Ticker

6/recent/ticker-posts

Wai Da Gaske Annabi (Saw) Ya Yi Kitso A Kansa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wai da gaske Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi kitso a kansa? Wane irin ne ya yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn Maajah sun riwaito daga Ummu-Haani’ (Radiyal Laahu Anhumaa) ta ce:

« قَدِمَ النَّبِىُّ -صلى الله عليه وسلم- إِلَى مَكَّةَ وَلَهُ أَرْبَعُ غَدَائِرَ تَعْنِى عَقَائِصَ »

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya iso Makkah alhalin yana da kitso gado huɗu a kansa. (Sahih Abi-Daawud: 4191).

Al-Haafiz Ibn Hajr (Rahimahul Laah) ya ce

فَحَاصِلُ الْخَبَرِ أنَّ شَعْرَهُ طَالَ حَتَّى صَارَ ذَوَائِبَ فَضَفَرَهُ أرْبَعَ عَقَائِصَ، وَهَذَا مَحْمُولٌ عَلَى الْحَالِ الَّتِي يَبْعُدُ عَهْدُهُ بِتَعَهُّدِهِ شَعْرَهُ فِيهَا وَهِيَ حَالَةُ الشُّغْلِ بِالسَّفَرِ وَنَحْوِهِ، وَاللهُ أعْلَمُ

Abin da wannan hadisi yake nunawa a taƙaice shi ne, gashin kansa ya yi tsawo ne har yana sauka a gaban goshinsa, don haka sai ya kitse shi gado huɗu. Wannan kuma ana ɗaukar sa a kan halin da ya yi nesa da kulawa da gashin ne, kamar a halin shagaltuwarsa da matsalar tafiya ko makamancin hakan. Kuma Allaah ne masani. (Fat-hul Baariy: 10/360).

Ya zo a cikin littafin Injaahul Haajah a Haashiyah na Ibn Maajah cewa

لَعَلَّهُ فَعَلَ ذَلِكَ لِدَفْعِ الْغُبَارِ . انْتَهَى

Me yiwuwa ya yi hakan ne domin kawar da tattaruwar ƙura ga gashin. Shikenan.

A kan haka ne Al-Mubaarakafuuriy (Rahimahul Laah) ya ce

وَهُوَ الظَّاهِرُ لِأَنَّهُ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - كَانَ فِي السَّفَرِ

Wannan kuma ita ce fassara ta fili, domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance a cikin halin tafiya ne a lokacin. (Tuhfatul Ahwaziy: 5/390).

Shiyasa malamai suka ce: Wannan duk a babin al’adar larabawan zamaninsa ne, bai fita daga cikin hakan ba. Sannan a cikin karantarwarsa bai sanya tsawaita gashin da yawaita shi har a samu daman kitse shi, wani aikin samun lada ba, haka ma aske shi. Ya dai yi umurni ne kawai cewa a karrama gashin idan ya yi yawa. (Sahih Abi-Daawud: 4165).

Amma idan zamani ko wuri ya sauya ta yadda tsawaita gashin ko yawaita shi da kitse shi ya koma al’adar mata ne a keɓance, to bai halatta maza su yi koyi da su a cikin hakan ba. Haka kuma idan yin hakan ya kasance wata alama ce da waɗansu kafirai ko fasiƙai suka bambanta da ita, kuma har waɗansu wawaye suke koyi da su, to a nan ma bai halatta masu mutunci su yi hakan ba, don gudun yin koyi da su.

Sananniyar ƙaida ce tabbatacciya a cikin addini cewa, an hana koyi da mata a cikin tufafinsu da kwalliyarsu da sauran abubuwan da suka keɓance su. Saboda maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِالرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ، وَ لَا مَنْ تَشَبَّهَ بِالنِّسَاءِ مِنَ الرِّجَالِ »

Mai kamantuwa da maza daga cikin mata ba ta cikinmu, haka ma mai kamantuwa da mata daga cikin maza. (Sahih Al-Jaami’: 5433).

Haka ma koyi da kafirai da fasiƙai da makamantansu ma bai halatta ba, domin maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), cewa

« لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِغَيْرِنَا، لَا تُشَبِّهُوا بِالْيَهُودِ وَ لَا بِالنَّصَارَى »

Mai kamantuwa da waɗanda ba mu ba, ba ya cikinmu. Kar ku kamantu da Yahudawa ko da Nasara. (Sahih Al-Jaami’: 5434).

Haka kuma maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ »

Duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to kuwa yana a cikinsu. (Sahih Al-Jaami’: 6149).

Allaah ya ƙara mana fahimta.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments