Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Dole

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum Mace ce iyayenta suka aurar da ita ga wanda bata so yanzu wata tare kenan ba'a tare ba ita yarinyar tana zaune a gidan iyayenta da sunan aure sabida shi wanda aka daura mata aure da shi baya ma kasar baki ɗaya Gashi ita yarinyar bata da kwanciyar hankali shin yaya matsayin wannan auren?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Waalaikumussalamu. To bayin Allah da farko dai Ya kamata ku sani babu auren dole a musulunci. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya hana iyayen mace budurwa ko waliyyanta su aurar da ita ga wanda bata so, Amma idan yarinyar 'karamace wacce bata balagaba to mahaifinta yana da ikon aurar da ita domin ita babu bukatar a nemi izininta kamar yadda malamai sukace.

Amma idan budurwace wacce ta balaga to ita baya halatta a bada aurenta ba tare da neman yardarta ba sabida faɗin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa BA A AURAR DA BUDURWA SAI AN NEMI AMINCEWARTA (IZININTA) SAI SAHABBAI SUKACE YAYA IZININTA YAKE? SAI ANNABI YACE SHINE TAYI SHIRU. (Bukhari da muslim).

Ya taɓa faruwa a lokacin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam WANI MAHAIFI YA YIWA ÝARSA AUREN DOLE SAI TAKAI KUKANTA GURIN MANZON ALLAH SAI MANZON ALLAH YA BATA ZAƁI MA'ANA IDAN TANA SON SA TAJE TA ZAUNA DASHI IDAN KUMA BATA SON SA SAI A RABA AUREN, SAI ITA MATAR ta ce TA AMINCE DA ZAƁIN MAHAIFINTA AMMA DAMAN TANA SON MATA SU SANI CEWA IYAYENSU ba su DA IKON SUYI MUSU AUREN DOLE (Ibn maja)

Wannan yake nuna mana baya halatta a aurar da mace ga wani namiji har sai an nemi yardar ita matar matukar dai ta zama budurwa to sai an kirayeta an nemi yardarta idan tayi shiru irin shirunnan na jin kunya wanda yake nuna cewa ta amince to shikenan sai a ba su dama su fa fahimci juna ayi musu aure.

Amma idan ta nuna alamun cewa bata sonsa to ba ya halatta a tilasta mata cewa dole sai ta aure shi wannan haramunne a musulunci.

Idan kuma an riga an ɗaura mata auren da wanda bata so, to anan wajen ita yarinyar tana da zaɓi guda biyu na farko shine Idan ta amince ta yarda zata zauna da mijin to shikenan auren ya inganta, zaɓi na biyu idan yarinyar ta ce ita bata son sa to auren 'bataccene ma'ana be ingantaba kamar yadda hadisin dake sama ya tabbatar.

Akwai hadisi daya tabbata cewa khansa'a bnt khudaam Al'ansariyya babanta ya aurar da ita lokacin tana bazawara ita kuma bata son auren. Saitaje wajen Annabi ta sanar dashi. Sai ya raba auren. Irwa'ul galeel 1830.

Sabida haka ina kira ga yarinyar data kwantar da hankalinta wannan aure idan har tilasta mata aka yi kuma har yanzu bata sonsa to auren ba ingantaccen aure bane, sai dai kuma duk da haka yanzu ba itace take da ikon tabbatar da rashin ingancin auren ba a'a zuwa zatayi ta kai kara inda ake da ikon warware aure kamar wajen iyayen mahaifinta ko kuma kotun musulunci, wannan itace hanyar da ya kamata tabi tabbas idan takai kara ɗaya daga cikin waɗannan guraren matukar ta sanar dasu cewa ita bata son wanda aka aura mata kuma ba da amincewarta aka yi aurenba, na tabbata zasu rusa auren domin daman auren bataccen aure ne. wannan shine mafi alkhairi a wajenta kuma hakan baya nuna cewa ta bujirewa iyayenta ko ta tozarta iyayenta da ýan'uwanta.

Sa'annan shima wanda aka aurawa ɗin yana da laifi mutukar yasan bata sonsa. Domin an haɗa kai dashi an zalunceta kenan.

Abinda ya dace shine idan ya fuskanci bata sonsa da gaske to ya janye ya kyaleta. Idan ya yi haka to tabbas zai samu sakamako mai kyau.

Ahmad ya ruwaito wani hadisi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yake cewa "Wanda yabar wani abu saboda Allah, Allah zai musanya masa da wanda ya fishi alheri

Lallai ya kamata iyayenmu ku gane cewa shi Auren dole ba koyarwar musulunci bane Amma duk da haka idan ýarku tazo muku da mutuminda baku aminta da addininsa ba to anan baya halatta ku aura mata shi matukar bashi da tarbiyya duk yadda takai da son sa harammune ku biye mata

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments