Ticker

6/recent/ticker-posts

A Bakin Aurenki Idan Baki Bari Ba!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Mijina yana mu’amala da mata a waje, don in yi maganin hakan sai na yi amfani da wani layin waya ina tura masa saƙon waazi ba tare da ya san ni ce ba. Da ya fara zaton wataƙila ni ɗin ce, sai ya ce: Idan ni nake turawa, to a bakin aurena idan ban bari ba! Ni kuma sai da na sake turawa har sau biyu sannan na bari. Daga baya dai ya tura ni gidanmu har sai da na yi watanni huɗu sannan ya biyo ni da saƙon saki ta waya, alhali da ma akwai saki ɗaya. Bayan na gama idda sai kuma ya dawo aka sake ɗaura mana sabon aure. Malam, wai yaya matsayin wannan auren na yanzu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A kan wannan mas’alar mun amsa Tambaya ta A188 inda muka ce:

Sakin aure na’uka ne mabambanta in ji malamai: Akwai Saki Naajiz akwai kuma Mu’allaq. Naajiz shi ne wanda mai yin sakin ke nufin aukuwar shi a daidai lokacin da ya faɗe shi kawai, bai rataya shi ga aukuwar wani abu ba.

Shi kuwa Mu’allaq shi ne sakin da ya rataya aukuwarsa ga wani sharaɗi, kamar wanda ya ce wa matarsa: In kika fita zuwa wuri kaza, to kin saku!

Hukuncin wannan sakin a wurin malamai ya kasu kashi biyu:

(i) Akwai Al-Mu’allaqul-Qasamiy, wanda mai faɗinsa yake nufin ƙarfafa maganarsa ce kawai. Watau so ya ke ya hana matar aikata wani abu, ko kuma ya ɗora ta kan aikata wani abu. Amma ba nufinsa aukuwar sakin ba ne! Malamai sun nuna, a nan ba a cewa sakinsa ya auku, ko da kuwa abin da ya rataya maganar a kansa ya auku, watau ko da matar ta aikata wannan abin da ya faɗan. Hukuncinsa kawai sai ya yi kaffarar rantsuwa: Ciyar da miskinai guda goma, ko tufatas da su, ko kuma ’yanta baiwa. Idan kuma bai samu ikon hakan ba sai ya yi azumin kwanaki uku.

(ii) Akwai kuma Al-Mu’allaqus-Shartiy, wanda mai faɗinsa yake da nufin aukar da sakin tun daga zuciyarsa. Wannan kam sakinsa ya auku a daidai lokacin da matar ta aikata abin da ya rataya sakin a kansa.

Don haka a nan ana buƙatar sanin menene manufar mai faɗin irin wannan sakin, kafin ya yanke hukunci a kansa.

Daga nan ya fito fili kenan cewa

(i) Idan ya tabbata daga mijin cewa, da ma sakin ta yake nufi tun daga zuci a lokacin da ya faɗi waccan maganar, to sakinta da ya yi na ƙarshen ya kammala saki uku kenan. Don haka ba zai yiwu su sake yin aure da shi ba, sai daga bayan ta auri wani mijin na-daban kuma ta rabu da shi bayan cikakkiyar saduwa ta auku a tsakaninsu, kamar yadda aya ta tabbatar. (Surah Al-Baqarah: 230).

فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُ مِنْ بَعْدُ حَتَّىٰ تَنْكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُ ۗ فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَنْ يَتَرَاجَعَا إِنْ ظَنَّا أَنْ يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ ۗ وَتِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ

Sa´annan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima´i da wani miji waninsa. Sa´annan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cewa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani. (Surah Al-Baqarah: 230).

(ii) Idan kuwa ba sakin yake nufi ba, kawai dai tsoratar da ita yake nufi to wannan auren da suka ƙulla a yanzu ya yi. Kuma saura igiyarsa ƙwara ɗaya tal. Sai su kiyaye.

Allaah ya ƙara mana shiriya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓��𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments