AYATUSH SHIFA'I BA?". Bayan na farka daga barcin, na yi tunani sosai sai na gano cewar ashe ayoyin suna nan agurare shida ne daga cikin Littafin Allah".

    "Da na rubuta masa ajikin Farar takarda, na wanke da ruwa na bashi yasha, sai ya tashi kamar wanda aka kunceshi daga Igiya" (Wato ya warke nan da nan).

    Babu shakka Wayannan ayoyin suna maganin kowace irin cuta mutum ke fama da ita.

    Yanda ake amfani da su a nemi Ruwan Zamzam ko wayanda bana zam-zam ɗin ba, a karanta wayannan ayoyi a cikin ruwan, idan an karanta su a ciki sai a sha da niyyar neman waraka daga cutar da ke damunka. in shaa Allâhu Allah zai baka lafiya.

    Ayoyin Guda Shiddane gasu kamar haka:-

    ﻭَﻳَﺸْﻒِ ﺻُﺪُﻭﺭَ ﻗَﻮْﻡٍ ﻣُّﺆْﻣِﻨِﻴﻦ

     (suratul Tauba aya ta14)

    ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﻗَﺪْ ﺟَﺎﺀﺗْﻜُﻢ ﻣَّﻮْﻋِﻈَﺔٌ ﻣِّﻦ ﺭَّﺑِّﻜُﻢْ ﻭَﺷِﻔَﺎﺀ ﻟِّﻤَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟﺼُّﺪُﻭﺭِ ﻭَﻫُﺪًﻯ ﻭَﺭَﺣْﻤَﺔٌ ﻟِّﻠْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦ

     (Suratul Yunus ayata 57)

    َﻳﺨْﺮُﺝُ ﻣِﻦ ﺑُﻄُﻮﻧِﻬَﺎ ﺷَﺮَﺍﺏٌ ﻣُّﺨْﺘَﻠِﻒٌ ﺃَﻟْﻮَﺍﻧُﻪُ ﻓِﻴﻪِ ﺷِﻔَﺎﺀ الِنَاس

     ( Suratul Nahl aya ta 69)

    ﻭَﻧُﻨَﺰِّﻝُ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥِ ﻣَﺎ ﻫُﻮَ ﺷِﻔَﺎﺀ ﻭَﺭَﺣْﻤَﺔٌ ﻟِّﻠْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦ

    (Suratul Isra'i aya ta 82)

    ﻭَﺇِﺫَﺍ ﻣَﺮِﺿْﺖُ ﻓَﻬُﻮَ ﻳَﺸْﻔِﻴﻦ

     (Suratush Shu'ara ayah ta 80.)

    ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﻟِﻠَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻫُﺪًﻯ ﻭَﺷِﻔَﺎﺀ

    (Suratul Fusilat aya ta 44).

    Waɗannan sune ayoyin da ake kira AYATUSH SHIFA'I (Ayoyin Waraka)

    Ko Wace irin Cuta ke damuka In shaa Allahu zaka samu waraka daga Allah. Ya Allah ka kara mana lafiya a jikin mu.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.